Iyalina

Bikin aurar da matasa (3000) Lokaci Guda
Duk da wadata  da yalwar arzuki da kasar Saudiyya take ninkaya a ciki, sai dai mutum zai sha mamaki idan aka bincina masa kadan daga matsalolin da matasan kasar suke fuskanta gameda aure.

Budurwa ta kai shekara talatin ko arba’in, ko ma fiye ba ta taba aure ba, ya zama ruwan dare gama duniya a kasar, samari da ‘yan matan da suke ganin tsakaninsu da aure sai dai ko a aljannah kuwa Allah ne kadai ya san yawansu.

Abubuwa da dama ne suka hadu suka haifar da wannan matsala, amma dai za’a iya cewa kashin bayan matsalar shi ne T SADAR AURE inda wani dansa zai shiga makarantar faramare amma mahaifinsa bai gama biyan bashin da ya ci a auren mahaifiyar yaron ba!

Sadakin  Riyal dubu hamsin (Naira milyan biyu da doriya) ba wani sadaki ne na gani na fada ba, tun da yakan kai har dubu dari!

Wannan a sadaki kawai kenan, ba’a maganar biki wanda shi ma guda ne babariba, don akalla yakan lankwame kwatankwacin abin da sadakin ya lamushe, kai wani lokacin ma har ninninkawa yake yi!

Sannan ga maganar gidan haya da tarkacen da za’a zuba a ciki, da motar bashi, da tafiya wani gari, ko ma wata kasa don a ci amarci da angwanci da tsinke (Honey Moon)…

Wannan kuma duk  ba’a zo maganar karkon auren ba, don ita ma Magana ce mai zaman kanta.

Duba da yadda wannan matsala take nema ta illata al’ummar baki daya ta bangarori da dama, wasu kungiyoyin taimakon jama’a a kasar –musamman wadanda suke mayar da hankali akan rayuwar iyali- suka tashi haikan wurin murkushe ta, da salo, da dabaru iri iri, daya da ciki shi ne: Hada ma’aurata da dama a biki guda, tare da ba su gudunmawa ta musamman kafin, da lokacin, da kuma bayan auren don saukaka musu al’amura.

Za’a iya kasa irin wannan aure na taimakekeniya zuwa kashi biyu:

Na Farko: Wanda dangi, ko kabila,  ko unguwa daya suke yi tsakanin ‘ya’yansu.

Na Biyu: Wanda cibiyoyin taimakon al’umma  suke yi.

An fara wannan tsari karkashin irin wadannan cibiyoyi na alheri tun sama da shekaru goma da suka shude, kuma abin ya yi tasiri ba dan karami ba, shi ya sa ma kullum yake kara samun karbuwa tsakankanin matasa da iyayen angwaye  da amarye duk da  cewa ya saba da ala’adun larabawa.

A sati dayan nan da ya shude kadai an yi bikin aurar da matasa sama da dubu uku ta wannan hanya.

Ranar Juma’a 10/6/2011 bikin aurar da “Marayu” 100  na farko karkashin gidan Marayu na Insaan a Riyadh.

Ranar Laraba 22/6/2011 bikin aurar da matasa  800 (]ari takwas) a Jizan karo na takwas karkashin cibiyar saukaka aure ta Jizan

Ranar Asabar 25/6/2011 bikin aurar da matasa dari biyu a Sharkiyya  karo na farko karkashin cibiyar Wi’am a Dammam

Ranar Lahadi 26/6/2011 bikin aurar da matasa dari biyu karo na tara a Ahsa’a

Ranar Laraba 29/6/2011 bikin aurar da matasa  1000 (dubu) a Madina karo na uku  karkashin cibiyar Usraty

Ranar Laraba 29/6/2011 bikin aurar da matasa 1200 (dubu da dari byu) karo na goma sha biyu a Jiddah  karkashin cibiyar Mawaddah.

Gudunmawar da ake ba wa wadannan matasa takan saba daga gari zuwa gari, hakanan yawa da karancin angwayen da amaren, amma dai a dunkule tana kunsar abubuwa kamar:

Dauke musu nauyin taron biki wanda na bayyana a baya cewa yana lamushe dubunnan Riyal barkatai

Kyautar kudi,kamadaga Riyal dubu biyar har zuwa dubu talatin

Kyautar set ]in kayan ]aki (gado, kujeru, kwaba… dss)

Kyautar kayayyakin lantari (Tukunyar sanyaya daki Ac- biyu zuwa sama- firinji,  injin wanki, injin shara, rishon gashe-gashe dss).

Set din gwal ga amarya.

Kwasa-kwasai daban dabankansanin makama  da  yadda ake gudanar da rayuwar iyali, hada da shedar halarta.

Kyaututtuka kala kala da sukan hada har da  motar hawa sabuwa fil  da gwala-gwalai dss. (ta  hanya kur’ar mai rabo ka dauka).

Wadannan cibiyoyi sukan sa sharadai na wanda zai cancanta irin wannan tagomashi, ala misali sharadan  cibiyar Usraty ta Madina sun hada da:

Angwon ya zama dan Madina ko daya daga cikin kauyukanta

Shedar auren da ba ta wuce shekara ba, mai satamfin kotu a jiki.

Kada sadakin da zai bayar ya wuce Riyal 35000 (Dubu talatin da biyar. Kwatankwacin Naira milyan daya da rabi).

Ya zama yana da aikin yi, kuma gundarin kudin shigarsa a wata bai wuce Riyal 3000 (dubu uku).

Halartar kwasa-kwasai na musamman  da cibiyar take gabatarwa ga masu shirin aure.

Duk wanda ya cika wadancan sharadai to ya cancanji wannan goma ta arzuki.

Ranar larabar da ta shude (29/6/2011) ne aka yi wannan gagarumin biki a Jiddah da  Madina kamar yadda ya gabata, kuma Allah ya sa na samu damar halartar na Madinan tun daga farko har karshe. Tsarinsa  ya burge ni kwarai, kuma na ga alamar ya  ya kayatar da  mahalarta. Abin sai wanda ya gani.

An yi taron ne a rufaffan dakin taron babban filin wasan kwallo na sarki Muhd. Ibn AbdulAziz dake Madina.

An kawata dakin kwarai da fitilu iri iri masu daukar hankali, kai har da fitulun kwai irin namu na gargajiya guda talatin da daya saboda tuna da!

An karaso da angwayen wurin taron bayan an kewaya garin Madina da su  a cikin manyan motoci (masu cin mutane hamsin) guda goma, ga tarin  babura nan  na samari suna jagorantar motocin, cikin farin ciki da ‘yan wakoki da  bushe bushe da mahaya baburan suke yi wadanda dukkanisu samari ne.

Bayan angwayen sun yi sallar Isha’i, sai suka shigo wurin taro a tsanaki cikin farin ciki, kowanennesu sanye da doguwar riga fara, da hula, da Gutrah (Rawani  ko yafen kai irin na ‘yan Saudiyya) su ma duka farare, da Iqal  (Kwarkwaro n da suke sawa a saman yafen) baki,  sannan ga  tsantsareriyar Mishlah (Alkyabba) ruwan madara kowanne ya zubo ta.

Sarkin Madinamai Martaba AbdulAziz Ibn Majid Ibn Abdul Aziz ya karaso dakin taron karfe 10:8 na dare, ana ta yi masa kirari, da ya zauna sai aka sanya  wani bangare na kiran sallar masallacin manzo, sannan kuma sai taro ya fara.

Mashahurin makarancin nan, malami a jami’ar Musulunci ta Madina, kuma tsohon limamin Masallacin Manzon Allah (SAW) Dr. Muhammad Ayyub shi ya bude taron da karatun Alqur’ani, inda ya rangada tilawar ayoyi shaukun karshe na Suratul Furqan.

Sannan kuma sai wasu kwararrun mawakan gargajiya suka kasa angwayen kashi biyu, sannan suka  jagorance su baki daya suna ta rera wakoki irin nasu na gargajiya, ga guda nan ana ta yi daga dakin taron mata inda amaren suke,  sannan suka taho da su a wani tsari na layi da tafiya  mai ban sha’awa, suka kewaya sarki da shauran mahalarta suka gan su, suka  taya su murna, kuma saka yi musu addu’a  ta alheri.

Bayan sun koma sun zauna sai wata kungiyar masu rawar gargajiya irin ta yan su (masu kamun kifi) suka zo suka cashe, sannan sai aka harba fitilu masu kyalkyali, duk don nuna farin ciki.

Bayan nan kuma sai Babban sakataren cibiyar ta Usrati, wadda ta tsara wannan biki, wato Dr. Abdul Bari Atthubaiti, limami a masallacin manzo, kuma babban alkali a babbar kotun Madina ya yi jawabin sa, inda ya godewa Allah bisa tallafin da ya yi musu na iya  gabatar da wannan hidima ga matasansu, sannan ya yi bayanin mahimmancin irin wannan aiki a musulunci, ya kuma kwadaitarwa kan a rika bayar da gudunmawa don gudanar da shi,  daga bisani kuma ya godewa mahukunta kasar musamman sarkin Madina, babban bako, kuma shugaban kwamatin gudanarwa na cibiyar bisa hadin kai da kaimi, da karfin gwiwa da yake ba su, da kuma duk wanda ya bayar da gudunmawa, ko ta shawara, ko tunani, ko kudi … ko fatan alheri, ko ma halarta wurin taron.

