Dangin Iya da Baba

Tun lokacin da matata ta halarci wani mahimmin kwas a ofishin “A1 Nana” game da salon Annabawa a tarbiyyar ‘ya’yansu,  da alakarsu da su, zubin rayuwarmu  da ‘yayanmu ya canza baki daya; musamman ta bangaren alakarmu da su, zama da su, da hira da su; saboda mun ga tsohon tsarin da muke bi ya yi hannun-riga da na wadannan manyan bayin Allah, ba ya ga matsalolin da yake rikito  mana iri-iri.

Na fahimci zama da yara, da fita tare da su, da shiga da su cikin manya, duk yana daga cikin tsarin annabawa wurin tarbiyyar ’ya’yansu, kuma ba ya kawo raini kamar yadda da muka dauka, yana ma dada sa yaran su   kara kaunar mahaifan nasu, su kara hankali, kuma su koyi abubuwa da dama na rayuwa da zama da jama’a.

Tun daga lokacin duk wani wurin ibada -kamar masallaci-sa-da-zumunci-kamar zuwa barkar haihuwa– da taimakon jama’a kamar aikin gayya, da su muke tafiya, sai dai idan akwai wani uzuri. Mun ga alfanun wannan   salo na annabawa matuka gaya, kuma ku gwada ku ga abin mamaki.

Daurin auren wani dan`uwana da aka yi kwanakin baya shi ne na farko da na tafi da su Muhammadu ’ya’yana, Ahmad saboda zumudin za’a tafi da shi    kauye daurin aure  ko  bacci bai iya yi ba sosai; don shi ne ma ya tashe mu sallar asuba.

An dade a danginmu ba’a yi daurin auren da ya kwashi jama’a irin wannan ba; don kusan duk ’yanuwa na kusa da na nesa ba wanda bai halarta ba.

A kan hanyarmu ta dawowa sai Mahmud ya ce: “Abba dama haka ’yanuwanmu suke da yawa?” sai na ce masa: “Ai dangi ne da ku kamar tururuwa” sai Ahmad ya kyalkyale da dariya, ya ce “Abba ita tururuwa dangi ne da ita da yawa?” sai na ce masa ba ka taba ganin shurin tururuwa ba ne, ai ’yan uwa ne da ita kamar me, shi ya sa, idan mutum yana da ’yan uwa da yawa hausawa suke cewa yana da dangi kamar tururuwa” Sai Muhammad ya ce: “Abba kuna diban kama da wanda aka daurawa aure amma kuma ni ban taba ganinsa ba sai yau, amma dai ba KANEnka ba ne?”

Sai na ce masa “A’a kanena ne dai na dangi,  shi ma sunansa Musa, don haka TAKWARAna  ne;  amma ni   na  yi fuce da TANKO; ne saboda YAYYEna  dukkansu mata ne. Shi kuwa ya fi shahara da KALLAMU; ka san  hausawa su kan kira  mai suna Musa Kallamu ko KALLA.

Ni da Kallamu tare muka yi wasan-kasa, kuma da ma ni da shi  abokan wasa ne; DAN-MACE-DA-DAN-NAMIJI muke. Kenan TAUBASHIna ne. Shi kuwa     daya Taubashin nawa wato TALLE, YAN-MAZA-ZAR muke da shi. Ma’ana, da TSOHOna, da GYATUMAr Kallamu, da BABAn Talle, uwa daya uba daya; shi ya sa ma ba na wasa da shi Tallen; da yake ka san  a al’adar hausawa, ‘yan-maza-zar ba wasa tsakaninsu, sai tsakanin dan-mace-da-dan-namiji.

Sai Mahmud ya ce: shi kenan  da azumi, in za mu tafi tashe mun huta da sayen talle! Sai na ce masa, a’a  ai ba talle yake sayarwa ba, abin da ya sa ake kiran sa da haka  saboda  babarsa tana haifar sa, ko waiwayowa ba ta yi ta gan shi ba, ta ce ga garinku nan; (ta mutu)  abin da yasa  ake  ce masa Talle kenan.

