TUNATARWA

Ya Yan uwa!!
kuna bukatar lafiya? Yawaita Azumi!
Kuna bukatar hasken fuska? Yawaita sallar dare!
Kuna buktar haskaka kwakwalwa? Yawaita karanta Al-Qur’ani!
Kuna bukatar tsira? Kiyaye salla akan lokacin ta!
Kuna bukatar farin ciki? Yawaita istighfari!
Kuna bukatar gushewar bakin ciki? Ku lazimci addu’a!
Kuna bukatar Albarka? Yawaita salati ga Annabi Muhammad(SAW)!
Kuna bukatar gushewar kunci? Yawaita Lahaula wala quwwata illa bilLah!

Daga: Sa’ada Mahdi

Advertisements

ASSALAMU ALAIKU…

ASSALAMU ALAIKUM,’YAR UWA KO KIN SAN CEWAR JARIRI TUN YANA CIKIN MAHAIFIYAR SA,YANA JIN MAGANGANUN DA AKEYI,TO, TUN DA HAKA NE ME ZAI HANA KIYI KOKARIN SHIGAR DA KARATUN ALKUR’ANI CIKIN KWAKWALWARSA,DOMIN IDAN YA FITO DUNIYA YAYI MASA SAUKI, MAIMAKON SHIGAR DA SHIRME DA SHIRIRI TA.DOMIN SHI ALKUR’ANI WANI MABUDI NE DA YAKE BUDE KWAKWALWA YARO DON KARBAR KOWANE IRIN ILIMI.LIKITA KIKE SO DAN KI YA ZAMA KO INJINIYA? DAN KASUWA KO MAI SANA’AR HANNU? TO, GAGGAUTA KI YAWAITA KARANTA ALKUR’ANI KO SAURARON KASET KO MP3 DA SAURAN NA’URORIN DA YA SAWWAKA KODA WAYAR HANNU.ALLAH YA AGAZA MANA,AMIN.

Aside

KWAYOYI 100 DON MAGANCE MATSALOLIN AURATAYYA

kwayoyiz 100 kullum
‘yar uwa! ga wani labari da dumi-dumin sa,ko kin san kwayoyin nan 100,wanda ake hadiya kullum? don magance matsalolin yau da kullum musamman na gidan Aure,yi kokarin kora wadannan kwayoyi idan zaki kwanta barci ke har da mai gidan.SUBHANALLAH 33. ALHAMDULILLAH 33. ALLAHU AKBAR 34.

Iyalina

Ko kina sauraron gawurtaccen shirin nan da ofishin A1-Nana yake gabatarwa a gidan Radio Rahmah mai taken: “Exemplary Family Life?” to kar ki sake  a ba ki labari!  Ana gabatar da wannan }ayataccen shiri ne da yaren  ingilishi da misalin }arfe   biyar na yamma  duk ranar Laraba.  Bugu da }ari, ofishin ya bu]e ~angaren bayar da shawarwari akan  tarbiyya, zamantakewar aure,  lafiya,  gudanar da gida,  sulhu tskanin ’ya’ya da iyayensu, makusanta,  ma’aurata, kishiyoyi dss, ga kuma ~angaren fatawowi da hukunce hukunce na shari’a, ba ya ga  kwasa-kwasai daban dagaban da suke  da ala}a da ~angarorin da aka ambata, da ma wasu fagagen daban kamar sana’o’i dss     Garzaya ofishin yanzu a  No: 8 NNDC Quarters, daga lahadi zuwa alhamis  daga  9:00 AM  zuwa 2:00 PM ko a  buga lambar waya 080157383838. 064-891213, ko aika mail: nawc.a1f@gmail.com.

View original post

Maganin Matsalarka a Tafin hannunka

Ko kina sauraron gawurtaccen shirin nan da ofishin A1-Nana yake gabatarwa a gidan Radio Rahmah mai taken: “Exemplary Family Life?” to kar ki sake  a ba ki labari!  Ana gabatar da wannan }ayataccen shiri ne da yaren  ingilishi da misalin }arfe   biyar na yamma  duk ranar Laraba.  Bugu da }ari, ofishin ya bu]e ~angaren bayar da shawarwari akan  tarbiyya, zamantakewar aure,  lafiya,  gudanar da gida,  sulhu tskanin ’ya’ya da iyayensu, makusanta,  ma’aurata, kishiyoyi dss, ga kuma ~angaren fatawowi da hukunce hukunce na shari’a, ba ya ga  kwasa-kwasai daban dagaban da suke  da ala}a da ~angarorin da aka ambata, da ma wasu fagagen daban kamar sana’o’i dss     Garzaya ofishin yanzu a  No: 8 NNDC Quarters, daga lahadi zuwa alhamis  daga  9:00 AM  zuwa 2:00 PM ko a  buga lambar waya 080157383838. 064-891213, ko aika mail: nawc.a1f@gmail.com.

ME KA SANI GAMEDA ANNABI MUHAMMAD (SAW)?

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN {AI .

Yabo da Godiya su tabbata ga Allah ma]aukakin sarki wanda ya nuna mana hanyar shiriya, ya kuma kare mu daga fa]awa hanyar ~ata. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayye kuma za~a~~en manzonsa(Muhammadr), wanda aka aiko shi don ya zamo rahama ga dukkan talikai, kuma abin kowi ga masu bin hanyar }warai, tsira da aminci su tabbata ga alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiriya da shiriyarsu har zuwa ranar {iyama.

Bayan haka ;

Ya yan’uwa musulmai, ha}i}a mafificin abin da za’a bashi lokaci da kulawa ta musamman shine karantar tarihi da rayuwar Annabir tsaftacacciya, domin ta kan sanya musulmi yaji tamkar cewa tare dashi akayi wannan rayuwar , takan kuma sanya shi yaji cewa shi ma ]aya daga cikin ma]aukaka kuma barrantattu(Sahabbai) wa]anda su ne }ashin-bayan kafuwan musulunci da samun ]aukakarsa. Kuma dai ta hanyar karantar tarihin ne musulmi zai san dayawa daga cikin siffofin Annabir da hanyoyin da yabi wajen }ira i zuwa ga musulunci alokacin zaman lafiya da kuma lokacin ya}i.

Kamar yadda ta hanyar karantar tarihi ne musulmi zai gane lokuta da guraren da musulmai suke samun }arfi ko kuma rauni,da kuma abubuwan da suke kawo cin nasara ko kuma rashinsa, da kuma hanyoyin da za a bi wajen warware matsaloli idan suka faru komin girmansu.

Bugu da }ari, ta hanyar karantar tarihin Annabir ne musulmai zasu dawo da martabarsu da suke da ita ,ta hanyar sanin da tabbatar da cewa Allah yana tare dasu kuma zai taimakesu matu}ar suna bauta masa bauta ta gaskiya kuma suna mi}a wuya ga shari’arsa. Allah ma]aukakin sarki yace :

“إن تنصر الله ينصركم ويثبت أقدامكم. ( سورة محمد: 7 « In kuka taimaki Allah to zai taimake ku, kuma zai tabbatar da dugaduganku ».  kuma yace:

“إنا لننصر رسلنا والذين ءامنوا في الحياة الدنيا ويوم يقوم الأشهاد”.(سورة غافر:51).

« lallai hakika muna taimakon mazanninmu da wa]anda suka yi imani a rayuwar duniya da ranar da shaidu ke tsayawa(Kiyama). ». kuma yace :

ولينصرن الله من ينصره إن الله لقوي عزيز”.(سورة الحج:40).

«Ba shakka kuma  Allah zai taimaki mai taimakonSa. Hakika Allah mai Karfi ne  mabuwayi ».

‘Yan uwa Musulmai, ha}i}a  abubuwan da za’a fa]a cikin wa]annan shafuffuka, abubuwa ne ka]an game da tarihin Annabir, ta yadda zai zamo kamar shimfi]a ne da share fage  ga duk  mai bu}atar fa]a]a karatu da bincike kan tarihin Annabir. Allah ma]aukakin sarki yace :

“محمد رسول الله“. (سورة الفتح:29).

“ Muhammad manzon Allah ne”.

Muhimman abubuwa game da tarihin Annabir sune kamar haka:

 1. DANGANTAKAR ANNABIr:

Shine (Baban Alqasim), Muhammad ]an Abdullah ]an Abdulmu]allib ]an Hashim ]an Abdumanaf ]an  {usaiyi ]an Kilab ]an Murrah ]an Ka’ab ]an Lu’a’iyi ]an Galib ]an Fihri ]an Malik ]an Nadri ]an Kinanah ]an Khuzaimah ]an Mudrakah ]an Iliyas ]an Mudar ]an Nazar ]an Ma’add ]an Adnan. Wannan itace dangantakarsa  wacce babu sa~ani akai, kamar yadda kuma ba’a yi sa~ani ba wajen cewa “Adnan” ]aya ne daga cikin zurriyar Annabi Isma’ilu.(wato kenan dangartakan Annabir ta ha]u da ta Annabi Isma’I ]an Annabi Ibrahimu).

 1. 2.    SUNAYEN ANNABIr:

An kar~o hadisi daga Jubair ibn Mu]’im, Annabir ya ce :”Ha}i}a Ina da sunaye masu yawa;Ni ne Muhammad ,Ni ne Ahmad ,Ni ne Almahi (wato wanda Allah zai share kafirci da shi).Ni  ne Al-hashir  (wanda za’a fara tayar da shi ranar {iyama). Ni ne Al’a}ibu (wanda babu Annabi bayansa).[ Bukhari da Muslim suka ruwaito shi].

An kar~o Hadisi daga  Abu-musal’Ash‘ari yace :”Annabir ya kasance yana fa]a mana wasu daga cikin sunayensa sai ya ce : “Ni ne Muhammad, Ni ne Ahmad, Ni ne Mu}affi(wato na }arshen Annabawa), Ni ne Alhashir, Ni ne Nabiyyut-Taubah, Ni ne Nabiyyur- Rahmah”. [Muslim ne ya  ruwaito shi].