Sannan aka kuma yin wakoki, sai kuma wakilin kamfani Haadiya Abdul Ladif Jamil ya gabatar da jawabi a madadin kamfanoni da cibiyoyi da mutanen  da suka bayar da gudunmawa.

Sai aka kuma yin ‘yan wakoki, aka sa jawabin sarki Abdallah na tagomashin da ya yi wa ‘yan kasar na bayar da kyautar Riyal dubu daya duk wata ga duk mai neman aiki har ya zuwa ya samu, sannan kuma sai aka yi raywarsu ta gargajiya da ake yi da takubba da sanduna.

Daga nan kuma sai aka yi kuri’ar mai rabo ka dauka na abubuwa uku:

Motoci uku sababbi fil kirar Hyundai 2011

Kayan daki (gado, kujeru, kwaba dss)  guda goma

Set din gwal guda biyar

An  rubuta sunan kowane ango a jikin takarda, aka sa a cikin wani gilashi aka juya su baki daya, sannan wata ‘yar karamar yarinya da ba ta wuce shekara shida ba da aka caba wa ado ta zo- a bainar jama’a-  ta dauki takarda daya daga cikin takardun nan dari biyar, ta kai wa mai gabatarwa, shi ma take a nan ya bude ya karanta sunan wanda ya ci mota ta farko, aka kira shi nan take sarki ya danka masa makullin motar,  sannan ta kuma daukowa, aka karanto  wanda ya ci ta biyu, shi ma ya zo ya karbi makullin…. Haka dai har zuwa kyautar karshe.

Daga nan  sai aka bai wa mahaifin amaryar da sakadinta ya fi na kowacce karanci a wadanda aka yi musu bikin, inda ya rangwanta ya karbi Riyal dubu goma kacal! (Kimanin Naira dubu dari hudu da talatin)! An ba shi kyauta ne don ragowar iyaye su yi koyi da shi wurin karbar sadaki kadan kamar yadda ya yi!

Sannan kamfanin waya na STC shi ma ya bai wa kowane daya daga cikinsu kyauta, hakanan ma cibiyar Usrati (amma wadannan kyaututtuka ba a wurin aka raba su ba).

Dama kuma a jawabin Babban sakataren cibiyar liman Thubaiti ya bayyana cewa cibiyar Salih Al-Rajihi  ta dauki nauyin kai gabadayan angwayen da amarensu  haji bana, har da karin wasu ma’auratan dari biyar.

Wannan ita ma ba karamar dankwaleliyar kyauta ba ce, don jumullar kudin da ta ci: Riyal milyan bakwai da rabi (Riyal 5000×1500) (Kimanin Naira 322,500,000).

Idan ka san yadda zuwa haji yake yi wa matasan Saudiyya wahala, za ka san cewa in ba irin wannan damar ba, to wasu da dama daga cikin wadannan matasa ba za su iya sauke farali ba sai nan da shekaru masu tarin yawa in ma sun iya saukewa.

Daga nan kuma sai sarkin Madina ya mika kyaututtukan da cibiyar ta tanada ga wadanda suka bayar da gudunmawa da suka hada da kamfanoni, cibiyoyin agaza wa jama’a, da  kafafan yada labarai,  dss.

Sannan kuma ya je, shi da liman Thubaiti babban sakataren Usrati suka yi hoto su da angwayen don tarihi.

Bayan an ci abincin dare, kowane ango ya je ya dauki amaryarsa ya yi gaba.

Sarkin Madina AbdulAziz ibn Majid, daLimamin Haramin Madina Dr. AbdulBari Athubaiti, da wasu daga cikin angwaye a Madina.

A hirar da na yi da jami’in yada labarai na Usrati, Ustaz Nadim Bakhsh ya bayyana min cewa  jumullar gudunmawar da  ma’auratan suka samu daga cibiyar Riyal milyan shida ne (Kimanin Naira 258,000,000)- ban da kudin kai su hajji- kamar yadda ya bayyana min cewa kudin da aka kashe a wurin taron ya doshi Riyal 500,000 (Kimanin Naira: 21,500,000)

Yanzu abin tambaya a nan shi ne:

Ina wadannan cibiyoyi suke samun kudaden da suke yin irin wannan hidima?

Menene tasirin irin wannan gudunmawa a cikin al’ummarsu?

Me za mu koya daga irin wannan hobbasa a kasashenm?

Game da tambaya ta daya, to suna samun kudinsu ne daga:

Daidaikun mutane kowa dai dai karfinsa. Misali:  motoci biyu daga cikin ukun da aka yi kura’ar mai rabo ka dauka a Madina, set din gwala-gwali biyar, set din kayan daki guda goma, daidaikun mutane ne suka dauki nauyin hakan kamar yadda aka bayyana a wurin taron.

Cibiyoyi da kungiyoyi taimakon jama’a, kamar cibiyar Salih Al-Rajihi, wadda ita kadai ta dauki nauyin bikin aurar da matasa (maza da mata) dari takwas a Jizan, da dari biyu a Ahsa’a. da kai gabadayan na Madina har da karin dari biyar hajji. A wurin bikin aurar da wadancan matasa 800, babban sakataren kwamatin amintattu na wannan cibiya ta alhaeri ya bayyana cewa duk shekara  cibiyarsu tana kashe Riyal milyan goma  shatakwas (kimanin Naira milyan dari bakwai da saba’in da hudu) wurin aurar da samari da ‘yan mata 4000 (dubu hudu) a sassa daban daban na Saudiyya. Ka tuna aurar da matasa daya daga cikin tarin ayyukansu.

Kamfanoni daban daban kamar kamfanin Haadiyah Abdul-Ladif Jamil na wata ‘yar kasuwa a kasar. Wannan baiwar Allah mai suna Haadiyah- ta hanyar wannan kamfani nata-  ita ta bayar da kusan rabin gudunmawar da aka baiwa matasan a Madina a bikin bana, don said a ta bai wa kowane ango da amarya mahimman kayayyakin lantarki da suke bukata a gidansu (Ac uku, firinji daya, injin wanki daya, injin shara daya, rishon gashe gashe daya… dss) don haka a bikin Madina  na bana kadai ta bayar da kyautar: Ac 1500, firinji 500, injin wanki 500, injin shara 500, rishon gashe gashe 500. Bugu da kari, ba a Madina kadai take bayar da irin wannan gudunmawa ba, har da wasu daga sassan kasar, kamar yadda ba bana ta fara ba.

Zakkah (Manyan malaman Saudiyya sun bayar da fatawa cewa za’a iya ba irin wadannan cibiyoyin zakka don gudanar da irin wadannan ayyuka).

Ya kamata wasu  tambayayi biyu su haifu daga wannan tambayar ta farko, wadannan tagwayen tambayoyi su ne: Ya aka yi wadannan masu kudi suke  ciyar da dukiyoyinsu a irin wadannan ayyukan alheri, kuma ya aka yi irin wadannan cibiyoyi suke iya gamsar da kamfanoni da masu kudin  har suke iya yi musu marka-markar kudi haka?

Gameda da abin da ya shafi karfin halinsu wurin ciyar da dukiyoyinsu ta wannan hanya, ni a ganina akwai dalilai da dama da suka sa suke yin haka. Ga wasu daga ciki:

Imaninsu da alkawarin Allah (SWT) cewa wanda ya ciyar ta farkinSa zai ninninka masa, da fadin Manzon Allah (SAW) cewa “Kudi bai taba raguwa ba don an yi sadaka da wani bangare nasa).

Nemankudi da manufa, ma’ana sun san me yasa suke neman kudi, kuma yin irin wadannan ayyuka da kudaden nasu yana daga cikin manufofinsu na nemansu, don haka lokacin da suke ciyar da kudinsu ta wannan hanyar suna jin cewa suna cimma wani mahimmin buri ne a rayuwarsu.

Alamar cewa suna kwatanta cin halak da fitar da hakokkin Allah a dukiyarsu, domin wanda yataradukiyarsa ta hanyar haram bai fiya samun dacewar yin irin wadannan kyawawan ayyukan ba.

Tarbiyantarsu da aka yi akan bayarwa, ba akan karba ba

Tausayi da rahama da jinkan talakawa dake zukatansu. Dss

Gameda yadda irin wadannan cibiyoyin suke iya gamsar da su har su iya damka amanar kudadensu a hannunsu kuwa, ni a ganina wannan yana komawa zuwa abubuwa da dama wasu daga ciki su ne:

Kyakkyawar niyyar wadannan cibiyoyi. Bahaushe yana cewa wai “Farar aniya laya”

Amanarsu. Zai wahala ka ji an ce irin wadannan cibiyoyi sun ci amanar wanda ya ba su kudi su yi aikin alheri da shi, ko su raba a tsakaninsu.

Masu gudanar da su ba da wannan aikin suka dogara ba, don duk manyan ma’aikatan wuri za ka ga suna da harkokinsu daban, kai wasu ma masu kudin gaske ne.