Talle ya fi kowa farin-jini a danginmu; saboda da kusan zaman-doya-da-manja ake yi da a dangin. A haihuwarsa ne aka sasanta; shi yasa ma ake ce masa SADAU.

Allah da ikonsa ni kadai ne a gidanmu namiji; don haka ko kuda ba’ a so ya hau kaina, shi kuma Kallamu mace daya ce jal a gidansu. Ita ce ‘yar babarsu ta  karshe; don haka ita ma ’YAR LELE ce Wannan  ‘YAR’ AUTA ta su Kallamu KANDE ake ce mata; saboda duk  yayyenta maza ne; kamar yadda  na gaya muku tun da fari, Amma sunanta na yanka, Fadimatu. Sai dai ko da za ku  ji a gidansu ana kiran: FADIMA, ko, FATIMA, ko  TUMA, ko FATI, ko ZARA’U, ko ZARA, ko BINTA, ko BATULA , ko BATULU, ko TA RASULU,   ita din dai ake nufi, saboda duk mai suna Fadimatu hausawa kan kira ta da daya daga cikin wadancan sunaye. Harwalau dai akan ce mata TA-SALLA, ko GOSHI, Ta-salla saboda ranar sallah aka haife ta, Goshi kuma saboda irin alherin da babarta ta samu lokacin da ta haife ta.

Ahmad ya ce: Abba me ya sa sunayen ‘yanuwanmu wasu iri, dama akwai “Annabi dan Asabe!” sai Muhammad ya ce: “ta yiwu sunan wani sahabin ne, Ladi ma ina jin sunan matar wani Sahabi ne!” sai Muhmud ya ce: “kar fa mu fadi abin da ba mu sani ba; abba ya ce ba kyau, ga Abba ba sai mu tambaye shi ba!?” sai na ce:   Yauwa Mahmud haka ya kamata, in mutum bai san abu ba ya tambaya, kuma  kada  ya fadi abin da bai sani ba.  Sai Muhammad ya ce In Allah ya yarda ba zan kuma ba. To Abba mecece amsar tambayar da Ahmad ya yi?” Sai na ce:   ‘Ya’yan danginmu ba a faya kiran mu da sunayenmu na yanka ba; saboda kusan dukkaninmu sunayen wasu manya aka sa mana a dangin; to saboda kara irin ta Bahaushe, shi ya sa ake dan sakayawa.

Kun ga dai a gidan su  Kallamu  akwai wanda ake kira :

1-DAN-ASABE; saboda ranar Asabar aka haife shi.

2-DAN-TANI \ DAN-LITI; saboda ranar Litinin aka haife shi. 3-BALA \ DAN-BALA \ BALARABE ; saboda ranar Laraba aka haife shi. Amma an fi sanin sa da YAWALE; saboda mahaifiyarsa tana cikin aikin haji ta haife shi. Hajinta na bayu kuwa da  cikin Fadimatu ta yi, shi ya sa ma wasu suke kiran ita Fadimatun YABI, ita ma kuwa ranar laraba aka haife ta; don haka akan ce mata LARAI, wasu kuma su kira ta LARABA , wasu kuma BALARABA. Kai Fadimatu dai da sunaye ake iri iri!

Mu kuma a gidammu akwai:

4-LADI; saboda ranar Lahadi aka haife ta. 5-TALATU; saboda ranar Talata aka haife ta. Amma danginmu na karkara sun tsaya kai-da-fata akan wai ranar Litinin aka haife ta; don haka ma kwansu da  kwarkwatarsu TANI ko ATINE suke ce mata. 6- LAMI; saboda ranar Alhamis aka haife ta. 7-JUMMAI \ JUMMA; saboda ranar Juma’a aka haife ta.

Ba shakka Jummai ta sha-miya a duniyan nan ta Subahana; don ko GAMBOn TAGWAYEnta- ARUWA da MARKA– gaba yake da ni, ko da yake SAKOna ne; don ba wai can-can ya girme ni ba. Su kuwa ana kiran su da haka ne saboda lokacin damina aka haife su. Amma a makaranta an fi sanin su da Hasan da Husaina. Yaya Jummai – duk da ba dakinmu daya da ita ba- amma dai ta zama kamar mahaifiyarmu; da ma hausawa na cewa “Babbar Ya, Uwa

Sai Ahmad ya ce: “To Abba su waye KAKANIN KAKANInmu kuma?”