 1. 3.    TSARKAKAR DANGANTAKAR ANNABIr:

Ya ‘yan’uwa musulmai; ku sani cewa Annabinmu Muhammadr wanda shi ne fiyayyen halitta ; Allah ya kiyaye mahaifinsa(Abdullah) daga fa]awa cikin zina. Don haka an haifi Annabir ne ta hanyar aure irin wadda aka sani bata mummunar hanya ba.

An kar~o hadisi daga Wasilah ibn Asqa’I yace: Annabir ya ce: ‘Ha}i}a Allah ya fifita Annabi Isma’il daga cikin ‘ya’yan Annabi Ibrahimu, ya kuma fifita Kinana  daga cikin ‘ya’yan gidan Isma’ilu, ya kuma fifita {uraishawa daga cikin ‘ya’yan gidan kinana, ya kuma fifita ‘ya’yan gidan Hashim daga cikin {uraishawa, Ni kuma ya fifita ni daga cikin ‘ya’yan gidan Hashim ». [Muslim ne ya ruwaito shi].

Haka kuma lokacin da (Hira}al) sarkin }asar Rum ya tambayi Abu-sufyan(]aya daga cikin masu nuna }iyayya ga Annabir kafin ya musulunta) game da dangantakar Annabir sai yace:” Lallai dangantakarsa mai kyau ce a cikin mu, sai Hira}al yace: Ha}i}a haka ne ma dukkan sauran Annabawa ake aiko su daga mafi kyawun dangartakar mutanensu. [Bukhari ne ya  ruwaito shi].

 1. 4.    HAIHUWAR ANNABIr:

An haifi Annabir ne ranar litinin a watan Rabi’ul Awwal, malamai sun }ara wa juna sani game da kwanan watan da aka haife shi; wasu suka ce: biyu(2) ga wata, wasu kuma: takwas(8) ga wata, wasu kuma: goma(10) ga wata, wasu kuma suka ce:Sha biyu(12) ga wata. Babban malamin Tafsirin nan (Ibn Kasir) yace: « Maganar da  babu sa~ani akai ita ce cewa :An haife shi ne shekarar da ake  }ira (shekarar Giwaye) kamar   yadda   Ibrahim  ibnul -muzir Alhuzami  (malamin Bukhari)          da Khalifatu ibn  Khayya] da sauransu suka fa]a.

Masana Tarihi suka ce: lokacin da mahaifiyar   Annabir (Aminatu)  ta ]auki cikinsa ta ce : « Ban ji  nauyinsa ba  kamar yadda sauran mata suke ji, lokacin dana haife shi kuwa ; sai wani haske  ya fito tare  da shi  wanda ya haskaka gabar da yamma.

An kar~o hadisi  daga  Irbad ibn Sariya yace: “ Na ji Annabir yana cewa: Lallai ha}i}a tabbas  haka Allah  ya  rubuta a cikin  Lauhul-mahfuz   cewa nine cikamakin Annabawa, haka kuma al’amarin ya ke agurinSa  tun  kafin a halicci Annabi Adamu,   abubuwan da su ke nuna haka kuwa sune; Addu’ar mahaifina Annabi Ibrahimu (lokacin da ya ro}i Allah a aiko da wani manzo cikin larabawa), da kuma albishirin da Annabi Isau yayi wa mutanensa(cewa wani Annabi zai zo bayansa), da kuma           hasken     da mahaifiyata ta gani lokacin da ta haife ni, wanda  ya  haskaka   }asar  Sham (siriya).

Mahaifin Annabir ya  rasu ne kafin a haife shi.Wasu malamai suka ce : ya rasu  ne bayan haihuwarsa da wata ]aya ko kuma shekara ]aya.Amma  maganar da tafi shahara ita ce ta farko.

 1. 5.    SHAYAR DA ANNABIr:

Suwaibah ce ta shayar da shi zuwa ]an wani lokaci, sannan aka nema masa wajen shayarwa a }abilar (Bani-Sa’ad), sai Halimatus Sa’adiyya ta cigaba da shayar da shi, ya kuma zauna tare da ita tsawon shekara hu]u a gurin da }abilar Banu-Sa’ad ]in suke, a can ne ma aka tsaga }irjinsa aka tsaftace shi daga munanan halaye da rabon shai]an, ganin haka, Halimatus Sa’adiyya sai ta tsorata tayi gaggawar mayar da shi wajen mahaifiyarsa.

Mahaifiyarsa ta rasu ne a hanyar dawowanta zuwa Makka a wani guri da ake }ira (Abwa’i), a lokacin yana da shekara shida. Saboda haka ne ma lokacin da Annabir ya zo wucewa ta wannan gurin zai nufi garin Makka shekarar da akayi (Fathu Makka) sai ya tsaya a gurin ya nemi izinin Ubangijinsa don ya ziyarci kabarinta, Allah yayi masa izini, sai ya tsaya yayi kuka har yasa wa]anda suke tare da shi kuka.kuma yace: “ku ziyarci {aburbura domin tana tunatar da mutuwa.” [Muslim ne ya ruwaito shi].

Ummu-aiman (baiwar da ya ci gadanta a gurin babansa.) ita ta cigaba da rainonsa bayan rasuwar Mahaifiyarsa, sai kakansa Abdulmu]allib ya cigaba da kula dashi. Lokacin da Annabir ya kai shekara takwas, kakansa sai ya rasu, amma kafin rasuwarsa, sai ya bada wasiccin ri}on Annabir wa Baffansa(wato Abu-[alib) sai ya cigaba da kula dashi, ya kuma bashi cikakkiyar kulawa da taimako da kuma goyon baya musamman ma lokacin da aka bashi manzanci, duk da cewa shi bai musulunta ba. Saboda haka ne ma ranar {iyama Allah zai sassauta masa azaba kamar yadda ya tabbata a ingantaccen hadisi.

 1. KIYAYEWAR DA ALLAH YA YI MASAr DAGA {AZANTAR  JAHILIYYA:

Allah ma]aukakin sarki ya kiyaye annabinSa tun yana }arami daga }azantar jahiliyya da ma kowace irin aibi, ya kuma }awata shi da halaye masu kyau, har ya zamo sunan da ya yafi shahara dashi a cikin mutanensa shi ne; Al-‘ameen (wato amintacce), lura da abubuwan da suka bayyana musu na tsarkakansa da gaskiyarsa da ri}on amanarsa. Saboda haka ne ma lokacin da {uraishawa suka yi nufin sa ke gina ]akin {a’aba, a lokacin yana da shekara Talatin da biyar, bayan sun gama ginawa sai suka yi sa~ani wajen mayar da Hajrul-Aswad(Ba}in dutse) gurbinsa, kowace {abila tana cewa ita zata mayar don ta samu wannan falalar, daga }arshe sai suka daidaita kan cewa; gaba ]ayansu sun amince duk wanda ya fara shigowa masallacin to shi zai mai da dutsen gurbinsa, sai ko akayi dace wanda ya fara shigowa masallacin shine Annabir, sai suka ce Al-‘ameen ya zo kuma suka amince cewa shi zai mai da dutsen. Sai Annabir ya shimfi]a mayafinsa a }asa, ya ]auki dutsen da hannunsa ya ]aura a tsakiyar mayafin, (kasancewar da ma manya-manyan {abilun su hu]u ne); Annabir sai ya umarci wakilin kowace {abilar da ya ri}e gefen mayafin sannan su ]aga shi zuwa gurin da za’a mayar da da dutsen, Annabir sai ya ]auka da hannunsa ya mai dashi gurbinsa. [Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi].

 1. 7.    AUREN ANNABIr:

Annbir ya auri Khadija ce lokacin yana da shekara Ashirin da biyar(25). Dalilin auren kuwa shine : Annabir ya fita fatauci wa khadija zuwa }asar sham(siriya) tare da yaron gidanta Maisarah. Bayan dawowarsu daga fataucin, sai maisarah ya ba wa khadija labarin abubuwan mamaki da ya gani game da Annabir da kuma irin gaskiyarsa da ri}on amanarsa, daga nan sai khadija ta nemi Annabir da ya aure ta.      Annabir bai }ara aure ba har zuwa  rasuwar khadija (ta rasu ne kafin a yi hijira zuwa Madinah da shekara uku). Bayan rasuwarta sai Annabir ya auri Saudah ‘yar Zam’an, sannan ya auri A’ishah ‘yar Abubakar, (ita ka]ai ce Annabir ya aure ta tana budurwa). Sannan ya auri Hafsah ‘yar Umar, sai Zainab ‘yar Khuzaimah, sai Ummu-salma(asalin sunanta Hindu ‘yar Umaiya). Sannan ya auri Zainab ‘yar Jahsh, sai Juwairiyya ‘yar Haris, sai Ummu-habiba(asalin sunanta Ramlah ko Hindu ‘yar Abu-sufyan). Sannan sai ya auri Safiyya ‘yar Huyayyi lokacin da akayi ya}in Khaibar , sai ya auri Maimunah ‘yar Haris wacce ita ce mace ta }arshe da Annabi r ya aura(Allah ya }ara musu yarda).

 1. 8.     ‘YA’YAYEN ANNABIr:

Dukkanin ‘ya’yayen Annabir maza da mata in banda Ibrahim ; Khadija ce ta haifa masa su. Mahaifiyar Ibrahim ita ce Mariyatul Kib]iyya wacce Mu}au}is ya ba da ita kyauta wa Annabir.

‘ya’yayensa  maza sune :

Al-}asim (da shi ne ake yi wa Annabir alkunya, kuma bai jima ba a duniya ya rasu). Sai A]-]ahir da A]-]ayyib.Wasu malamai suka ce : ]ansa Abdullahi shi ne ake masa la}abi da A]-]ahir da A]-]ayyib domin an haife shi ne a cikin musulunci. An haifi Ibrahim ne a Madinah, ya rayu tsawon watanni Ashirin da biyu, ya riga Annabir rasuwa da wata uku.

‘ya’yayensa  mata sune :

 • Zainab : ita ce babbarsu, ]an goggonta (Abul-Ass) ne ya aure ta.
 • Ru}aiyah: mijinta shi ne Usman bn Affan.
 • Fa]imah: mijinta shine Aliyyu bn Abi-[alib, ta haifa masa Al-hasan da Al-husain (shuwagabanin matasan Aljannah).
 • Ummu-kulsum:  Usman bn Affan ne ya aure ta bayan rasuwar Ru}aiyah ( Allah ya }ara musu yarda).