Tsari da iya gudanarwa; domin idan mutum ya bayar da kudi a yi wani abu da shi, ko shi da kansa aka ce ya kashe kudin nan, da wahala ya iya kashe su yadda ya kamata, kuma ta hanyar da ta dace kamar yadda  su za su yi, don haka idan mutum ya ba su kudi ba ya jin cewa za’a barnatar masa, ko banzatar masa da dukiya.

Kiyaye sharuddan da mai kudin zai bayar; idan mutum ya ce ga kudi a gina rijiya, to fa ba yadda za’a yi su  yi wani abu da shi daban- kamar gina masallaci- sai sun nemi izininsa, ko kuma su dawo masa da kudinsa idan ba za su iya cika sharadinsa ba.

Yin komai a bude ba tare da rufa rufa ba; kowace shekara suna buga rahoto na musamman gameda da  abin da suka samu da abin da suka kashe,  da ayyukan da suka yi- hard a hotuna da maganganun wasu daga cikin wadanda suka amfana- da abin da suka sa gaba a shekara mai zuwa, da kudin da zai ci,  su yada kowa ya gani, sannan kuma sukan rubuta rahoto na musamman ga wanda ya ba su kudi mai kauri su yi masa bayani filla-filla na yadda suka kashe kudin, kuma su tambaye shi idan ya amince da yadda suka kashe, ko kuma yana da gyara a kai.

Tallata kamfanonin da suka ba su gudunmawa a jaridu da mujallu, da shafukan yanar gizo, da sanarwarkanhanya ta hanyar sanya sunayensu da tambarinsu da bayanin cewa wadannan kamfanoni ne suka dauki nauyin wannan aiki. Suna yin haka a duk sanarwar da za su fitar mai alaka da shirin da za su yi. (Amma ban ga suna rubuta sunayen daidaikun mutane ba, sai dai kamfanoni, ko cibiyoyin taimakon jama’a).

Girmamawa wa]anda suka bayar da gudumawa da ba su shedar yabo,  a wurin taro.

Gameda da tambaya ta biyu kuwa- Manene tasirin irin wadannan gudunmawa a cikin al’ummarsu?

Gaskiyar lamari irin wannan  gudunmawa da sharye shirye suna  da tasiri  matuka a rayuwarsu, daga cikin irin wannan tasirin akwai:

Yaduwar soyayya da kaunar juna tsakanin jama’a,  don haka za ka ga akwai karancin gaba da hassada da keta tsakanin mawadata da matalauta, saboda mawadaci zai yi wa talaka abin da ko mahaifinsa ba zai iya yi masa ba. Za ka jima kafin ka ji talakan Saudiyya yana zagin mai kudi.

Hadin kai da dunkulewa tsakanin gabadayan al’umma; domin kuwa su dai wadanda ake bai wa wannan gudunmawa masu karamin karfi ne, amma kuma duk inda aka gabatar da irin wannan shiri za ka ga  sarkin yankin shi ne yake jagorantar shirin, sannan kuma malamai da limamai, da alkalai,  da sauran manyan mutane na yankin manyan baki, su kuma masu kudi su ne masu bayar da gudunmawa, ga talakawa nan kuma wadanda suka samu wannan taimako, sannan ga ragowar mutanen gari nan da suke taya su murna, kowane bangare yana yi wa dayan addu’a da fatan alheri.

Rage matsalar rashin aure, tsakanin matasa.  Na fada a baya cewa ta kai akan samu samari da ‘yan matan da suke hakura da aure, kamar yadda za ka ga mata da yawa  sun  wuce shekara talatin, har sun doshi arba’in amma ba wanda ya taba kula su da niyyar aure, amma ta hanyar irin wannan shiri, da kuma wasu shirye shiryen da dama ana samun raguwar wannan bala’i.

Sai tambaya ta karse; Me za mu koya daga irin wannan hobbosa?

Gaskiya abubuwan da muke koya a irin wannan suna da tarin yawa, zan fadakar akan wasu kadan daga ciki wa la’lla su yi mana amfani:

Neman dukiya ta hanyar halal; domin wanda yataradukiya ta hanyar haram da wuya ya samu dacewar yin irin wadannan ayyuka kamar yadda na fada a baya.

Yan abu don Allah, ba don siyasa, ko neman suna, ko neman daukaka da bautatar da talakawa da cutatatar da su don an ba su wani abu daga dokiyar da Allah ya ba wa mutum ajiya ba. Ko kuma taimakawa mutum da nufin kai ma ya taimaka maka a nan gaba.  Ba shedar zukatan irin wadancan bayin Allah nake yi ba, don shinan gaibu sai Allah, amma dai yadda suke al’amuran nasu akwai alamar Allah a ciki, don za ka ga hidima ta milyoyin Riyal amma ba za ka san wanda ya yi ba, kai har shardantawa ma suke yi cewa  kada a fadi sunansu. Ko a  bikin da na halarta ranar Laraba a Madina, take a nan sarki ya bayar da sanarwar cewa wani bawan Allah ya bayar da kyautar karin motoci biyu sababbi ga angwayen- bai fadi sunansa ba-

Ciyar da dukiyoyinmu tafarkin Allah madaukakin sarki, kamar ta hanyar irin wadannan ayyuka, gina masallatai, makarantu, asibitoci,  haka magunanun ruwa, daukar nauyin dalibai da masu bahasi, samar da ayyuka ga matasa dss, maimakon kashe kudi a abubuwan da in ba su cutar ba, to amfanin da suke da shi bai taka kara ya karya ba in har akwai shi, kamar batar da dukiya a fagen wasanni, kade kade da raye raye, tarurruka marasa asali a addini,  ci banza ci wofi, ko gantali kasashen duniya, saya wa matasa kwaya don bautar da su a fagen siyasa, kashewa matan banza dss. Daga cikin abin da ya kamata a yi tsokaci a kansa a nan akwai mugun nufin da wasu suke da shi wurin ciyar da dukiyoyinsu, sai su ba wa mutum kudi da yawa –watakila ma ba zai iya sarrafa su ba- su je wai ya je ya yi aikin alheri, amma a hakikanin gaskiya ba wannan ne a ransu ba, so suke su bata shi, su samu bakin maganar cewa kowa “Kowane gauta ma ja ne, sai in bai sha rana ba” “Malamai” aka fi danawa irin wannan tarkon don mugun nufi!

Rashin dogara da gwamnati a komai. Wani abin da zai ba ka sha’awa a nan shi ne duk irin wannan hidindimu ba gwamnati ce take yi ba, sai dai kawai daidaikun jami’an gwamnati wanda ya yi niyya, kuma yana da hali, shi ma ya bayar da abin da zai iya – kamar a bara sarkin Madina shi ma ya bayar da kyautar motoci biyu- ko a rika dauka a albashinsa duk wata. To idan har a kasa irin Saudiyya kasar da ‘yan kasarta suke samun duk wani abin more rayuwa dai dai gwargwado, kasar da fetur ya fi ruwa arha, amma duk da haka ba sa  dogara kacokan akan gwamnati, ina ga mu da abubuwa da dama na lalurar rayuwa ba su wadata ba, ko ma babu su baki daya, bugu da kari, kullum  ita kanta gwamnatin kuka  take yi cewa ba za ta iya ba; sai an tallafa mata! Don haka danuwa maimakon kullum a zauna a dakali a yi ta takaici, ko a shiga gidan radio a yi ta babatu cewa gwamnati ba ta yi kaza ba, ko taki yin kaza, duba abin kai da sauran abokana za ku iya yi domin ku taimaki kanku da al’ummarku ko da gwamnati ba ta shigo ciki ba. Alhamdu Lillahi akwai wadanda suka fara irin wannan kokarin, kuma kullum ci gaba suke samu.

Kokarin dogaro da kai. Yana daga cikin abubuwan da za su konawa mai hankali rai a ce wai matsalar mahaifiyar mutum ko kanwarsa, ko matarsa, ko dansa ko kanensa, ko makocinsa… dss, amma saboda akidar “Allah ya ba ku mu samu” da ta yi katutu a zakatan da yawa daga cikinmu, wai jira yake wani banasare daga kasar turai, ko balarabe daga kasar larabawa ya zo ya taimaka masa! Bayan zai iya tabuka wani abu! Wannan alama ce ta mutuwar zuciya da rashin kishin kai da kulafuci.  Don haka ya kamata mu rika kokarin warware matsalolinmu da kanmu ba sai mun jira wasu ba, kuma na tabbata za mu iya da izinin Allah.

