MAGANIN BASHI!

Wata rana Annabi (SAW) ya shiga masallaci, sai ya yi
kicibis da wani mutumin Madina ana ce masa “Abu Umama” sai Annabi (SAW) ya ce:
Abu Umama! ya na gan ka a masallaci a zaune, ga shi kuwa yanzu ba lokacin
sallah ba ne?! Sai ya ce” “Bakin ciki, da BASUSSUKA ne suka yi min katutu ya
manzon Allah!
” Sai Annabi (SAW) ya ce: Me zai hana in koya maka wata
magana, da in dai ka fade ta Allah zai ya ye maka bakin cikin da yake damun ka,
kuma ya biya maka bashin da yake kanka!” Sai ya ce: Godiya nake ya
manzon Allah!” Sai  ya ce masa: “Duk
safiya da maraice ka  rika yin wannan
addu’a:

«اللَّهُمَّ إِنِّى أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ
وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْجُبْنِ
وَالْبُخْلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ غَلَبَةِ الدَّيْنِ وَقَهْرِ الرِّجَالِ»

“ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI, WA A’UZU BIKA
MINAL AJZI WAL KASALI, WA’A UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI,  WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA
QAHRIRRIJALI”

Ma’ana” Ya Allah ina neman tsarinKa daga bakin ciki, ina
neman tsarinKa daga gajiyawa da kasala, ina neman tsarinKa daga tsoro, ragwanta
da rowa, ina neman tsarinKa kar BASHI ya kai ni kasa, ko mazaje su ga
bayana”

Wannan sahabi –Abu Umama- ya ce: “Sai na yi yadda  Annabi (SAW) ya ce na yi, sai kuwa Allah ya
yaye min bakin cikin da ke damuna, kuma ya biya min BASUSSUKAN  da suke kaina.

Baya ga addu’a, akwai wasu abubuwa da za su taimaka wurin
tseratar da mutum daga masifar bashi da izinin Allah. Ga wasu daga ciki:

(1)Ya tuba daga akidar cin bashi in dai yana da ita. Da yawan hausawa suna da
akidar cin bashi koda ba lalurar hakan, shi ya sa ake yi wa malam bahaushe
kirari da: “Bahaushe mai ban haushi; NA TANKO MAI KAN BASHI” Irin
wadanda wannan akida ta cin bashi ta yi musu katutu a zuciya ko kusa ko alama
ba sa fargabar cinsa. Amsar da suke yawo da ita kullum a aljihu ko da za su yi
karo da mai yi musu nasiha gameda wannan mummunar akida ita ce: “AI SHI
BASHI HANJI NE YANA CIKIN KOWA!

Talauci: Daga cikin
manyan abubuwan dake janyo shi akwai
jahilci, da rashin sana’a sai a dage wurin neman ilimi komai wahala; don
bayan wuya sai dadi” kuma a nemi sana’ar yi don a dogara da kai. Sana’a
tana daga cikin maganin matsalolin da za’a fada a lamba (3,4).

Akidar “Allah
ya ba ku mu samu
” a tuba a rungumi akidar “Allah ya ba mu, mu ba ku

Tsammanun
wa rabbuka “wai malam ya ki noma don zakka
” ya daure ya gyara gonarsa.

Ba ki da gashin wance, ki ce sai kin yi kitson wance” Ma’ana mutum ya dauki
rayuwar da ta fi karfinsa, ko ya rika dorawa kansa abin da ba shi da hali,
kamar cin bashi saboda ramuwar biki, yin anko, mallakar waya bayan ba halin
rike ta, yin aure ko kari bayan ba halin yin hakan. Wata baiwar Allah ta kawo
kukunta wurin malam Ja’afar Allah ya jikan sa cewa mijinta ya kara aure amma ko
inda zai sa matar babu; don haka da ita uwar gidan gami da ’ya’yanta da amaryar
hade da shi kansa mai gidan duk a daki daya suke kwana!!! Kullum in sun yi masa
korafi sai ya ce zai kokari ya kama wa amaryar
gidan haya! dss.

Tsadar kayayyaki don haka  gwamnati da ’yan kasuwa,
su taimaka wurin rage wannan matsala.

Abu Huraira (R.A) ya rawaito cewa: (a farkon lamari) Idan
aka kawo mamaci don Annabi (SAW) ya yi masa sallah,  sai ya tambaya: “Shin ya bar abin da za’a
biya masa bashi da shi”? Idan aka ce
“ee” sai ya yi masa sallah, idan aka ce “a’a” sai ya ce da ragowar
musulmi ku yi wa sahibinku sallah. Bayan an yi yake-yake  (an samu wadata) sai ya ce: “Ni ne mafi
cancantar Muminai daga kawukansu (daga yau) wanda duk ya mutu ya bar bashi daga
muminai, to (ya komo kaina) ni zan biya, wanda kuma ya bar dukiya ta magadansa
ce” (Bukhari da Muslim) Allah ya karawa Annabi daraja.

3 Comments (+add yours?)

  1. Nasidi
    Feb 16, 2012 @ 08:01:26

    Assalamu alaikum.
    Allah ya saka muku da alkhairi, akwai yan gyare-gyare na font a wannan rubutun

    Reply

  2. Sk Dan Alhaji
    May 04, 2012 @ 10:00:16

    Mungode allah yasaka da alherisa ameen.

    Reply

  3. usman
    Apr 22, 2013 @ 19:26:41

    Allah ya biya da alkhairi

    Reply

Leave a comment