Imam Nawawi yace: « Babu sa~ani kan cewa ‘ya’yayen Annabir mata su hu]u ne, maza kuwa su uku ne a bisa ingantacciyar magana ».

 1. 9.         AIKO ANNABIr DA MANZANCI :

An aiko Annabir da manzanci ne lokacin da ya cika shekara Arba’in a rayuwarsa.

Mala’ika Jibril ya fara zuwa masa ne ranar Litinin goma sha bakwai (17) ga watan Ramadhan a lokacin yana kogon Hira. Kuma ya kasance a duk lokacin da wahayi ya zo masa, ya kan shiga mawuyacin hali, fuskarsa takan canza, kuma Goshinsa yayi zufa.

Lokacin da Mala’ikan ya zo masa a karo na farko,  yace da shi: ka yi karatu !. sai Annabir ya ce : Ni ban iya karatu ba !!. Sai Mala’ikan ya dam}e shi da }arfi har sanda Annabir ya shiga mawuyacin hali sannan ya sake shi, ya sake ce masa : ka yi karatu !!. Annabir ya ce : Ni ban iya karatu ba !!!. haka aka yi har sau uku, ana ukun sai Mala’ikan ya ce da shi : « Kayi karatu da sunan Ubangijinka wanda yayi halitta.* Ya halitta mutum daga gudan jini.* Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne mafi karimci.* Wanda ya sanar (da mutum) game da alkalami.* Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.* ». [ suratul Alaq, Aya :(1-5) ].

Sai manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya dawo gurin Khadija a firgice yana ~ari, ya bata labarin abubuwan da suka faru da shi. Khadija (Allah ya }ara mata yarda) sai ta kwantar masa da hankali ta ce : « Albishirinka !! ha}i}a nasan Allah ba zai tozartar da kai ba har abada, domin kuwa kana sadar da  zumunci !, kana fa]in gaskiya !, kana ]aukan nauyin marar galihu !, kuma kana taimakon wa]anda masifu suka afka musu.

Daga nan sai wahayi ya yanke, Annabir ya zauna tsawon lokaci wahayi baya zuwa masa. Ana nan a haka wata rana Annabir yana tafiya cikin garin Makka, sai mala’ikan da ya zo masa a karo na farko ya bayyana masa a sama da shi, yana mai kwantar masa da hankali da kuma masa albishirin  cewa ha}i}a shi ]an aiken Allah ne zuwa ga mutane. Lokacin da Annabir ya ganshi sai ya firgita ya juya ya koma gida wajen Khadija(R.A) yana cewa : ku lullu~e ni ! ku lullu~e ni !!. Sai Allah ya sau}ar masa da wahayi cewa : « Ya wanda ya lullu~a da mayafi.* Ka tashi domin kayi garga]i wa mutane.* Kuma ka girmama Ubangijinka.* Kuma ka tsarkake tufafinka”. [ suratul Muddassir, Aya:(1-4) ].

Wa]annan ayoyi sun }unshi umarni ne ga Annabir daya tashi yayi garga]i wa mutanensa ga barin shirka ya kuma }ira su i zuwa ga bautar Allah shi ka]ai. Daga nan ne fa Annabir yayi ]amara ya zage damtse ba dare ba rana ya fara }irar yara da manya, maza da mata, ‘ya’yaye da bayi, ba}i da fari kan azo a bauta wa Allah ma]aukakain sarki.Sai aka samu cikin kowace {abila wa]anda Allah ya nufe su da shiriya da samun rabo duniya da lahira suka amsa }irarsa,suka musulunta. Kafiran Makka sai suka fara cutar dasu suna gana musu ba}ar azaba, amma Annabir Allah ya kare shi ne daga cutarwarsu ta hanyar baffansa Abu-[alib, domin ya kasance mutum ne mai daraja da fa]a-aji a cikinsu, don haka baza su iya cutar da Annabir da komai ba saboda sun san irin son da yake yi masa.

Imam Ibnul Jauzi yace : Annabir ya zauna a Makka tsawon shekaru uku yana Da’awarsa a ~oye, bayan sau}an fa]in Allah ta’ala : « sai ka tsage gaskiya game da abin da aka umarceka dashi, ka kuma kau da kai daga masu shirka ». [ suratul   Hijri,Aya :(94)],sai Annabir ya fara Da’awarsa a bayyane. Lokacin da fa]in Allah ta’ala ya sau}a : « kuma kayi garga]i ga danginka mafiya kusanci ».[ suratu Ashshu’ara’I, Aya:(214)]. Sai Annabir ya fito ya hau dutsen Safa yayi kira da }arfi yace : Ya ku mutane na !! sai mutane suka ce wa ye yake }ira ?!sai akace : ai Muhammadu ne, sai suka zo suka tattaru, Annabir yace dasu : Ya ‘ya’yan gidan wane da wane………, Ya ‘ya’yan gidan Abdu manaf, ya ‘ya’yan gidan Abdul-mu]allib………..yanzu zaku gaskatani in nace muku wani doki zai fito ta }ar}ashin wannan dutsen ?! sai suka ce : }warai da gaske, domin kuwa baka ta~a mana }arya ba, sai yace dasu : to ha}i}a ni mai garga]i ne agare ku kafin zuwan azaba mai tsanani(ga wanda ya}i yin Imani). Sai baffansa Abu-lahab yace : « tir da kai yanzu da ma don wannan kawai ka taramu »,sai ya tashi ya tafi, sai Allah ta’ala ya sau}ar da suratul Masad cewa : «  Hannaye biyu na Abu- lahab sun halaka kuma ya halaka……. » har zuwa }arshen surar. [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].

 1. JURIYAR ANNABIr KAN CUTARWAR DA AKE MASA:

Annabir ya kasance mai ha}uri ne da neman lada kan duk abubuwan da yake fuskanta daga mutanensa na wahalhalu da tsanani. Har ma ya kai ga cewa ya umarcin sahabbansa da suyi hijira zuwa }asar habasha(Eutopia) don guje wa zalunci da }as}ancin da suke fuskanta, sai suka aikata hakan.

Babban malamin tarihin nan (Ibn- Ishaq) yace: lokacin da baffan Annabir ( Abu-[alib) ya rasu, sai {uraishawa suka fara cutar da Annabir cutarwa mai tsanani wadda basu ta~a tsammanin zasu iya masa irinsa ba lokacin baffansa yana da rai. Abu-Nu’aim ya ruwaito hadisi daga Abu-Huraira(R.A) yace: lokacin da Abu-[alib ya rasu sai {uraishawa suka }untata wa Annabir, har Annabir ya ke cewa: Ya baffana!! Ban ji da]in rashinka da nayi ba.!!

Hadisi ya zo cikin Bukhari da Muslim cewa: wata rana Annabir yana sallah a masallacin  {a’aba, sai Uqbah ]an Abi-mu’ai]  ya ]auko mahaifar Ra}umi ya zuba a bayan Annabir, Annabir bai ]ago daga sujjada ba har sanda ‘yarsa Fa]imah tazo ta ]auke, sai Annabir a lokacin yace: “Ya Allah ka dam}i wane da wane cikin {uraishawan nan”. Hadisi ya zo cikin Bukhari cewa:”wata rana Uqbah ]an Abi –mu’ai] yazo ta bayan  Annabir sai ya sha}e shi sha}a mai tsanani, har sanda Abubakar(R.A) ya zo ya ture shi yace: don me zaku kashe mutum(Annabir) haka kawai don ya ce ubangijinsa shine Allah?!!”.

11. RAHAMAR ANNABIr DA TAUSAYINSA  GA MUTANENSA:

Lokacin da cutarwa ya tsananta ga Annabir bayan rasuwar Abu-[alib da Khadija(R.A) ; Annabir sai ya fita daga Makka ya nufi garin [a’if, anan ne ya }ira }abilar Sa}iif i zuwa ga musulunci, saidai kash !ha}o bai cimma ruwa ba, domin kuwa basu tari Annabir da komai ba in banda cutarwa mai tsanana da izgilanci da tsaurin kai, har ya kai ga cewa sun jejjefe shi da duwatsu suka ji masa rauni a }afafuwarsa, daga }arshe Annabir sai ya yanke shawarar dawowa garin Makka. Annabir yace : « Na kamo hanyar dawowa daga [a’if ina cike da ba}in ciki, ban fa]aka ba har sanda na zo gurin da ake }ira {arnus-sa’alib (mi}atin mutanen Najd), ina ]aga kaina sai ga wani girgije yamin inuwa, dana duba sai naga ashe mala’ika Jibril ne a ciki, sai ya }ira ni yace : ha}i}a Allah yaji abin da muta nenka suka gaya maka, da kuma martanin da sukayi maka, yanzu haka Allah ya aiko maka da mala’ikan dake ri}e da duwatsu ne don ka umarce shi da duk abin da kaso ayi dasu. Sannan sai mala’ikan dake ri}e da duwatsu ya }ira ni ya min sallama yace : Ya Muhammad ! ha}i}a Allah yaji maganar da mutanenka suka maka, kuma nine mala’ikan dake ri}e da duwatsu, Allah ya turoni ne don ka umarce ni da duk abin da kaso, in kaso yanzu sai in kifar da wa]annan manyan duwatsun a kansu ? sai Annabir yace :a’a kada ayi musu haka, saidai ina fatar Allah zai fitar daga tsatsonsu wa]anda zasu bauta wa Allah shi ka]ai kuma bazasu masa tarayya da komai ba ».   [ Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].

Kuma Annabir ya kasance yana fita a mausimi(duk lokacin da za’ayi wani taro na musamman) don ya bijirar da da’awarsa ga {abilun larabawa yana cewa :Waye zai bani mafaka ?. Waye zai taimake ni ?, domin {uraishawa sun hana ni isar da sa}on ubangijina ! ».

A lokacin mausimi, Annabir sai ya ha]u da mutane shida daga cikin mutanen  Madinah  a gurin da ake }ira Aqabah, ya }ira su izuwa ga musulunci sai suka musulunta, sai suka koma Madinah suka cigaba da }ira, har musulunci ya watsu a garin Madinah. Sannan akayi mubaya’ar Aqaba ta farko da ta biyu dukkansu a ~oye, lokacin da aka umarci Annabir da wa]anda suke tare dashi dayin hijira zuwa Madinah,sai suka fita ]aya-bayan-]aya.