Kafa cibiyoyin taimakon jama’a masu zaman kansu da bayar da taimako ta hanyarsu. A cikin al’ummarmu akwai wasu da Allah ya datar da su, suke iya  ciyar da dukiyarsu ta hanyar alheri, kamar ciyarwa, kudin magani,  kudin makaranta, taimakawa malamai,  kai mutane hajji da umara, dss sai dai abin la’akari a nan shi ne, da zarar Allah ya karbi ransu, ko wadatarsu ta yi kasa, sai wannan aikin alherin ya yi rauni, ko ma ya tsaya. Wani bawan Allah a daya daga cikin jahohin arewacin Nijeriya ya sanya daruruwan marayu makaranta mai tsada, kuma ya dauki nauyin biya musu kudin makaranta, duk shekara yana kashe milyoyin kudi a wannan aikin alheri, amma yana rasuwa mafi yawancin yaran karatun ya gagare su, har makarantar kasan kasa suka kasa zuwa! Irin wannan da cibiya ya kafa mai kula da wannan ya samar mata da hanyar samun kudi, da da wahala wannan aikin alheri ya mutu da mutuwarsa,  Don haka ina kira ga masu halin da Allah azurta su da zuciya ta yin irin wannan taimako da su rika bude cibiyoyi, su sa masu amana, kuma kwararru wurin gudanarwa don gudanar da ita, kuma su sama musu hanyoyin samun kudi masu dorewa. Wasu cibiyoyin a Saudiyya manyan otel suke ginawa a kusa da harami, wasu kuma noma, wasu kuma su sayi hannun jari, wasu kuma sayen kadarori, wasu su ribar rubuce rubucensu dss. Na je wata makaranta a Afrika ta kudu a shekarun baya, sai naga wanda ya gina ta, ya gina wani babban gidan mai a jikanta, ya kuma mallaka mata shi, don ya zama daya daga cikin hanyoyinta na samun kudin shiga. Wannan hanya ta burge ni sosai!

Bayar da kulawa ta musamman ga raunana a cikin al’umma. Na farko dai wadanda ake bai wa wannan taimako masu karamin karfi ne, sannan kuma a ba’a manta da nakasassu ba,  don bara waccan kungiyar kula da nakasassu ta Riyadh babban birinin Saudiyya mai suna (Harakiyya) matasa (maza da mata) dari da biyu ta aurar, bara

Wasu daga cikin  angwaye  “Nakasassu”

kuma saba’in da biyar, inda kowane ango da amarya suka samu gudunmawar Riyal dubu hamsin, bayan bikin da aka yi musu. Abin bai tsaya a nan ba, don kamar yadda ya gabata  sati ukun da suka wuce cibiyar AbdulAziz ibn Fahd marayu –wadanda suka tashi a gidan marayu- dari ta aurar, kuma shirinta na wannan shekara  shi ne ta aurar da  irin wadannan  marayun dubu a bangarori da dama na kasar.

Daukar mataki a aikace don magance matsala, maimakon takaitawa akan korafi da takaici, ko mutum ya tafi da rayuwarsa a “adawa”!

Fada da cikawa,  sau tari za ka ga wasu daga cikin mutane a kasashe irin namu sun bayar da gudunmawar kudi a wurin taro, amma karshenta kafin su fito sai an yi jan ido, wani lokacin ma sai dai a bar shi da Allah! Ko kuma mutum ya ce ya bayar da gudunmawar milyan daya misali, nan kuwa a zuciyarsa dubu goma ya yi niyya, ragowar ya fada ne don alfahari da burga, don haka bayan ya bayar da goman- in ya bayar kenan- ragowar sai dai a yi masa Allah ya isa!  Amma su a irin wadannan tarurrukan na su, sau tari  kafin ma a bayar da  sanarwar cewa wane, ko cibiya kaza ta bayar da gudunmawaR kaza, gudunmawar tuni  ta zo hannu. Alal misali kyaututtukan mai rabo ka dauka;  gwalagwalai, da sababbin motoci uku a Madina, da wasu sababbin guda bakwai aJidda.. dss, gurin taron ma aka zo da su, take a nan, a gaban jama’a za’a bude takarda, a karanto sunan mutum, a mika masa mukulli, ga motar nan a waje in ya so ya shiga abarsa ya yi gaba a lokacin.

Dorewa akan aikin alheri, za ka ga duk irin wadannan ayyuka in aka fara  su, to an fara kenan kullum sai dai su yi gaba, ba su yi baya ba, ballantana a ce sun mutu, yanzu baya ga matasa 1200 da aka yi bikin aurarwa Jiddah satin da wuce, to kafin hajin bana ma za kuma bikin aurar da wasu guda 1000 (dubu) kamar yadda Shugaban kwamatin gudanarwa na cibiyar –Mawaddah- wato babban alakali a kotun daukaka kara ta Makka Sheikh Abdullah ibn Abdur Rahman Aluthaim ya bayyana a wurin taron,  sabanin mu da dorewar abu a wurinmu ba karamin jan aiki ba ne.

Kowa ya bayar da irin gudunmawar da zai iya, kuma daidai karfinsa, a irin wadanann cibiyoyin za ka ga kowa da irin gudunmawar da yake bayarwa, ba kuma da wani jin nauyi ba, a lokacin da wani zai bayar da kyautar milyan goma, wani dubu goma zai bayar, wani zai bayar da kyautar ruwa da lemukan da za’a sha a wurin taro, wani kuma tashi zai yi ya raba kyauta ba tare da wani jin nauyi ba, tare da cewa zai iya zama malami ko ma’aikaci,  wani babban mutum mai matsayi a cikin jama’a amma wannan ba zai hana shi irin wannan aikin da wasu a irin wurinmu za su iya daukar sa a matsayin aiki na kaskanci ba.

Malamai da managarta a cikin al’umma  su rika shiga cikin rayuwar mutane, kuma su rika rike amana, su zama masu  iya gudanarwa a duk wani aiki da aka dora musu. Duk da cewa wannan abin nema ne akan kowa, amma dai ba kamar irinsu.

Allah ya sanya musu alheri, ya kara musu taimako, mu ma ya agaza mana wurin kokarin kwatantawa Amin summa Amin.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu

(Laraba 6/07/2011

Nura Abdullahi Madina

MAGANIN BASHI!
Wata rana Annabi (SAW) ya shiga masallaci, sai ya yi

kicibis da wani mutumin Madina ana ce masa “Abu Umama” sai Annabi (SAW) ya ce:

Abu Umama! ya na gan ka a masallaci a zaune, ga shi kuwa yanzu ba lokacin

sallah ba ne?! Sai ya ce” “Bakin ciki, da BASUSSUKA ne suka yi min katutu ya

manzon Allah!” Sai Annabi (SAW) ya ce: Me zai hana in koya maka wata

magana, da in dai ka fade ta Allah zai ya ye maka bakin cikin da yake damun ka,

kuma ya biya maka bashin da yake kanka!” Sai ya ce: Godiya nake ya

manzon Allah!” Sai  ya ce masa: “Duk

safiya da maraice ka  rika yin wannan

addu’a:

«اللَّهُمَّ إِنِّى أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ

وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْجُبْنِ

وَالْبُخْلِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ غَلَبَةِ الدَّيْنِ وَقَهْرِ الرِّجَالِ»

“ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI, WA A’UZU BIKA

MINAL AJZI WAL KASALI, WA’A UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI,  WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA

QAHRIRRIJALI”

Ma’ana” Ya Allah ina neman tsarinKa daga bakin ciki, ina

neman tsarinKa daga gajiyawa da kasala, ina neman tsarinKa daga tsoro, ragwanta

da rowa, ina neman tsarinKa kar BASHI ya kai ni kasa, ko mazaje su ga

bayana”

Wannan sahabi –Abu Umama- ya ce: “Sai na yi yadda  Annabi (SAW) ya ce na yi, sai kuwa Allah ya

yaye min bakin cikin da ke damuna, kuma ya biya min BASUSSUKAN  da suke kaina.

Baya ga addu’a, akwai wasu abubuwa da za su taimaka wurin

tseratar da mutum daga masifar bashi da izinin Allah. Ga wasu daga ciki:

(1)Ya tuba daga akidar cin bashi in dai yana da ita. Da yawan hausawa suna da

akidar cin bashi koda ba lalurar hakan, shi ya sa ake yi wa malam bahaushe

kirari da: “Bahaushe mai ban haushi; NA TANKO MAI KAN BASHI” Irin

wadanda wannan akida ta cin bashi ta yi musu katutu a zuciya ko kusa ko alama

ba sa fargabar cinsa. Amsar da suke yawo da ita kullum a aljihu ko da za su yi

karo da mai yi musu nasiha gameda wannan mummunar akida ita ce: “AI SHI

BASHI HANJI NE YANA CIKIN KOWA!”

Talauci: Daga cikin

manyan abubuwan dake janyo shi akwai

jahilci, da rashin sana’a sai a dage wurin neman ilimi komai wahala; don

“bayan wuya sai dadi” kuma a nemi sana’ar yi don a dogara da kai. Sana’a

tana daga cikin maganin matsalolin da za’a fada a lamba (3,4).

Akidar “Allah

ya ba ku mu samu” a tuba a rungumi akidar “Allah ya ba mu, mu ba ku”

“Tsammanun

wa rabbuka “wai malam ya ki noma don zakka” ya daure ya gyara gonarsa.

“Ba ki da gashin wance, ki ce sai kin yi kitson wance” Ma’ana mutum ya dauki

rayuwar da ta fi karfinsa, ko ya rika dorawa kansa abin da ba shi da hali,

kamar cin bashi saboda ramuwar biki, yin anko, mallakar waya bayan ba halin

rike ta, yin aure ko kari bayan ba halin yin hakan. Wata baiwar Allah ta kawo

kukunta wurin malam Ja’afar Allah ya jikan sa cewa mijinta ya kara aure amma ko

inda zai sa matar babu; don haka da ita uwar gidan gami da ’ya’yanta da amaryar

hade da shi kansa mai gidan duk a daki daya suke kwana!!! Kullum in sun yi masa

korafi sai ya ce zai kokari ya kama wa amaryar

gidan haya! dss.