Sai na ce: Mu dai TATTABA-KUNNEn Malam BARAU ne; don iyayenmu ne JIKOKInsa.

Muna zuwa nan sai Muhammad ya ce: Kash! Abba ga shi har mun karaso gida, kuma ba ka gama ba, ga shi tarihin da dadi! Sai Mahmud ya ce: Don Allah Abba in za ka tafi kasuwar ladin makoli ka tafi da mu sai ka karasa mana a hanya? Sai Ahmad ya ce Ee don Allah Abba ka tafi da mu  dama ina so in ga kasuwar kauye! Sai na ce: to shikenan, amma ban da wanda ya makara wurin shirin tafiya makaranta ko da sau daya ne, tsahon wannan satin, kun yarda? Suka ce EEEE!!! mun yarda.  Sai na ce: To,  Allah ya kai mu.

Da sati ya zagayo, tun da sanyin safiya su Mahmud suka je suka wanke mota tas suka goge, sannan suka yi wanka suka shirya, bayan mun karya kumallo tare da su, sai muka kama hanya, sai Ahmad ya ce: “Abba saboda lokaci ko za fara ci mana gaba yanzu? Sai Muhammad ya ce: Abba mun tsaye ne inda ka ce: kuna taba kunne, sai na ce masa a’a ko dai ba ka ji ba sosai, ce muku na yi: mu TATTABA-KUNNEn Malam BARAU ne; don iyayenmu ne JIKOKInsa.

Duk yaron da ya fara tsawon rai bayan an ta haihuwa a gidansu yaran suna komawa, hausawa su kan kira shi: “Barau” ko“BAWA” ko “DOGARA” in mace ce kuma su ce mata “AYASHE” To shi ma KAKAn iyayen namu daga nan sunan nasa ya samo asali, amma sunansa na yanka Sama’ila. Yana da danwa daya ana kiran ta KILISHI; saboda lokacin haihuwarta ya dace da lokacin da aka yi wa Babansu nadin sarauta, amma hakikanin sunanta, Bilkisu; shi ya sa ma ake  yi mata kirari da MAI GADON ZINARE.

Kaka Yusufu matansa hudu, ‘ya’ya talatin  daya babu, koda yake  kusan ashirn ba biyu sun riga mu gidan-gaskiya. Wadanda suke raye a yanzu kuwa su ne: Farko dai akwai wanda ake cewa:

1- MAI-KANO; Saboda Abdullahi sunansa.

2- GARBA\ SADAUKI; saboda Abubakar sunansa, kuma ana yi masa lakabi da SADDIKU.

3- SANDA; saboda Ummaru sunansa, kuma ana yi masa lakabi da FARUKU.

4- SHEHU; saboda Usmanu sunansa, kuma ana yi masa lakabi da ZUNNURAINI.

5- GADANGA SADAUKI; saboda Aliyu sunansa, kuma ana yi masa lakabi da HAIDARA.

6- SADIYA; saboda Halimatu sunanta.

7- ABU; saboda Zainabu sunanta.

8- KULU; saboda Hauwa’u sunanta.

9– DIJE; Amma asalin sunan Khadijatu ne, kuma ana yi mata lakabi da KUBURA

10-RAKIYA, amma asalin sunan nata Rukayyatu ne. Koda yake an fi ce mata AZUMI; saboda da ita, da Babanmu, duk a watan azumi aka haife su; shi ya sa ma za ku ji maimakon Ummaru Sanda, an fi ce masa DAN-AZUMI ko LABARAN .

Shi kuma Baban Talle ranar sallah karama aka haife shi; don haka za ku ga an fi sanin sa da SALLAU . Amma da a ce ranar sallah babba aka haife shi da  ALHAJI za a rika ce masa duk da bai yi aikin Haji ba,  kamar dai yadda za su cewa mace HAJIYA in a ranar aka haife ta.