12. HIJIRAR ANNABIr ZUWA MADINAH :

Sai Annabir da Abubakar(R.A) suka nufi kogon Saur suna masu hijira zuwa Madinah, suka zauna cikin kogon tsawon kwanaki uku, don haka labarinsu sai ya ~ace wa {uraishawa. Lokacin da Annabir da Abubakar suka shiga Madinah, sai mutanen garin suka kar~e su hannu bibbiyu, sai Annabir ya gina masallacinsa da masau}insa.

13. YA}U}UWAN  DA ANNABIr YAYI A  RAYUWARSA:

An kar~o hadisi daga Ibn Abbas(Allah ya }ara masa yarda) yace: ”lokacin da Annabir ya fita daga garin Makka yana mai hijira, sai Abubakar(R.A) yace: wa]annan mutane ({uraishawa) sun shiga uku sun lalace!! Ta yaya za’ayi su fitar da Annabinsu daga garinsa!! Sai Allah ma]aukakin sarki ya sau}ar da fa]insa : « An yi izini ga wa]anda ake yakarsu da cewa lalle an zalunce su, kuma lallai hakika Allah mai iko ne kan taimakonsu ».[suratul Hajji, Aya :(39)]. Itace aya ta farko data sau}a tana umarni da ya}i. Ya}u}unan da Annabir yayi a rayuwarsa guda Ashirin da bakwai(27) ne, wa]anda ya}i ya faru a cikinsu guda tara(9) ne, gasu kamar haka :

1.Badr. 2.Uhud. 3.Muraisi’i. 4.Khandaq.    5.Bani-{uraiza. 6. Khaibar. 7. Fathu-Makka. 8. Hunain.  9. A]]a’if.

Kuma ya aika Sariyyah(rundunan ya}i }ar}ashin jagorancin wani sahabi) guda hamsin da shida(56).

14. HAJJIN ANNABIr DA UMARARSA :

Annabir bai yi hajji ba bayan hijirarsa zuwa Madinah sai hajji guda ]aya wadda shine ake }ira Hajjatul-wada’i(wato hajin ban-kwana). Annabir yayi umara ne sau hu]u (4) a rayuwarsa, dukkaninsu cikin watan Zul-{a’ada ne banda wacce yayi tare da hajinsa, gasu kamar haka :

1.Umarar Hudaibiyya(wacce kafurai suka hana shi shiga garin Makka). 2. Umarar {ada’i. 3. Umarar Ju’uranah. 4. Umarar da yayi tare da hajinsa.

15. SIFFOFIN  ANNABIr :

Annabir ya kasance mutum ne madaidaici, kuma ya kasance fari ne mai ha]e da ja, yana da gashi mai yawa, mai tsananin ba}in ido ne, kuma ya kasance ba yi da gashin da ya lullu~e  gaba ]aya kan }irjinsa da cikinsa, yana da gashi a tsakiyar }irjinsa da cikinsa.

16. HALAYEN  ANNABIr :

Annabir shi yafi kowa kyauta, da fa]in gaskiya, da taushin hali, da iya zamantakewa, Allah ma]aukakin sarki yace: “ kuma lallai hakika kana kan halayen kirki ma]aukaka”.[suratul {alam, Aya:(4)]. Kuma Annabir yafi kowa jarunta da kamewa da }an}an-da-kai, kuma ya kasance mai matu}ar kunya ne fiye da budurwa a tarbukanta, ya kan kar~i kyauta kuma yayi sakamako akai, amma baya kar~ar sadaqa kuma baya ci, kuma ya kasance ya kanyi fushi idan an keta ha}}in Allah ma]aukakin sarki, amma baya fushi idan an keta ha}}insa, kuma ya kasance yakan ci gwargwadon abinda ya samu, baya }i ko mayar da abinda Allah ya bashi, kuma baya }wa}}wafi da bi-biyan abinda bai bashi ba, kuma ya kasance baya cin abinci a kishingi]e ko akan teburi, kuma ya kasance watanni uku sukan shu]e a gidansa ba a ]aura tukunya akan murhu ba don girka abinci, kuma ya kasance yana zama da talakawa da miskinai, yana kuma ziyartan marasa lafiya, kuma ana zuwa ma}abarta dashi.

Annabir ya kasance ya kanyi raha amma baya fa]in }arya cikinsa, kuma baya }yal}yalewa wajen dariyarsa( wato murmushi yake yi), kuma ya kasance mai hidima ne ga iyalensa, yace: “ mafi alkhairin cikinku shine wanda yafi ku kyautata wa iyalensa, nine kuwa nafi ku kyautata wa iyalaina”.[Tirmizi ne ya ruwaito shi, Albani kuma ya ingantashi]. Anas bn Malik(R.A) yace: “ nayi yaron gida wa Annabir tsawon shekara goma(10), amma bai ta~a zargi na ba kan wani abu dana aikata kan cewa; don me na aikata kaza? Ko kuma kan wani abu da ban aikata ba cewa; don me baka aikata kaza ba?!!.

Annabir bai gushe ba yana tausasa wa dukkanin halitta, yana kuma nuna musu ayoyi da abubuwan gagara-koyo da suke nuni akan manzancinsa,daga ciki akwai kamar: tsagewar wata (lokacin da {uraishawa suka nemi shi da yayi addu’a hakan ya faru), ~u~~ugar ruwa daga tsakankanun yatsunsa, nusantawar da kututture yayi masa(lokacin da Annabir ya bar tsayuwa akansa don hu]uba), kawo kukan da Ra}umi yayi gurinsa, bugu da }ari kuma; ya bada labarin abubuwan gaibu da zasu faru sai suka faru kamar yadda ya fa]a, d.ss.

17. FALALAR  ANNABIr:

An kar~o hadisi daga Jabir ]an Abdullah(R.A) cewa Annabir ya ce: an bani wasu abubuwa guda biyar wa]anda ba a ba dasu ba ga wani Annabiu da yazo gabanina: (1). an taimake ni da tsorata abokan gaba wa]anda tsakanina dasu akwai nisar tafiyar wata guda. (2). an sanya min }asa ta zamo tsarkakakkiya (wajen yin taimama) kuma gurin sallah, don haka; duk  wanda sallah ta riske shi a hanya sai ya tsaya yayi. (3). kuma an halattamin cin ganima wacce bata halttaba ga wani Annabi daya zo gabanina. (4). an bani damar yin ceto( a farfajiyar {iyama).       (5). Annabawan da suka zo gabani na sun kasance ana aikosu ne zuwa ga mutanensu kawai; ni kuwa an aiko ni ne zuwa ga mutane baki ]aya”. [Bukari da Muslim ne suka ruwaito shi].

Ya zo a cikin sahihu-Muslim a hadisin Anas(R.A) cewa Annabir yace: “Ni ne farkon wanda zai fara yin ceto ranar {iyama, kuma nafi dukkan Annabawa samun mabiya ranar {iyama, nine  kuma zan fara }wan}wasa }ofar Aljanna don a bu]e”. Ya zo a hadisin Abu-huraira (R.A) cewa Annabir yace: “Ni ne shugaban ‘yan-Adam  ranar {iyama, kuma ni ne farkon wanda zai fara fitowa daga kabari ranar {iyama, ni ne kuma farkon wanda zaiyi ceto,kuma farkon wanda za’a bashi damar yin ceto”.

18. IBADAR ANNABIr DA SALON  RAYUWARSA:

A’ishah (Allah ya }ara mata yarda) tace : Annabir ya kasance yakan yi sallar dare har }afafuwansa su kumbura su tsatstsage, sai aka ce masa ; Annabir don me kake haka bayan kuwa an gafarta maka zunubanka?!! Sai yace : to ai ya dace in zamo bawa mai godiya(kan ni’imomin da akamin).[Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]. Ta cigaba da cewa : kuma shimfi]ar Annabir da yake barci akai fata ne wadda akayi masa cushe da tankan dabino. Ya zo a hadisin Ibn Umar(R.A) yace : ha}i}a naga Annabir yana kai-kawo bai samu abinda zai sa a ma}oshinsa ba, duk abinda ya rasa baya damunsa matu}ar na duniya ne, duk da cewa shine shugaban duniya gaba ]aya.

Muna godiya ga Allah ta’ala daya sanya mu cikin al’ummarsa, kuma yayi mana gam-da-katar dayi masa biyayya, kuma muna ro}on Allah ya tasar damu ranar {iyama cikin masu bin littafinsa da sunnarsa. Amin summa Amin.

 

MUHIMMAN ABUBUWAN DA  SUKA

FARU A  RAYUWARSAr:

ü  Isra’I da Mi’iraji(tafiyar da akayi dashi zuwa masallacin {udus da hawa da akayi dashi zuwa sama) : ya faru ne kafin ayi hijira zuwa Madinah da shekara uku, a lokacin ne aka farlanta salloli.

ü  Shekarar farko bayan hijira: hijira zuwa Madinah, gina masallacinsa, fara }o}arin kafa daular musulunci, farlanta Zakka.

ü  Shekara ta biyu: Ya}in Badr babba,(a cikinsa ne Allah ya ]aukaka muminai ya kuma ]orasu akan abokan gabansu).

ü  Shekara ta uku: Ya}in Uhud ; a wannan ya}in ne musulmai suka samu rauni saboda sa~awar da wasu daga cikinsu sukayi wa karantarwan Annabir da shagaltuwa wajen ]iban ganima.

ü  Shekara ta hu]u : ya}in Banin-Nadiir; a wannan ya}in ne Annabir ya fitar da yahudawan Banin-Nadiir daga Madinah saboda warware al}awari da sukayi.

ü  shekara ta biyar: ya}in Banil- Mus]alaq, ya}in Ahzab, ya}in Bani- }uraiza.

ü  shekara ta shida: sulhun-Hudaibiyya, kuma a wannan shekarar ne aka haramta giya har abada.

ü  shekara ta bakwai: ya}in Khaibar, a wannan shekarar ne Annabir da musulmai suka shiga  garin Makka sukayi umara, kuma a shekarar ne ya auri Safiyyah ‘yar Huyayyi.