Tsadar kayayyaki don haka  gwamnati da ’yan kasuwa,

su taimaka wurin rage wannan matsala.

Abu Huraira (R.A) ya rawaito cewa: (a farkon lamari) Idan

aka kawo mamaci don Annabi (SAW) ya yi masa sallah,  sai ya tambaya: “Shin ya bar abin da za’a

biya masa bashi da shi”? Idan aka ce

“ee” sai ya yi masa sallah, idan aka ce “a’a” sai ya ce da ragowar

musulmi ku yi wa sahibinku sallah. Bayan an yi yake-yake  (an samu wadata) sai ya ce: “Ni ne mafi

cancantar Muminai daga kawukansu (daga yau) wanda duk ya mutu ya bar bashi daga

muminai, to (ya komo kaina) ni zan biya, wanda kuma ya bar dukiya ta magadansa

ce” (Bukhari da Muslim) Allah ya karawa Annabi daraja.

NASIHA
“Iyaye su shayar da ‘ya’yansu  shekaru biyu cif-cif ga wadanda suka nufi

cika lokacin shayarwa” (Bakara : 233).

Annabi (SAW)

ya ce: “Ku umarci ‘ya’yanku da su yi sallah suna ‘yan shekara bakwai, in suka

kai goma ba su yi ba, ku doke su a kanta, kuma ku raba musu makwanci” (Abu

Dawud).

Annabi (SAW)

ya ce: “In mutum yana so ya zama tantagaryar makaryaci, to duk abin da ya ji ya

karas (Muslim).

Bincike ya nuna cewa iya yawan  haddace-haddacen da mutum yake yi,  iya kara fadin da kwakwalwarsa take yi da

kara rike abubuwa.

YA MUTU YA DAWO!!!
Ya ce na dawo daga kwas din aikin soja kenan ina mai cike da farin ciki,  ina ta tunanin yadda zan je na samu yara da sauran mutanen gida da masoya.

Bayan na isa gida da ’yan sa’o’i, kowa yana ta murna,  manya da yara.

Kwatsam sai na ji ana dukan kofa da karfin gaske,  da na fita sai na ga jami’an tsaro, suka kira ni da cikakken sunana, kuma suka ce ni suka zo nema, don haka shige mu je!

Suka tasa keyyata zuwa ofishin ’yan sanda. Har zuwa wannan lokaci ban wani damu ba; don na san ban yi wani laifi ba.

Amma ba zato ba tsammani sai na ji wai ana tuhuma ta da wani mugun laifi, wanda wannan ya sa ba ki daya na rude, na firgice, na dimauce, har na kasa magana.

Ana tuhumar ka da kisan ganganci! Mataimaki D.P.O ya ce min! kai ne ka kashe wane dan wane,  kuma  kana da sammaci a kotu!

Sai na rasa abin da yake min dadi a duniyan nan, hankalina ya dugunzuma, na kasa gasgata abin da nake ji, na yi ta hakilon gamsar da kaina kan cewa wani ake tuhuma ba ni ba, sunan ne dai ya yi kama, ko wani kuskuren fahimta.

Amma daga karshe na fuskanci abin babba ne, bayan an   ta bincika ta ba ji ba gani. Abin ya kara dagulewa bayan masu binciken sun sanar da ni cewa inkarina ba shi da wani amfani; don ga shedu nan duk sun rantse suna masu tabbatarwa cewa kai ne makashin wannan mutum! Ya ce haka na yi ta fafutukar kare kaina, har karfina ya kare, musamman lokacin da na ga an mika ala’amarina zuwa gurin alkali.

Nan wasu mutane suka bayyana gareni suka ba da sheda cewa lallai ni ne na yi kisan nan, kuma Wallahi Billahillazi La Ilaha Illa huhu ban taba ganin shedun nan ba, kuma ban taba sanin mutumin  da suka ce na kashe ba!

Haka na zauna tsahon shekaru goma sha biyar a kurkuku! Saboda ’ya’yan mutumin nan kanana ne, bayan sun balaga suka ki yin afuwa, suka ce su kawai kisasi suke nema! Bayan bakin ciki da damuwa, da zaman dar dar da na yi tsahon shekarun nan sha biyar a ciki, rannan da sanyin safiyar ranar Juma’a sai ga jami’an tsaro sun shigo inda nake daure, suka miko min takarda don na rubuta wasiyyata, kuma suka sanar da ni cewa yau ita ce ranata ta karshe a duniya! Suka lakkana min Kalmar shahada.

Bayan na gama rubuta wasiyya da dan lokaci, sai suka sani a gaba zuwa filin sare kai, muka samu filin makare da jama’a, ga jami’an tsaro nan iya ganinka sun yi masa kawanya. Har zuwa wannan lokacin ambaton Allah ba ya yankewa daga bakina.

Aka karasa da ni gurin fille kai bayan an rufe min idanuwana, mai shela ya fara shelanta laifin da aka ce na yi, da madogarar da aka dogara da ita wurin yanke min hukuncin kisa. A daidai wannan lokaci sai na dada tunawa da Allah, kuma na kara dagewa wurin ambatonsa, da addu’a, na ce: “Ya ubangiji zalunta ta aka yi!  Ya ubangiji ni zalunta ta aka yi!! Kuma ka yi alkawari, kuma alkawarinka gaskiya ne, kuma kana amsa addu’ar wanda aka zalunta, ya ubangiji ni zalunta ta aka yi, kuma kai ne masanin dukkanin abubuwan da suke boye, na mika lamarina gareka, ba bu abin bautawa da gaskiya sai kai!!!… WALLAHI ban kammala addu’ata a lokacin da ake karanto wancan bayani ba, sai kawai na ji ana hayaniya ana ihu da karfi, na kuma jiyo sautin wani mutum yana cewa da karfi: “Kada ku kashe shi! Ni ne na yi kisan!! kada ku kashe shi!  Ni ne na yi kisan!!  Sai guri ya rude aka ta hayaniya, karanta bayani ya tsaya cik, sai na ji daya daga cikin jami’an tsaron yana cewa: Ga shedun nan sun yi ikrari cewa su ne suka yi kisan,  na ji wasu kuma suna neman a gaggauta zartar da hukunci, haka aka dauki lokaci mai tsaho ana ta cece ku ce, ni kuma ina durkushe, ido a rufe, hannu da kafa a daure! A karshe dai Allah ya fallasa su. Hukuncin kisasi ya fadi daga kaina. Na dawo duniya kai ka ce ranar aka haife ni….

Ina masu bukatu, ina masu fama da bakin ciki da damuwa, ina masu neman waraka… dss. Kun ga yadda addu’a take tasiri? Don haka kar ku sake. Wannan abu ya faru a Saudiyya kamar yadda Badr Almishary ya fada a kaset dinsa  قرع لأبواب السماء.  Shi kuma ya dakko daga littafin الفرج بعد الشدة

NAMadina

IBADA DA HUKUNCHI
Iyaye su shayar da ‘ya’yansu  shekaru biyu cif-cif ga wadanda suka nufi cika lokacin shayarwa” (Bakara : 233).

Annabi (SAW) ya ce: “Ku umarci ‘ya’yanku da su yi sallah suna ‘yan shekara bakwai, in suka kai goma ba su yi ba, ku doke su a kanta, kuma ku raba musu makwanci” (Abu Dawud).

Annabi (SAW) ya ce: “In mutum yana so ya zama tantagaryar makaryaci, to duk abin da ya ji ya karas (Muslim).

Hadarin Sihiri da Hukuncinsa
Tambaya: “Malam menene hukuncin  mai yi wa kishiyarta asiri tana bunnewa, kuma ta shiga tsakanin ‘ya’yanta da mahaifinsu, duk ta hanyar asiri”?  Lubabatu Aliyu

Amsa: Yi wa wani asiri ta hanyar raba shi da wani da yake kauna da juyar da shi daga halin kauna da soyayya zuwa halin gaba da kiyayya, mummunan aiki ne, kuma nau’i ne na sihiri da ake kira ‘Sihrut Tafrik’, ko ‘As-Sarf’, wato sihirin rabawa tsakanin ma’aura, ko masoya, ko juya hankalin wani da susuta shi da zautar masa da hankalinsa daga wani abu da zai amfane  shi zuwa mai cutar da shi, ko kuma daga kaunar abin kaunarsa ko iyayensa zuwa kyamars u da bijire musu.  Akwai hanyoyi da dama da masu irin wannan mugun aiki su kan bi wurin cimma burinsu. Hukuncinsa a musulunci ya zo kurukuru a cikin al-Qur’ani mai girma inda Allah Madaukaki ya ambaci cewa kafirci ne, kuma malamai sun bayyana cewa duk wanda aka kama shi da irin wannan aiki to hukuncinsa shi ne alkali ya sa a kashe shi kisan kafirci da ridda ta barin addinin musulunci. Don haka ya wajaba wannan mata da duk wani mai mummunan aiki irin nata mai irin wannan bamagujiyar mugunta da bakar aniya, ya ji tsoron Allah ya tuba.