Dukkanin ‘yan uwan mahaifin nan nawa, wanda ya girma da wanda ya girme shi, in namiji ne BAFFA nake ce masa, in mace kuma GOGGO, yanzu ma na fadi sunayen saboda ku san danginku yadda ya kamata.

Babata Hajiya SHATU sunanta. Tana da ‘yan uwa guda biyu; INNA Salamatu, da KAWU Jafaru. Amma asalin sunnan nata A’ISHATU ne, shi ya sa za ku ji wasu suna kiran ta da INDO.

Muna kan hanyarmu ta dawowa sai aka bugo min waya, sai Ahmad ya ce: Abba wa ya bugo maka waya,? Sai na ce masa Yaya Jummai ce tana son in je in  raka ta karamar hakumar Zaria, wani  kauyen kayau a jihar Kaduna a Najeriya; don ta halarci shagulgulan bikin KORAU da AUDI ‘ya’yan wasu   kawayenta ZAZZAGAWA da yake ita Allah ya sa mata sha’awar harka da kauyawa.

Sai Muhammad ya ce Abba! Da ma mata suna yin zagi? Sai na ce kunnenka ya fara dodewa ne Muhammadu  Zazzagawa fa na ce ba ZAGAGE ba.  Sai ya ce: La baba ai na ji sosai  ni dai na dauka duk daya ne. Sai na ce a’a shi zagage jam’i ne na ZAGI ; wato mai jan akalar dokin sarki, shi kuwa Zazzagawa ai tilonsa shi ne BAZAZZAGE ko BAZAZZAGI. Ai duk tafiyarsu daya da irin su: KANAWA, KATSINAWA, DAURAWA, SAKKWATAWA, ZAMFARAWA,  KABAWA, HADEJAWA, ARAWA, ADARAWA, KURFAYAWA, ABZINAWA, ZABARMAWA, YARABAWA, GWARAWA, YAMALAWA, AGALAWA, NUFAWA, LARABAWA, TURAWA da shauransu. Ka ga ai dukkaninsu  jam’i ne na mutumin  da hausawa suke kira: BAKANO ko BAKANE, BAKATSINE, BADAURI, BASAKKWACE, BAZAMFARE, BAKABE, BAHADEJE, BA’ARE, BA’ADARE, BAKURFAYE, BA’ABZINE, BAZABARME, BAYARABE, BAGWARE, BAYAMALE, BA’AGALE, BANUFE, BALARABE, da BATURE.

Sai Mahmud ya ce: to amma me ya sa jam’in BAFILATANI ake cewa  FULANI, a jam’in BABARBARE kuma ake cewa BAREBARI me yasa  ba’a cewa Fulanawa ko Barbarawa ba kamar yadda aka ce a can.

Sai na yi murmushi na ce a to  ban da abin Mahmudu ai komai kusan ana  samun togaciya a ciki.

Sai Ahmad ya ce: Abba su wadancan da Umma Jummai za ta je bikinsu ya sunansu na yanka, kuma me ya sa ake ce musu Korau da Audi?

Sai  na ce: Shi Korau sunansa na yanka Zubairu, amma saboda babansa ya rabu da babarsa da cikinsa shi yasa ake ce masa Korau. Shi kuwa Audi abin da ya sa ake kiran sa da haka; saboda babansa ya mutu ya bar mahaifiyarsa da cikinsa, amma sunansa na yanka Aminu, Amma an fi ce masa Muhammadu; da yake  akwai wasu tarin sunaye da duk wanda kuka ji ana kiran sa da daya daga ciki, to a wurin hausawa Muhammadu ne. Kamar irin su: AUWALU, SANI, SALISU, RABI’U, HAMUSU, SADISU, SABI’U, SAMINU, TASI’U, ASHIRU, INUWA, TUKUR, BELLO, NASIRU, NAFI’U, MUJTABA, MUSTAFA, GALI, SHAFI’U, KABIRU, SAGIRU, BASHIRU, NAZIRU, MUNNIRU, NURU amma sai suka canza wasalin “u” da yake gaban bakin “r” zuwa wasalin “a” sai ya koma:

NURA ABDULLAHI MADINA (NAMadina)

Leave a comment