ü  shekara ta takwas: ya}in Mu’uta(tsakanin musulmai da Rumawa), fathu- Makka, ya}in Hunain(tsakanin musulmai da {abilun Hawaz da sa}iif).

ü  shekara ta tara: ya}in Tabuk; wannan shine ya}i na }arshe da Annabir yayi a rayuwarsa, kuma a wannan shekaran ne mutane suka zo gurin Annabir suka shiga musulunci }ungiya-}ungiya, shi yasa ake }irar wannan shekarar “shekarar wufudi”.

ü  shekara ta  goma: hajin ban-kwana, a shekarar ne Annabir yayi haji tare da musulmai sama da dubu ]ari.

ü  shekara ta goma  sha ]aya:  a farkon wannan shekarar ne Annabir ya rasu, ya rasu ne ranar litinin cikin  watan Rabi’ul- Awwal duk da cewa anyi sa~ani wajen }ididdige kwanan watan. Annabir ya rasu ne yana da shekara sittin da uku (63) a rayuwarsa, Arba’in (40) daga ciki kafin ya zamo Annabi, ashirin da uku(23) kuwa yana annabi kuma manzo, shekara goma sha uku (13) daga ciki yayi su ne a Makka, sauran goman (10) kuma a Madinah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa da sahabbansa).

Ya ‘yan’uwa musulmai!! Ku duba irin wannan rayuwa ta Annabir !Shin haka rayuwarmu take?!!Ko dai bamu sakankance bane cewa wannan annabi shine annabin da aka aiko mana ?!! ku tuna da fa]in Allah ma]aukakin sarki da yake cewa :   « Hakika kuna da abin koyi mai kyau game da manzon Allahr…… ». [suratul Ahzab, Aya :(21)]([1])

*           *          *

BAYANIN WURAREN DA AKA CIRO

 MAGANGANU:

 1. “Tahzibulasma’Iwallugaat”  na Imam Nawawi.
 2. “Attabsiratu-walhada’iq” na Imam Ibnul Jauzii.
 3. “Zadul-Ma’aad” na Imam Ibnul {ayyim.
 4. « Assiratun-nabawiyya »   na Imam Azzahabi.
 5. “Jawami’is-siratin-nabawiyya” na Imam Ibn Hazm.
 6. “Alfusul fi siratir-rasul” na Imam (Ibn Kasiir).
 7. “Sahihus-siratin-nabawiyya” na Ibrahimul- Alii.

Mai fassara: Muazu Abba Jabir


(1) baya daga cikin maganar mawallafin.

Bikin aurar da matasa (3000) Lokaci Guda

Duk da wadata  da yalwar arzuki da kasar Saudiyya take ninkaya a ciki, sai dai mutum zai sha mamaki idan aka bincina masa kadan daga matsalolin da matasan kasar suke fuskanta gameda aure.

Budurwa ta kai shekara talatin ko arba’in, ko ma fiye ba ta taba aure ba, ya zama ruwan dare gama duniya a kasar, samari da ‘yan matan da suke ganin tsakaninsu da aure sai dai ko a aljannah kuwa Allah ne kadai ya san yawansu.

Abubuwa da dama ne suka hadu suka haifar da wannan matsala, amma dai za’a iya cewa kashin bayan matsalar shi ne T SADAR AURE inda wani dansa zai shiga makarantar faramare amma mahaifinsa bai gama biyan bashin da ya ci a auren mahaifiyar yaron ba!

Sadakin  Riyal dubu hamsin (Naira milyan biyu da doriya) ba wani sadaki ne na gani na fada ba, tun da yakan kai har dubu dari!

Wannan a sadaki kawai kenan, ba’a maganar biki wanda shi ma guda ne babariba, don akalla yakan lankwame kwatankwacin abin da sadakin ya lamushe, kai wani lokacin ma har ninninkawa yake yi!

Sannan ga maganar gidan haya da tarkacen da za’a zuba a ciki, da motar bashi, da tafiya wani gari, ko ma wata kasa don a ci amarci da angwanci da tsinke (Honey Moon)…

Wannan kuma duk  ba’a zo maganar karkon auren ba, don ita ma Magana ce mai zaman kanta.

Duba da yadda wannan matsala take nema ta illata al’ummar baki daya ta bangarori da dama, wasu kungiyoyin taimakon jama’a a kasar –musamman wadanda suke mayar da hankali akan rayuwar iyali- suka tashi haikan wurin murkushe ta, da salo, da dabaru iri iri, daya da ciki shi ne: Hada ma’aurata da dama a biki guda, tare da ba su gudunmawa ta musamman kafin, da lokacin, da kuma bayan auren don saukaka musu al’amura.

Za’a iya kasa irin wannan aure na taimakekeniya zuwa kashi biyu:

Na Farko: Wanda dangi, ko kabila,  ko unguwa daya suke yi tsakanin ‘ya’yansu.

Na Biyu: Wanda cibiyoyin taimakon al’umma  suke yi.

An fara wannan tsari karkashin irin wadannan cibiyoyi na alheri tun sama da shekaru goma da suka shude, kuma abin ya yi tasiri ba dan karami ba, shi ya sa ma kullum yake kara samun karbuwa tsakankanin matasa da iyayen angwaye  da amarye duk da  cewa ya saba da ala’adun larabawa.

A sati dayan nan da ya shude kadai an yi bikin aurar da matasa sama da dubu uku ta wannan hanya.

 • Ranar Juma’a 10/6/2011 bikin aurar da “Marayu” 100  na farko karkashin gidan Marayu na Insaan a Riyadh.
 • Ranar Laraba 22/6/2011 bikin aurar da matasa  800 (]ari takwas) a Jizan karo na takwas karkashin cibiyar saukaka aure ta Jizan
 • Ranar Asabar 25/6/2011 bikin aurar da matasa dari biyu a Sharkiyya  karo na farko karkashin cibiyar Wi’am a Dammam
 • Ranar Lahadi 26/6/2011 bikin aurar da matasa dari biyu karo na tara a Ahsa’a
 • Ranar Laraba 29/6/2011 bikin aurar da matasa  1000 (dubu) a Madina karo na uku  karkashin cibiyar Usraty
 • Ranar Laraba 29/6/2011 bikin aurar da matasa 1200 (dubu da dari byu) karo na goma sha biyu a Jiddah  karkashin cibiyar Mawaddah.

 

Gudunmawar da ake ba wa wadannan matasa takan saba daga gari zuwa gari, hakanan yawa da karancin angwayen da amaren, amma dai a dunkule tana kunsar abubuwa kamar:

 1. Dauke musu nauyin taron biki wanda na bayyana a baya cewa yana lamushe dubunnan Riyal barkatai
 2. Kyautar kudi,kamadaga Riyal dubu biyar har zuwa dubu talatin
 3. Kyautar set ]in kayan ]aki (gado, kujeru, kwaba… dss)
 4. Kyautar kayayyakin lantari (Tukunyar sanyaya daki Ac– biyu zuwa sama- firinji,  injin wanki, injin shara, rishon gashe-gashe dss).
 5. Set din gwal ga amarya.
 6. Kwasa-kwasai daban dabankansanin makama  da  yadda ake gudanar da rayuwar iyali, hada da shedar halarta.
 7. Kyaututtuka kala kala da sukan hada har da  motar hawa sabuwa fil  da gwala-gwalai dss. (ta  hanya kur’ar mai rabo ka dauka).

Wadannan cibiyoyi sukan sa sharadai na wanda zai cancanta irin wannan tagomashi, ala misali sharadan  cibiyar Usraty ta Madina sun hada da:

 • Angwon ya zama dan Madina ko daya daga cikin kauyukanta
 • Shedar auren da ba ta wuce shekara ba, mai satamfin kotu a jiki.
 • Kada sadakin da zai bayar ya wuce Riyal 35000 (Dubu talatin da biyar. Kwatankwacin Naira milyan daya da rabi).
 • Ya zama yana da aikin yi, kuma gundarin kudin shigarsa a wata bai wuce Riyal 3000 (dubu uku).
 • Halartar kwasa-kwasai na musamman  da cibiyar take gabatarwa ga masu shirin aure.

Duk wanda ya cika wadancan sharadai to ya cancanji wannan goma ta arzuki.

Ranar larabar da ta shude (29/6/2011) ne aka yi wannan gagarumin biki a Jiddah da  Madina kamar yadda ya gabata, kuma Allah ya sa na samu damar halartar na Madinan tun daga farko har karshe. Tsarinsa  ya burge ni kwarai, kuma na ga alamar ya  ya kayatar da  mahalarta. Abin sai wanda ya gani.

An yi taron ne a rufaffan dakin taron babban filin wasan kwallo na sarki Muhd. Ibn AbdulAziz dake Madina.

An kawata dakin kwarai da fitilu iri iri masu daukar hankali, kai har da fitulun kwai irin namu na gargajiya guda talatin da daya saboda tuna da!

An karaso da angwayen wurin taron bayan an kewaya garin Madina da su  a cikin manyan motoci (masu cin mutane hamsin) guda goma, ga tarin  babura nan  na samari suna jagorantar motocin, cikin farin ciki da ‘yan wakoki da  bushe bushe da mahaya baburan suke yi wadanda dukkanisu samari ne.

Bayan angwayen sun yi sallar Isha’i, sai suka shigo wurin taro a tsanaki cikin farin ciki, kowanennesu sanye da doguwar riga fara, da hula, da Gutrah (Rawani  ko yafen kai irin na ‘yan Saudiyya) su ma duka farare, da Iqal  (Kwarkwaro n da suke sawa a saman yafen) baki,  sannan ga  tsantsareriyar Mishlah (Alkyabba) ruwan madara kowanne ya zubo ta.

Sarkin Madinamai Martaba AbdulAziz Ibn Majid Ibn Abdul Aziz ya karaso dakin taron karfe 10:8 na dare, ana ta yi masa kirari, da ya zauna sai aka sanya  wani bangare na kiran sallar masallacin manzo, sannan kuma sai taro ya fara.