Lalata kishiya ta hanyar sihiri da raba ta da mijinta da shiga tsakaninta da ‘ya’yanta ba shi ne zai jawowa mai neman a yi mata sihirin alherin duniyar da take fada da kishiyar a kansa ya dawo gare ta ba.  Arzikin duniya da na lahira duk a gun Allah yake, kuma babu wata hanya da za’a same shi sai da yardarsa.  Yaya za a yi kuwa a ce mutum mumini ya jefa dan uwansa cikin damuwa, ya hana masa kwanciyar hankali; saboda kawai yana ganin cewa shi ne ya hana shi samun wani abin duniya ko kadaituwa da kaunar miji da soyayyarsa, kuma musamman ma a ce ta hanyar kafircewa da Allah da bautawa aljanu.  Gaskiya wannan ba karamar tabewa ba ce, da kekasar zuciya, da rashin tsoron Allah, da fito-na-fito da kaddararsa, da rashin yarda da lamarinsa da dogaro da shi.

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam fa ya gaya mana cewa duk wanda ya je wurin boka ko dan duba, kuma ya tambaye shi kan wani abu har ya gaskata shi, to ya kafirta da abin da aka saukarwa  (Annabi) Muhammad sallalllahu alaihi wa sallam.

A wata riwayar kuma ba za’a karbi sallarsa ta kwana arba’in ba. Wannan wanda ya gaskata kenan, ba tare da ya aikata sihirin ba.  Kuma mafi rinjayen maganar malamai ita ce wannan tambayar da gaskatawar kafirci ne amma karami, ba mai fidda mutum daga musulunci ba.  Amma mai aikata sihirin da mai ba da kudi da umurni a yi wa wani, kuma wanda ake ba wa umurnin ya cika sharuddan da aljanun ke nema a yi musu, to duk wannan aikinsu daya ne da shi bokan, kafircinsu na fita daga addini ne.

Babban abin da ke cikin wannan ma shi ne bautawa shaidanu da aljanu da yi musu da’a cikin abin da suke so, na yanke-yanke ko neman cika wasu sharudda masu dan karen wahala, da bada umurnin a je wani wuri a yi tono a binne.  Wannan duk bautawa aljanu ne, bayan dumbin dukiyar da mutum zai halakar ta wannan mummunar hanya.  Allah ya tsaremu.

Nasihata ga duk wanda Allah ya jarraba da wannan mummunar ta’ada ita ce ya gaggauta tuba zuwa ga Allah,  kuma ya yi watsi da wannan shirka, kuma ya dogara da Allah bisa duk abin da yake nema, sannan ya ji tsoron cewa shi ramin mugunta in an tona shi ba a fa san wanda zai fara fadawa ba.

Daga cikin manyan hadurran da wannan mummunan aiki ya kunsa akwai:

1. Shirka da Allah da bauta wa aljanu.  Kila wata ta ce ai ita wurin ‘malami’ kawai ta je ba gun aljan ba, to ya kamata ki gane cewa shi wannan da kike kira malami ba ya iya komai da kashin kansa sai ya yi da’a ga aljanu su kuma su ba shi umurni ya cika musu. Wannan da’ar da kuma cika sharuddan yadda aljanin ya nema shi ne bakar shirka, domin bautawa wanin Allah ne da neman yardarsa, wato sanya masa kishiya ta hanyar mika wani hakkin ibada zuwa ga waninSa, kamar yanka dabba domin waninSa ko da da sunan Allah ne, ko kuma cika wasu sharuddan da ba Allah ne Ya ce a cika su ba, musamman kuma wurin bautawa wanda za a yi wannan abu dominsa.  Allah kuwa ya yi kashedi ga dukkan al’umma cewa “Duk wanda ya yi tarayya da Allah to lallai Allah ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka”.

2. Nisantar Allah.  Duk wanda Allah ya jarraba da wannan kazamar ta’ada ya fi kowa nisa da ubangiji Mahalicci.  Za ka same shi ba ya karatun Al-Kur’ani, ba ya zikirin Allah Ta’ala.   Babu abin da yake ba shi sha’awa sai aikin da zai sa shadanin aljaninsa ya yarda da shi.

3. Rashin dogaro ga Allah.  Mai sihiri ko kuma mai neman a yi masa sihirin bai yarda da cewa Allah ne abin dogaronsa ba, kuma shi ne mai taimakonsa ba, kuma shi kadai ne mai iya fitar da shi daga kowace matsala, ya kuma dauke masa kowa ce irin damuwa a zuciyarsa ko jikinsa ko abokin zamansa ko zuriyyarsa.  Allah Madaukaki yana cewa:  “Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa”.

Haba baiwar Allah, ga mahaliccinki, mai kowa mai komai, wanda ba bu abin da zai faru cikin halittarsa sai da saninsa da izininsa, wanda shi ne Mabuwayi, babu wanda ya gagare shi, babu mai iya ja da shi, ga shi da kansa yana ba ki alwashi cewa in kin dogara da shi to ya isar maki, wato ya isar maki daga wata cuta da  ta shafe ki daga wani dan Adam ko aljan sai da izininsa, ya isar maki daga abokin gabarki, ya isar maki daga zaluncin azzalumi cikin sammai ko kassai, cikin duhun dare ko ido-na-ganin-ido, ya isar maki daga mai nufin jefa miki badin ciki a zuriyyarki ko a dukiyarki ta hanyar raba ki da abin kaunarki, miji ko da ko dan uwa ko makamantansu, ya isar maki daga dukkan sharri daga dukkan mai nufin sharri.  Don Allah ki daure ki dogara da shi, za ko ki ga cika alkawari. “Wa ya fi Allah cika alkawari?” (Suratut Taubah: 111).

4. Cutar da dan uwa ko ‘yar uwa musulmi.  Wannan kuma babban abu ne da ya shafi hakkin shi wanda aka cutar din, domin har abada Allah zai bi ki da alhakinsa har sai in ya yafe miki, bayan babban laifin shirkar da aka yi.  Abu ne sananne cewa ba ya halatta mutum ya cutar da dan uwansa musulmi.  Amma sihiri hanya ce mummuna ta rusa wannan babban umarni na shari’ah. Za ka ga mutum yana zaune tare da abokin zamansa, miji ko mata, ko da, ko uwa, ko uba, ko kaka, ko jika, ko koshin lafiyar da Allah ya hore masa, ko dukiyar rufin asiri da Allah ya ba shi, ko aikinsa da ya ke samun abincinsa ta hanyarsa, ko kasuwancinsa na halaliyarsa, ko mulkin da Allah ya ba shi amanarsa, amma haka kawai sai wani ya bullo cike da hassada da bakin ciki da mugunta, ya hada kai da boka mai sihiri tare da ba shi wani abin duniya don su taru su bautawa wani mugun aljani domin raba wannan bawan Allah da abin da yake so din nan.  Duk wanda ya yarda da Allah da Ranar karshe to ya tabbatar da cewa zai hadu da Allah Madaukaki, kuma zai yi masa ukuba mai tsanani akan cutar dan uwansa musulmi ta hanyar sihiri,  kuma ya sani cewa in ya tuba ma anan duniya tsakaninsa da Allah to Allah mai gafara ne kuma zai gafarta masa hakkin da yake tsakaninsa da shi na shirkar da ya yi, da tsafin da ya yi, amma in ya bari har ya mutu a kan haka, to shi da aljanna fa faufau, kuma ba zai fita daga Jahannama ba.  Sannan kuma hakkin dan uwansa musulmi na cutar da shi da raba shi da abin kaunarsa, to Allah ba zai gafarta masa ba sai ya nefi yafewarsa daga wanda ya cuta din.

5. daurewa wannan karyar gindi ta hanyar karawa wadannan miyagun bokaye wadanda jahilai suke kira ‘malamai’, da samar musu sanadin rayuwa. Wannan kuwa abu ne da yake kara karfin wannan shirkar a cikin al’umma.  Da a ce daukacin mutane za su yi watsi da bokaye, su kuma daina zuwa wurinsu, da ba su kudi ko wani abin duniya a kan wannan mugunta da suke yiwa mutane, to hakika da an dode wannan babbar kofar sharri, sai fa idan za su ci gaba da bautawa aljanun nasu, su kuma aljanun su sato musu dukiyar mutane.

6. Yada gaba tsakanin al’umma.  Lallai sihiri babbar hanya ce ta hada mutane gaba da kiyayya. Domin duk wanda ya san kina ko kana  da hanu  wurin lalata masu dan uwa ko abin kaunarsa to gaba ta kullu kenan tsakaninku.

7. Yada firgici da tsoro tsakanin mutane, ta yadda zai zama in sihiri ya yadu tsakanin al’umma, to komai kankantar abin da ya faru ga mutum ko wani nasa sai ya fara zaton cewa sihiri wani ya yi masa, tun bai yi bincike ko ya je wurin likita ya rasa magani ba.

8. Taho-mu-gama  da fushin Allah Madaukaki, domin duk al’ummar da ta fada cikin wannan mummunan hali, kuma malamanta suka yi shiru ba su fadakar da mutane kan hadarinsa ba, to fushin Allah zai fada mata kuma ta rasa albarka, ta rasa zaman lafiya.

Sabubban Yawaituwar Sihiri Da Fantsamarsa Cikin Al’umma

*Raunin imani; Allah Madaukaki na cewa : “Duk wanda ya yarda da Allah to Allah zai shiryar da zuciyarsa”. Daga an ce imani da Allah ya raunana, kuma kaunar taimakonsa da sa ran kariyarsa ta yi sakosako a zuciya, kuma tsoronsa ya yi karanci, dogaro da shi ya raurawa, to za ka ga mutane suna dunguma zuwa turakun bokaye da masu sihiri, su kuma su kara musu nisa daga Allah.