Mashahurin makarancin nan, malami a jami’ar Musulunci ta Madina, kuma tsohon limamin Masallacin Manzon Allah (SAW) Dr. Muhammad Ayyub shi ya bude taron da karatun Alqur’ani, inda ya rangada tilawar ayoyi shaukun karshe na Suratul Furqan.

Sannan kuma sai wasu kwararrun mawakan gargajiya suka kasa angwayen kashi biyu, sannan suka  jagorance su baki daya suna ta rera wakoki irin nasu na gargajiya, ga guda nan ana ta yi daga dakin taron mata inda amaren suke,  sannan suka taho da su a wani tsari na layi da tafiya  mai ban sha’awa, suka kewaya sarki da shauran mahalarta suka gan su, suka  taya su murna, kuma saka yi musu addu’a  ta alheri.

Bayan sun koma sun zauna sai wata kungiyar masu rawar gargajiya irin ta yan su (masu kamun kifi) suka zo suka cashe, sannan sai aka harba fitilu masu kyalkyali, duk don nuna farin ciki.

Bayan nan kuma sai Babban sakataren cibiyar ta Usrati, wadda ta tsara wannan biki, wato Dr. Abdul Bari Atthubaiti, limami a masallacin manzo, kuma babban alkali a babbar kotun Madina ya yi jawabin sa, inda ya godewa Allah bisa tallafin da ya yi musu na iya  gabatar da wannan hidima ga matasansu, sannan ya yi bayanin mahimmancin irin wannan aiki a musulunci, ya kuma kwadaitarwa kan a rika bayar da gudunmawa don gudanar da shi,  daga bisani kuma ya godewa mahukunta kasar musamman sarkin Madina, babban bako, kuma shugaban kwamatin gudanarwa na cibiyar bisa hadin kai da kaimi, da karfin gwiwa da yake ba su, da kuma duk wanda ya bayar da gudunmawa, ko ta shawara, ko tunani, ko kudi … ko fatan alheri, ko ma halarta wurin taron.

Sannan aka kuma yin wakoki, sai kuma wakilin kamfani Haadiya Abdul Ladif Jamil ya gabatar da jawabi a madadin kamfanoni da cibiyoyi da mutanen  da suka bayar da gudunmawa.

Sai aka kuma yin ‘yan wakoki, aka sa jawabin sarki Abdallah na tagomashin da ya yi wa ‘yan kasar na bayar da kyautar Riyal dubu daya duk wata ga duk mai neman aiki har ya zuwa ya samu, sannan kuma sai aka yi raywarsu ta gargajiya da ake yi da takubba da sanduna.

Daga nan kuma sai aka yi kuri’ar mai rabo ka dauka na abubuwa uku:

 1. Motoci uku sababbi fil kirar Hyundai 2011
 2. Kayan daki (gado, kujeru, kwaba dss)  guda goma
 3. Set din gwal guda biyar

An  rubuta sunan kowane ango a jikin takarda, aka sa a cikin wani gilashi aka juya su baki daya, sannan wata ‘yar karamar yarinya da ba ta wuce shekara shida ba da aka caba wa ado ta zo- a bainar jama’a-  ta dauki takarda daya daga cikin takardun nan dari biyar, ta kai wa mai gabatarwa, shi ma take a nan ya bude ya karanta sunan wanda ya ci mota ta farko, aka kira shi nan take sarki ya danka masa makullin motar,  sannan ta kuma daukowa, aka karanto  wanda ya ci ta biyu, shi ma ya zo ya karbi makullin…. Haka dai har zuwa kyautar karshe.

Daga nan  sai aka bai wa mahaifin amaryar da sakadinta ya fi na kowacce karanci a wadanda aka yi musu bikin, inda ya rangwanta ya karbi Riyal dubu goma kacal! (Kimanin Naira dubu dari hudu da talatin)! An ba shi kyauta ne don ragowar iyaye su yi koyi da shi wurin karbar sadaki kadan kamar yadda ya yi!

Sannan kamfanin waya na STC shi ma ya bai wa kowane daya daga cikinsu kyauta, hakanan ma cibiyar Usrati (amma wadannan kyaututtuka ba a wurin aka raba su ba).

Dama kuma a jawabin Babban sakataren cibiyar liman Thubaiti ya bayyana cewa cibiyar Salih Al-Rajihi  ta dauki nauyin kai gabadayan angwayen da amarensu  haji bana, har da karin wasu ma’auratan dari biyar.

Wannan ita ma ba karamar dankwaleliyar kyauta ba ce, don jumullar kudin da ta ci: Riyal milyan bakwai da rabi (Riyal 5000×1500) (Kimanin Naira 322,500,000).

Idan ka san yadda zuwa haji yake yi wa matasan Saudiyya wahala, za ka san cewa in ba irin wannan damar ba, to wasu da dama daga cikin wadannan matasa ba za su iya sauke farali ba sai nan da shekaru masu tarin yawa in ma sun iya saukewa.

Daga nan kuma sai sarkin Madina ya mika kyaututtukan da cibiyar ta tanada ga wadanda suka bayar da gudunmawa da suka hada da kamfanoni, cibiyoyin agaza wa jama’a, da  kafafan yada labarai,  dss.

Sannan kuma ya je, shi da liman Thubaiti babban sakataren Usrati suka yi hoto su da angwayen don tarihi.

Bayan an ci abincin dare, kowane ango ya je ya dauki amaryarsa ya yi gaba.

Sarkin Madina AbdulAziz ibn Majid, daLimamin Haramin Madina Dr. AbdulBari Athubaiti, da wasu daga cikin angwaye a Madina.

A hirar da na yi da jami’in yada labarai na Usrati, Ustaz Nadim Bakhsh ya bayyana min cewa  jumullar gudunmawar da  ma’auratan suka samu daga cibiyar Riyal milyan shida ne (Kimanin Naira 258,000,000)- ban da kudin kai su hajji- kamar yadda ya bayyana min cewa kudin da aka kashe a wurin taron ya doshi Riyal 500,000 (Kimanin Naira: 21,500,000)

Yanzu abin tambaya a nan shi ne:

 1. Ina wadannan cibiyoyi suke samun kudaden da suke yin irin wannan hidima?
 2. Menene tasirin irin wannan gudunmawa a cikin al’ummarsu?
 3. Me za mu koya daga irin wannan hobbasa a kasashenm?

Game da tambaya ta daya, to suna samun kudinsu ne daga:

 • Daidaikun mutane kowa dai dai karfinsa. Misali:  motoci biyu daga cikin ukun da aka yi kura’ar mai rabo ka dauka a Madina, set din gwala-gwali biyar, set din kayan daki guda goma, daidaikun mutane ne suka dauki nauyin hakan kamar yadda aka bayyana a wurin taron.
 • Cibiyoyi da kungiyoyi taimakon jama’a, kamar cibiyar Salih Al-Rajihi, wadda ita kadai ta dauki nauyin bikin aurar da matasa (maza da mata) dari takwas a Jizan, da dari biyu a Ahsa’a. da kai gabadayan na Madina har da karin dari biyar hajji. A wurin bikin aurar da wadancan matasa 800, babban sakataren kwamatin amintattu na wannan cibiya ta alhaeri ya bayyana cewa duk shekara  cibiyarsu tana kashe Riyal milyan goma  shatakwas (kimanin Naira milyan dari bakwai da saba’in da hudu) wurin aurar da samari da ‘yan mata 4000 (dubu hudu) a sassa daban daban na Saudiyya. Ka tuna aurar da matasa daya daga cikin tarin ayyukansu.
 • Kamfanoni daban daban kamar kamfanin Haadiyah Abdul-Ladif Jamil na wata ‘yar kasuwa a kasar. Wannan baiwar Allah mai suna Haadiyah- ta hanyar wannan kamfani nata-  ita ta bayar da kusan rabin gudunmawar da aka baiwa matasan a Madina a bikin bana, don said a ta bai wa kowane ango da amarya mahimman kayayyakin lantarki da suke bukata a gidansu (Ac uku, firinji daya, injin wanki daya, injin shara daya, rishon gashe gashe daya… dss) don haka a bikin Madina  na bana kadai ta bayar da kyautar: Ac 1500, firinji 500, injin wanki 500, injin shara 500, rishon gashe gashe 500. Bugu da kari, ba a Madina kadai take bayar da irin wannan gudunmawa ba, har da wasu daga sassan kasar, kamar yadda ba bana ta fara ba.
 • Zakkah (Manyan malaman Saudiyya sun bayar da fatawa cewa za’a iya ba irin wadannan cibiyoyin zakka don gudanar da irin wadannan ayyuka).

Ya kamata wasu  tambayayi biyu su haifu daga wannan tambayar ta farko, wadannan tagwayen tambayoyi su ne: Ya aka yi wadannan masu kudi suke  ciyar da dukiyoyinsu a irin wadannan ayyukan alheri, kuma ya aka yi irin wadannan cibiyoyi suke iya gamsar da kamfanoni da masu kudin  har suke iya yi musu marka-markar kudi haka?

Gameda da abin da ya shafi karfin halinsu wurin ciyar da dukiyoyinsu ta wannan hanya, ni a ganina akwai dalilai da dama da suka sa suke yin haka. Ga wasu daga ciki:

 1. Imaninsu da alkawarin Allah (SWT) cewa wanda ya ciyar ta farkinSa zai ninninka masa, da fadin Manzon Allah (SAW) cewa “Kudi bai taba raguwa ba don an yi sadaka da wani bangare nasa).
 2. Nemankudi da manufa, ma’ana sun san me yasa suke neman kudi, kuma yin irin wadannan ayyuka da kudaden nasu yana daga cikin manufofinsu na nemansu, don haka lokacin da suke ciyar da kudinsu ta wannan hanyar suna jin cewa suna cimma wani mahimmin buri ne a rayuwarsu.
 3. Alamar cewa suna kwatanta cin halak da fitar da hakokkin Allah a dukiyarsu, domin wanda yataradukiyarsa ta hanyar haram bai fiya samun dacewar yin irin wadannan kyawawan ayyukan ba.
 4. Tarbiyantarsu da aka yi akan bayarwa, ba akan karba ba
 5. Tausayi da rahama da jinkan talakawa dake zukatansu. Dss

Gameda yadda irin wadannan cibiyoyin suke iya gamsar da su har su iya damka amanar kudadensu a hannunsu kuwa, ni a ganina wannan yana komawa zuwa abubuwa da dama wasu daga ciki su ne:

 • Kyakkyawar niyyar wadannan cibiyoyi. Bahaushe yana cewa wai “Farar aniya laya”
 • Amanarsu. Zai wahala ka ji an ce irin wadannan cibiyoyi sun ci amanar wanda ya ba su kudi su yi aikin alheri da shi, ko su raba a tsakaninsu.
 • Masu gudanar da su ba da wannan aikin suka dogara ba, don duk manyan ma’aikatan wuri za ka ga suna da harkokinsu daban, kai wasu ma masu kudin gaske ne.
 • Tsari da iya gudanarwa; domin idan mutum ya bayar da kudi a yi wani abu da shi, ko shi da kansa aka ce ya kashe kudin nan, da wahala ya iya kashe su yadda ya kamata, kuma ta hanyar da ta dace kamar yadda  su za su yi, don haka idan mutum ya ba su kudi ba ya jin cewa za’a barnatar masa, ko banzatar masa da dukiya.
 • Kiyaye sharuddan da mai kudin zai bayar; idan mutum ya ce ga kudi a gina rijiya, to fa ba yadda za’a yi su  yi wani abu da shi daban- kamar gina masallaci- sai sun nemi izininsa, ko kuma su dawo masa da kudinsa idan ba za su iya cika sharadinsa ba.
 • Yin komai a bude ba tare da rufa rufa ba; kowace shekara suna buga rahoto na musamman gameda da  abin da suka samu da abin da suka kashe,  da ayyukan da suka yi- hard a hotuna da maganganun wasu daga cikin wadanda suka amfana- da abin da suka sa gaba a shekara mai zuwa, da kudin da zai ci,  su yada kowa ya gani, sannan kuma sukan rubuta rahoto na musamman ga wanda ya ba su kudi mai kauri su yi masa bayani filla-filla na yadda suka kashe kudin, kuma su tambaye shi idan ya amince da yadda suka kashe, ko kuma yana da gyara a kai.
 • Tallata kamfanonin da suka ba su gudunmawa a jaridu da mujallu, da shafukan yanar gizo, da sanarwarkanhanya ta hanyar sanya sunayensu da tambarinsu da bayanin cewa wadannan kamfanoni ne suka dauki nauyin wannan aiki. Suna yin haka a duk sanarwar da za su fitar mai alaka da shirin da za su yi. (Amma ban ga suna rubuta sunayen daidaikun mutane ba, sai dai kamfanoni, ko cibiyoyin taimakon jama’a).
 • Girmamawa wa]anda suka bayar da gudumawa da ba su shedar yabo,  a wurin taro.

Gameda da tambaya ta biyu kuwa– Manene tasirin irin wadannan gudunmawa a cikin al’ummarsu?

Gaskiyar lamari irin wannan  gudunmawa da sharye shirye suna  da tasiri  matuka a rayuwarsu, daga cikin irin wannan tasirin akwai:

 1. Yaduwar soyayya da kaunar juna tsakanin jama’a,  don haka za ka ga akwai karancin gaba da hassada da keta tsakanin mawadata da matalauta, saboda mawadaci zai yi wa talaka abin da ko mahaifinsa ba zai iya yi masa ba. Za ka jima kafin ka ji talakan Saudiyya yana zagin mai kudi.
 2. Hadin kai da dunkulewa tsakanin gabadayan al’umma; domin kuwa su dai wadanda ake bai wa wannan gudunmawa masu karamin karfi ne, amma kuma duk inda aka gabatar da irin wannan shiri za ka ga  sarkin yankin shi ne yake jagorantar shirin, sannan kuma malamai da limamai, da alkalai,  da sauran manyan mutane na yankin manyan baki, su kuma masu kudi su ne masu bayar da gudunmawa, ga talakawa nan kuma wadanda suka samu wannan taimako, sannan ga ragowar mutanen gari nan da suke taya su murna, kowane bangare yana yi wa dayan addu’a da fatan alheri.
 3. Rage matsalar rashin aure, tsakanin matasa.  Na fada a baya cewa ta kai akan samu samari da ‘yan matan da suke hakura da aure, kamar yadda za ka ga mata da yawa  sun  wuce shekara talatin, har sun doshi arba’in amma ba wanda ya taba kula su da niyyar aure, amma ta hanyar irin wannan shiri, da kuma wasu shirye shiryen da dama ana samun raguwar wannan bala’i.

Sai tambaya ta karse; Me za mu koya daga irin wannan hobbosa?

Gaskiya abubuwan da muke koya a irin wannan suna da tarin yawa, zan fadakar akan wasu kadan daga ciki wa la’lla su yi mana amfani:

 1. Neman dukiya ta hanyar halal; domin wanda yataradukiya ta hanyar haram da wuya ya samu dacewar yin irin wadannan ayyuka kamar yadda na fada a baya.
 2. Yan abu don Allah, ba don siyasa, ko neman suna, ko neman daukaka da bautatar da talakawa da cutatatar da su don an ba su wani abu daga dokiyar da Allah ya ba wa mutum ajiya ba. Ko kuma taimakawa mutum da nufin kai ma ya taimaka maka a nan gaba.  Ba shedar zukatan irin wadancan bayin Allah nake yi ba, don shinan gaibu sai Allah, amma dai yadda suke al’amuran nasu akwai alamar Allah a ciki, don za ka ga hidima ta milyoyin Riyal amma ba za ka san wanda ya yi ba, kai har shardantawa ma suke yi cewa  kada a fadi sunansu. Ko a  bikin da na halarta ranar Laraba a Madina, take a nan sarki ya bayar da sanarwar cewa wani bawan Allah ya bayar da kyautar karin motoci biyu sababbi ga angwayen- bai fadi sunansa ba-
 3. Ciyar da dukiyoyinmu tafarkin Allah madaukakin sarki, kamar ta hanyar irin wadannan ayyuka, gina masallatai, makarantu, asibitoci,  haka magunanun ruwa, daukar nauyin dalibai da masu bahasi, samar da ayyuka ga matasa dss, maimakon kashe kudi a abubuwan da in ba su cutar ba, to amfanin da suke da shi bai taka kara ya karya ba in har akwai shi, kamar batar da dukiya a fagen wasanni, kade kade da raye raye, tarurruka marasa asali a addini,  ci banza ci wofi, ko gantali kasashen duniya, saya wa matasa kwaya don bautar da su a fagen siyasa, kashewa matan banza dss. Daga cikin abin da ya kamata a yi tsokaci a kansa a nan akwai mugun nufin da wasu suke da shi wurin ciyar da dukiyoyinsu, sai su ba wa mutum kudi da yawa –watakila ma ba zai iya sarrafa su ba- su je wai ya je ya yi aikin alheri, amma a hakikanin gaskiya ba wannan ne a ransu ba, so suke su bata shi, su samu bakin maganar cewa kowa “Kowane gauta ma ja ne, sai in bai sha rana ba” “Malamai” aka fi danawa irin wannan tarkon don mugun nufi!
 4. Rashin dogara da gwamnati a komai. Wani abin da zai ba ka sha’awa a nan shi ne duk irin wannan hidindimu ba gwamnati ce take yi ba, sai dai kawai daidaikun jami’an gwamnati wanda ya yi niyya, kuma yana da hali, shi ma ya bayar da abin da zai iya – kamar a bara sarkin Madina shi ma ya bayar da kyautar motoci biyu- ko a rika dauka a albashinsa duk wata. To idan har a kasa irin Saudiyya kasar da ‘yan kasarta suke samun duk wani abin more rayuwa dai dai gwargwado, kasar da fetur ya fi ruwa arha, amma duk da haka ba sa  dogara kacokan akan gwamnati, ina ga mu da abubuwa da dama na lalurar rayuwa ba su wadata ba, ko ma babu su baki daya, bugu da kari, kullum  ita kanta gwamnatin kuka  take yi cewa ba za ta iya ba; sai an tallafa mata! Don haka danuwa maimakon kullum a zauna a dakali a yi ta takaici, ko a shiga gidan radio a yi ta babatu cewa gwamnati ba ta yi kaza ba, ko taki yin kaza, duba abin kai da sauran abokana za ku iya yi domin ku taimaki kanku da al’ummarku ko da gwamnati ba ta shigo ciki ba. Alhamdu Lillahi akwai wadanda suka fara irin wannan kokarin, kuma kullum ci gaba suke samu.
 5. Kokarin dogaro da kai. Yana daga cikin abubuwan da za su konawa mai hankali rai a ce wai matsalar mahaifiyar mutum ko kanwarsa, ko matarsa, ko dansa ko kanensa, ko makocinsa… dss, amma saboda akidar “Allah ya ba ku mu samu” da ta yi katutu a zakatan da yawa daga cikinmu, wai jira yake wani banasare daga kasar turai, ko balarabe daga kasar larabawa ya zo ya taimaka masa! Bayan zai iya tabuka wani abu! Wannan alama ce ta mutuwar zuciya da rashin kishin kai da kulafuci.  Don haka ya kamata mu rika kokarin warware matsalolinmu da kanmu ba sai mun jira wasu ba, kuma na tabbata za mu iya da izinin Allah.
 6. Kafa cibiyoyin taimakon jama’a masu zaman kansu da bayar da taimako ta hanyarsu. A cikin al’ummarmu akwai wasu da Allah ya datar da su, suke iya  ciyar da dukiyarsu ta hanyar alheri, kamar ciyarwa, kudin magani,  kudin makaranta, taimakawa malamai,  kai mutane hajji da umara, dss sai dai abin la’akari a nan shi ne, da zarar Allah ya karbi ransu, ko wadatarsu ta yi kasa, sai wannan aikin alherin ya yi rauni, ko ma ya tsaya. Wani bawan Allah a daya daga cikin jahohin arewacin Nijeriya ya sanya daruruwan marayu makaranta mai tsada, kuma ya dauki nauyin biya musu kudin makaranta, duk shekara yana kashe milyoyin kudi a wannan aikin alheri, amma yana rasuwa mafi yawancin yaran karatun ya gagare su, har makarantar kasan kasa suka kasa zuwa! Irin wannan da cibiya ya kafa mai kula da wannan ya samar mata da hanyar samun kudi, da da wahala wannan aikin alheri ya mutu da mutuwarsa,  Don haka ina kira ga masu halin da Allah azurta su da zuciya ta yin irin wannan taimako da su rika bude cibiyoyi, su sa masu amana, kuma kwararru wurin gudanarwa don gudanar da ita, kuma su sama musu hanyoyin samun kudi masu dorewa. Wasu cibiyoyin a Saudiyya manyan otel suke ginawa a kusa da harami, wasu kuma noma, wasu kuma su sayi hannun jari, wasu kuma sayen kadarori, wasu su ribar rubuce rubucensu dss. Na je wata makaranta a Afrika ta kudu a shekarun baya, sai naga wanda ya gina ta, ya gina wani babban gidan mai a jikanta, ya kuma mallaka mata shi, don ya zama daya daga cikin hanyoyinta na samun kudin shiga. Wannan hanya ta burge ni sosai!
 7. Bayar da kulawa ta musamman ga raunana a cikin al’umma. Na farko dai wadanda ake bai wa wannan taimako masu karamin karfi ne, sannan kuma a ba’a manta da nakasassu ba,  don bara waccan kungiyar kula da nakasassu ta Riyadh babban birinin Saudiyya mai suna (Harakiyya) matasa (maza da mata) dari da biyu ta aurar, bara