*Jahilcin mutane da hukuncin shari’ar Allah Madaukaki da hanin da ta yi kan sihiri, da kuma  jahilcinsu da musulunci kansa da sakon Annabawa da Manzannin Allah Madaukaki ya sa suna kiran matsafa da bokaye da masu sihiri da sunan malamai.  Shi kuma aikin sihiri ana kiran sa da sunan aiki ko kuma addu’a ko kuma ‘istihara’, da kuma jahiltarsu da hakikanin wadannan matsafa.

*Ruduwar mutane a zamanin yanzu da rayuwar duniya da tara abin duniya.  Duk fadi-tashinsu shi ne: ina zaka? Kudi, ina ka fito? Kudi, kuma mafi yawansu, suna neman kudin ne fiye da bukatunsu na yau da kullum. Ayyukan alheri sun yi karanci, riko da addini ya yi sako-sako, sabon Allah shi ne abin yin takara.  Fasikai su ne masu shahara, malamai su ne abin wulakantawa.  Sai ya zama kullum mutane cikin matsaloli, da damuwa, da rashin natsuwa da kwanciyar hankali, da yawan munin zato ga mutane, ciwukan zuciya sun yi cunkus a kirazan mutane, kuma suna zaton cewa wadannan matsalolin da damuwar da cutukan ba su da magani sai an je wurin ‘malami’ ya yi wa mutum ‘aiki’, wato ya yi masu asiri, ko dai ya cuci wani, ko kuma a yi masa tsafi da wani bangare na jikin wani dan Adam don ya yi kudi. Wannan yawan sabon Allah da ruduwa da duniya ya jawo cewa mafi yawan gidajen musulmi makwanci ne na shaidanu, wato aljanu, sabo da yawan tara kayan sabon Allah, hotunan batsa da kallon su, kayan wake-wake, fina-finan batsa da watsa al’umma, tsere wurin koyi da kafirai a kowane fage.  Kuma mutane suka yi nesa da karanta Al-kur’ani, ko zikirori da suka zo daga Annabin rahama, ko addu’o'in kawar da aljanu da tasirinsu. *Raunin malamai wajen aikinsu na magadan Annabawa wajen fadakar da jama’a da tsoratar da su azabar Allah musamman a kan shirka da tsafi da sihiri, har ta kai wasu ba su ma san cewa wannan abu kafirci ba ne, wasu kuma suna ganin ai in babu sihiri ma wani abin duniyar nasu ba zai samu ba, kamar masu mulki da masu kudi.

Wasu daga hanyoyin Fita Da Kuma Kariya Daga Wannan Musifa

Daga ciki akwai:  Jaddada imani a zukatan muminai, da komawa zuwa ga Allah da dogaro  da shi, da tabbatar da tauhidi da kadaita Allah cikin bauta, da nesantar duk abin da ke da alaka da shirka.  Kada kuma musulmi ya manta da fadin Allah cewa: “Kuma ba su cutar kowa da shi (sihirin) sai da izinin Allah”. Allah ya kare mu Amin summa Amin. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Dr. Abubakar Muhd. Sani B\Kudu

RAYUWA MAI ALBARKA
Yana daga cikin abin da duk wani dan adam yake nema a rayuwarsa ta duniya, samun albarka, domin da haka ne zai samu rayuwa ingattacciya , mai cike da dimbin nasara da ci gaba, kuma hanya ce da za ta jawo wa ragowar iyalansa da ma dukkan zurriyarsa samun albarka.

Duba da mahimmancin wannan al’amari naga dacewar in dan yi mana tsokaci game da abubuwan da suke jawo albarka a rayuwarmu ta yau da kullum, dafatan Allah ya amfanar da mu, ya kuma datar da mu izuwa abin da yake shi ne dai dai.

(1)Fara komai da ambaton sunan Allah :

Yana daga cikin abubuwan da suke jawo albarka a rayuwar mutum fara komai da ambaton sunan allah, Manzon Allah (S.A.W) Idan mutum ya shiga gidan sa, yana mai ambaton Allah yayin shiga, da kuma lokacin cin abinci, shaidan zai cewa abokansa : ba ku da gurin kwana da kuma gurin cin abinci a yau”.

Don haka ka ambaci sunan Allah, domin ambaton Allah shine abinda ya kamata musulmi yayi kafin kowane aiki, haka ma har a wajan tarawa da iyali, ( jimai ) anso ka ambaci Allah kana mai cewa : ” Allahumma jannibnas-shaidana, wa jannibus-shaidana ma razaktana”, to idan Allah ya azurta su da da a wannan daren, to hakika zai albarkace shi, domin duk alamarin da mabudinsa ambaton Allah ne, to kuwa albarka ba ta kaurace masa

(2) Jin tsoron Allah da kuma imani da shi :

Allah madaukakin sarki yana fada a cikin Alkur’ani mai girma: (( Lalle da mutanen alkaryu sun yi imani, kuma sun yi takawa, lallai da mun bude albarkatu akansu daga sama da kasa)) (Al-aaraf: 96). Kuma hakan zai kara fitowa fili, a fadin manzon Allah (S.A.W) inda yake cewa: “Muminin bawa mai takawa, da sannu zai rika samun albarka a rayuwarsa, da kuma cikin iyalinsa da ‘ya’yayensa”.

(3)Tsayar da sallah :

Allah (S.W.T) yana cewa : (( ka umarci iyalinka da yin sallah, kuma ka yi hakuri a kanta, Ba mu tambayar ka wani arziki, mu ne muke arzuta ka, kuma akiba mai kyau tana ga masu takawa)) (Daha : 132).

(4)Dogaro ga Allah :

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : ” Da a ce kuna dogaro ga Allah dogaro na gaskiya, da ya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana fita da safe alhalin cikinsa ba komai (mai jin yunwa), sannan ya dawo cikinsa yana koshe”.

(5)Yawaita karatun Al qurani :

Kamar yadda Allah (S.W.A) Yake fada ((kuma wannan littafi ne Mun saukar da shi mai albarka ne)) (An am: 92), domin shi Alkura’ni, Allah ya sanya shi ya zamanto mai albarka ga wanda ya bi koyarwarsa, ya ke yawan karanta shi, yake kuma amfani da hukunce hukuncensa. Saboda haka ne Annabi (S.A.W) ya ce: “Gidan da ake karanta Alkur’ani a cikinsa, mala’iku suna zama a cikinsa, shaidanu kuma na kaurace masa, kuma albarka da alkhairi suna yawaita da kuma fadada a wannan gidan”.

(6)Yawaita Istigfari :

Istigfari wani babban dalili ne da yake samar da albarka, kamar yadda manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya lazimci istigfari Allah zai sanya masa kowane kunci ya zamo masa sauki, kuma ya sanya masa akowace irin damuwa, wata mafita, kuma ya albarkace shi ta in da ba (9)Yawaita yin sadaka : Annabi (S.A.W) ya ce: “Sadakar da mutum yake boye ta yayin bayarwa, tana gusar da fushin Ubangiji”.

(10) Haduwa guri guda yayin cin abinci :

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : ” Ku ci abinci tare; ka da ku rarrabu, domin ita albarka tana tare da jama’a, domin abincin mutum daya zai ishi mutum biyu, abincin mutum biyu zai ishi mutum uku “. Haka nan kuma akwai wasu nau’ikan abinci da suke da albarka,domin haka ana so mutum ya rika yawan cin su, ko ya samu dacewa, su ne kamar haka: Nono, Zuma, Dabino, da kuma Man Zaitun.

(11)Yin Sahur lokacin yin azumi:

Annabi (S.A.W) ya fada : “Ku yi sahur domin a cikin yinsa akwai albarka” , abin da ake nufi da albarka a nan shi ne samun lada, sannan kuma dan mutum ya samu nutsuwa a yayin azumin

(12)Yin amfani da ruwan zam-zam :

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Hakika ruwan zam-zam mai albarka ne, kuma tabbas abinci ne ga mai jin yunwa, kuma magani ga mara lafiya”.

(13)Dacewa da Daren Lailtul Kadri:

Allah madaukakin sarki yana cewa: ((Hakika mun saukar da Alkur’ani a dare mai albarka)) (dukhan : 3), wato Lailatul Kadri, domin alkhairinta ya fi na wata dubu .

(14)Halartar masallacin idi :

Domin ranakun karama da babbar sallah ranaku ne masu albarka; an karbo daga Ummu Adiyyah Allah ya yarda da ita tana cewa: “Mun kasance ana umartar mu (mu taron mata ) da mu fita ranar idi, mace budurwa ma ana so ta fito daga dakinta, mace mai ala’ada ma haka, sai su kasance a bayan maza, suna masu neman albarkar wannan rana da kuma tsarkinta” .

(15)Sa da zumunci :

Manzon Allah (S.A.W) ya na ce wa: ” Sa da zumunci, tare da kyawawan halaye, hadi da kuma kyakykyawar makotaka, suna gina gidaje (wato suna sanya tare da kara albarka a gidaje), kuma suna jawo albarka a rayuwar mutum”.