  Wasu daga cikin  angwaye  “Nakasassu”

  kuma saba’in da biyar, inda kowane ango da amarya suka samu gudunmawar Riyal dubu hamsin, bayan bikin da aka yi musu. Abin bai tsaya a nan ba, don kamar yadda ya gabata  sati ukun da suka wuce cibiyar AbdulAziz ibn Fahd marayu –wadanda suka tashi a gidan marayu- dari ta aurar, kuma shirinta na wannan shekara  shi ne ta aurar da  irin wadannan  marayun dubu a bangarori da dama na kasar.

 1. Daukar mataki a aikace don magance matsala, maimakon takaitawa akan korafi da takaici, ko mutum ya tafi da rayuwarsa a “adawa”!
 2. Fada da cikawa,  sau tari za ka ga wasu daga cikin mutane a kasashe irin namu sun bayar da gudunmawar kudi a wurin taro, amma karshenta kafin su fito sai an yi jan ido, wani lokacin ma sai dai a bar shi da Allah! Ko kuma mutum ya ce ya bayar da gudunmawar milyan daya misali, nan kuwa a zuciyarsa dubu goma ya yi niyya, ragowar ya fada ne don alfahari da burga, don haka bayan ya bayar da goman- in ya bayar kenan- ragowar sai dai a yi masa Allah ya isa!  Amma su a irin wadannan tarurrukan na su, sau tari  kafin ma a bayar da  sanarwar cewa wane, ko cibiya kaza ta bayar da gudunmawaR kaza, gudunmawar tuni  ta zo hannu. Alal misali kyaututtukan mai rabo ka dauka;  gwalagwalai, da sababbin motoci uku a Madina, da wasu sababbin guda bakwai aJidda.. dss, gurin taron ma aka zo da su, take a nan, a gaban jama’a za’a bude takarda, a karanto sunan mutum, a mika masa mukulli, ga motar nan a waje in ya so ya shiga abarsa ya yi gaba a lokacin.
 3. Dorewa akan aikin alheri, za ka ga duk irin wadannan ayyuka in aka fara  su, to an fara kenan kullum sai dai su yi gaba, ba su yi baya ba, ballantana a ce sun mutu, yanzu baya ga matasa 1200 da aka yi bikin aurarwa Jiddah satin da wuce, to kafin hajin bana ma za kuma bikin aurar da wasu guda 1000 (dubu) kamar yadda Shugaban kwamatin gudanarwa na cibiyar –Mawaddah– wato babban alakali a kotun daukaka kara ta Makka Sheikh Abdullah ibn Abdur Rahman Aluthaim ya bayyana a wurin taron,  sabanin mu da dorewar abu a wurinmu ba karamin jan aiki ba ne.
 4. Kowa ya bayar da irin gudunmawar da zai iya, kuma daidai karfinsa, a irin wadanann cibiyoyin za ka ga kowa da irin gudunmawar da yake bayarwa, ba kuma da wani jin nauyi ba, a lokacin da wani zai bayar da kyautar milyan goma, wani dubu goma zai bayar, wani zai bayar da kyautar ruwa da lemukan da za’a sha a wurin taro, wani kuma tashi zai yi ya raba kyauta ba tare da wani jin nauyi ba, tare da cewa zai iya zama malami ko ma’aikaci,  wani babban mutum mai matsayi a cikin jama’a amma wannan ba zai hana shi irin wannan aikin da wasu a irin wurinmu za su iya daukar sa a matsayin aiki na kaskanci ba.
 5. Malamai da managarta a cikin al’umma  su rika shiga cikin rayuwar mutane, kuma su rika rike amana, su zama masu  iya gudanarwa a duk wani aiki da aka dora musu. Duk da cewa wannan abin nema ne akan kowa, amma dai ba kamar irinsu.

Allah ya sanya musu alheri, ya kara musu taimako, mu ma ya agaza mana wurin kokarin kwatantawa Amin summa Amin.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu

(Laraba 6/07/2011

Nura Abdullahi Madina

MAGANIN BASHI!

Wata rana Annabi (SAW) ya shiga masallaci, sai ya yi
kicibis da wani mutumin Madina ana ce masa “Abu Umama” sai Annabi (SAW) ya ce:
Abu Umama! ya na gan ka a masallaci a zaune, ga shi kuwa yanzu ba lokacin
sallah ba ne?! Sai ya ce” “Bakin ciki, da BASUSSUKA ne suka yi min katutu ya
manzon Allah!
” Sai Annabi (SAW) ya ce: Me zai hana in koya maka wata
magana, da in dai ka fade ta Allah zai ya ye maka bakin cikin da yake damun ka,
kuma ya biya maka bashin da yake kanka!” Sai ya ce: Godiya nake ya
manzon Allah!” Sai  ya ce masa: “Duk
safiya da maraice ka  rika yin wannan
addu’a:

«اللَّهُمَّ إِنِّى أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ
وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْجُبْنِ
وَالْبُخْلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ غَلَبَةِ الدَّيْنِ وَقَهْرِ الرِّجَالِ»

“ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI, WA A’UZU BIKA
MINAL AJZI WAL KASALI, WA’A UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI,  WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA
QAHRIRRIJALI”

Ma’ana” Ya Allah ina neman tsarinKa daga bakin ciki, ina
neman tsarinKa daga gajiyawa da kasala, ina neman tsarinKa daga tsoro, ragwanta
da rowa, ina neman tsarinKa kar BASHI ya kai ni kasa, ko mazaje su ga
bayana”

Wannan sahabi –Abu Umama- ya ce: “Sai na yi yadda  Annabi (SAW) ya ce na yi, sai kuwa Allah ya
yaye min bakin cikin da ke damuna, kuma ya biya min BASUSSUKAN  da suke kaina.

Baya ga addu’a, akwai wasu abubuwa da za su taimaka wurin
tseratar da mutum daga masifar bashi da izinin Allah. Ga wasu daga ciki:

(1)Ya tuba daga akidar cin bashi in dai yana da ita. Da yawan hausawa suna da
akidar cin bashi koda ba lalurar hakan, shi ya sa ake yi wa malam bahaushe
kirari da: “Bahaushe mai ban haushi; NA TANKO MAI KAN BASHI” Irin
wadanda wannan akida ta cin bashi ta yi musu katutu a zuciya ko kusa ko alama
ba sa fargabar cinsa. Amsar da suke yawo da ita kullum a aljihu ko da za su yi
karo da mai yi musu nasiha gameda wannan mummunar akida ita ce: “AI SHI
BASHI HANJI NE YANA CIKIN KOWA!

Talauci: Daga cikin
manyan abubuwan dake janyo shi akwai
jahilci, da rashin sana’a sai a dage wurin neman ilimi komai wahala; don
bayan wuya sai dadi” kuma a nemi sana’ar yi don a dogara da kai. Sana’a
tana daga cikin maganin matsalolin da za’a fada a lamba (3,4).

Akidar “Allah
ya ba ku mu samu
” a tuba a rungumi akidar “Allah ya ba mu, mu ba ku

Tsammanun
wa rabbuka “wai malam ya ki noma don zakka
” ya daure ya gyara gonarsa.

Ba ki da gashin wance, ki ce sai kin yi kitson wance” Ma’ana mutum ya dauki
rayuwar da ta fi karfinsa, ko ya rika dorawa kansa abin da ba shi da hali,
kamar cin bashi saboda ramuwar biki, yin anko, mallakar waya bayan ba halin
rike ta, yin aure ko kari bayan ba halin yin hakan. Wata baiwar Allah ta kawo
kukunta wurin malam Ja’afar Allah ya jikan sa cewa mijinta ya kara aure amma ko
inda zai sa matar babu; don haka da ita uwar gidan gami da ’ya’yanta da amaryar
hade da shi kansa mai gidan duk a daki daya suke kwana!!! Kullum in sun yi masa
korafi sai ya ce zai kokari ya kama wa amaryar
gidan haya! dss.

Tsadar kayayyaki don haka  gwamnati da ’yan kasuwa,
su taimaka wurin rage wannan matsala.

Abu Huraira (R.A) ya rawaito cewa: (a farkon lamari) Idan
aka kawo mamaci don Annabi (SAW) ya yi masa sallah,  sai ya tambaya: “Shin ya bar abin da za’a
biya masa bashi da shi”? Idan aka ce
“ee” sai ya yi masa sallah, idan aka ce “a’a” sai ya ce da ragowar
musulmi ku yi wa sahibinku sallah. Bayan an yi yake-yake  (an samu wadata) sai ya ce: “Ni ne mafi
cancantar Muminai daga kawukansu (daga yau) wanda duk ya mutu ya bar bashi daga
muminai, to (ya komo kaina) ni zan biya, wanda kuma ya bar dukiya ta magadansa
ce” (Bukhari da Muslim) Allah ya karawa Annabi daraja.

Previous Older Entries