(16) Sammako wurin fita neman arziki:

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah ya yi Albarka ga alummata ya yin da suka yi sammako wurin neman arzikinsu”. Shi ya sa za ki ga yawancin masu arziki da aka tambaye su game da sirrin arzikinsu sai suka ce sammako wurin neman arziki, daga cikinsu akwai Sakhru al- ghamidi, wanda yake cewa: ” yayin da na ji hadisin Manzon Allah (S.A.W) game da yin sammako wurin neman arziki, sai na wayi gari ina fita kasuwancina a farkon yini, kuma an rawaito cewa ya samu arziki mai yawan gaske.

(17) Yin aure:

Allah (S.W.T) yana cewa : ((Ku aurar da gwauraye daga gareku, da salihai daga bayinku, da kuyanginku, idan sun kasance matalauta, Allah zai wadatar da su daga falalarsa)) ( Nur : 32 ), kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Ku nemi samun arziki ta hanyar yin aure ” amma fa ga wanda ya samu halin yin auraen.

Zainab Ja’afar Mahmud Adam

MARTABAR IYAYE
• “Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah, kuma kowa ya yi tunanin me ya tanada ranar gobe (kiyama) ku ji tsoron Allah, hakika Allah sanau ne game da abubuwan da kuka kasance kuna aikatawa” (Suratul Hashr: 18)

• Annabi (SAW) ya ce: “Allah wadaransa! Allah wadaransa!! Allah wadaransa!!! Sai aka ce wa kenan ya manzon Allah! Sai ya ce: wanda ya riski tsufan iyayensa duka ko daya daga cikinsu, kuma ya kasa shiga aljanna” (Muslim: 6674)

YAUSHE NE 1000000=1000???!!! (KALU-BALE GA WASU IYAYE)
Wata rana wani matashi ya dawo gida sai ya ga tarin jama’a a kafar gidansu, gabansa ya yanke ya fadi; ya dauka ko rasuwa aka yi, daga baya sai ya ga ashe wai kannensa biyu mata ake daurawa aure, bai san ma an ba da su ba ballantana daurin aurensu! da ya yi magana sai aka ce masa: “To in an gaya maka me za ka iya yi, (Shi da yake fama da taluci me ya yi wa kansa ballantana wasu)?!” Bbai san lokacin da hawaye ya  fara shatato masa ba, ya fito waje hawaye shabe-shabe yana cewa: “Allah ya raba mu da talauci!”

Bugu da kari, wata baiwar Allah ita ma ta koka da yadda mahaifanta suke watsi da ita, saboda mijinta ya talauce! Ta ce: A da, da suke da abin hannunsu, komai sai abin da ta ce a gidansu,  musamman ma ga shi ita ce babba a gidan, amma da “yau” ta ci su da yaki sai ya zamana, wani lokaci ko sa ranar kannenta da suke ciki daya sai dai ta ji a sama! Ta ce wannan abu yana damu na fiye da misali, a ce talauci ya zabge mata daraja haka a idon iyayenta!

Shi kuma wannan wani karamin ma’aikaci ne, kwatsam sai ya bar wannan aiki ya buge da wata kaskantacciyar sana’a  da yake zaton zai yi saurin samun kudi ta ita,  da aka tambaye shi, sai ya ce, ya yi haka ne saboda gudin fushin mahaifiyarsa, saboda kannensa da yayyensa duk mawadata  ne,  don haka idan sha’ani ya taso– kamar biki ko suna– su kan ba ta kudi da yawa, shi kuma abin da yake iya ba ta bai taka kara ya karya ba, ita kuma sai ta yi ta fada har barazanar tsine masa take yi in bai yi mata irin yadda ‘yan’uwansa suke yi mata ba, ya yi mata duk wani bayani amma bata yarda ba, shi ya sa ya yanke shawarar shiga wannan sana’a takaskanci ko shi ma ya samu kudi don ya kara kima a idon mahaifiyarsa, kuma ya huta da zagi da tozartawa a gaban kannensa ba iyaka!

Dorawa ‘ya’ya abin da ba za su iya ba, ko fifita wasu akan wasu don kawai suna da kudi, ko suna auren masu da-akwai, ya sabawa koyarwar manzon Allah (SAW).

Ya zo a cikin (Bukhari da Musulim) Wata rana wani sahabin manzon (SAW) ya ba wa dansa wata kyauta, sai ya zo ya ce da Annabi ya yi masa shaida a kai, sai  ya ce masa  ragowar ’ya’yanka ma duk ka yi musu irin wannan kyauta?”

Sai ya ce A’a. sai ya ce:

“Kuma kana son su yi maka biyayya kamar yadda zai maka?

Sai ya ce: Sosai kuwa!

Sai ya ce masa: “Ku ji tsoron Allah ku yi adalci tsakanin ’ya’yanku!” a wata ruwayar: “Kar ka kuskura!” a wata ruwayar “wannan kyautar a fasa ta!” a wata ruwayar “Ka je wani ya yi maka shaida ni ba na shaida akan zalunci!” shikenan sai ya fasa.

Kuma a hankalce idan muka duba za mu ga  da wanda ya mallaki milyan goma, ya bai wa mahaifansa kyautar milyan daya, da wanda ya mallaki dubu goma ya ba su kyautar dubu daya ba wani bambanci tsakaninsu; don kowanne 10% na dukiyarsa ya ba su!

Nura Abdullahi Madina (NAMadina)

SON MASO WANI KOSHIN YUNWA!
Ina ma’auratan da suke zaman doya-da-manja? GA SHAWARA:

Ibnu Jauzi Allah ya jikan sa (Ya rasu: 597 AH) ya ce:

Wani mutum ya kawo min kukan tsanar matarsa da ya yi, ya kara da cewa: Ba zan  iya sakin ta ba saboda abubuwa da dama, daga ciki dai akwai tarin bashinta da na ci, kuma gaskiya ni ba ni da hakuri, tana fahimtar irin tsangwamarta da nake yi ta hanyar furucin dake fitowa daga bakina idan ina korafi.

“Ibnul Jauzi ya ce: Sai na ce masa: wannan ba zai tsinana maka komai ba! Gidaje ta kofofinsu ake shigarsu, don haka ya kamata ka zauna ka kebe da kanka, ka yi tunani don ka san an dora ta a kanka ne saboda zunubanka, don haka ka dage wurin neman hanzari da tuba zauwa ga Allah”.

“Nunkufurci, da cutatar da ita ba zai wani amfani ba, kamar yadda Alhasan ibnul Hajjaj ya ce: “(Halin da kuka samu kanku a ciki)  ukuba ce daga Allah gareku, don haka kada ku tinkari ukubarsa da takobi, ku fuskance ta da istigfari”

Ka sani cewa kai kana matsayin wanda aka jarraba ne, kuma kana da ladan hakuri (Ya kusanta ku ki wani  abu amma kuma alheri ne a gareku) kamar yadda Allah ya ce.

Don haka ka mu’amalanci Allah Subhanahu da hakuri akan abin da ya kaddara maka, kuma ka nemi ya yaye maka. Idan ka hada tsakanin istigfari da tuba, da hakuri akan hukncin Allah, da neman yayewa, nau’o’i uku na ibada sun hadu, kuma a ba ka lada akan kowace daya daga ciki.

Kar ka bata lokacinka da abin da ba zai amfane ka ba,  kada ka ce kuma wai za ka yi dabara don ka tsere daga abin da aka kaddara maka. Allah yana cewa “Idan Allah ya  dora maka wani abin da zai cutar da kai ba mai ya ye shi sai shi” …

“Amma cutatarwar da kake yi wa matarka ba ka da wani dalili a kai, saboda dora ta aka yi a kanka, don haka ka mayar da hankali akan wani abu ba wannan ba”.

An rawaito daga wani daga cikin magabata cewa wani mutum ya zage shi, sai ya turmuza kundukukinsa a kasa ya ce: “Allah ka gafarta min zunubin da na yi maka da saboda shi ne ka ]ora wannan mutumin akaina”

“Sai mai neman Shawara ya ce: wannan matar tana mutuwar so na, kuma zagewa take haikan wurin yi min hidima, amma kin ta ya gama girkuwa a zuciyata!”

“Sai na ce masa: Ka mu’amalanci Allah ta hanyar hakuri da ita sai ka samu lada”.

“Wata rana an ce da Abi Usman Annaisabori: Wane aiki ne ka fi sa rai da shi (ranar tashin }iyama?) Sai ya ce lokacin ina matashi ’yan uwana sun sun yi, sun na yi aure na ki, (wata rana)  sai wata mace ta zo gurina ta ce da ni: “Ya Aba Usman Lallai sonka ya gama zuciyata, har na kasa bacci, na rasa inda zan sa kaina, ina rokon ka don mai juya zukata,  ka aure ni”!

“Sai na ce mata mahaifinki yana raye”?

Sai ta ce: ee; telan nan na guri kaza ai shi ne mahaifina

Sai na aika wa da mahaifinta wasika ina neman aurenta, sai ya yi farin ciki da wannan magana, ni kuma na kawo shedu, aka  daura mana aure.

Da na tare da ita sai na ga ashe: Ido daya ne da ita! Ga ta mai kambale!! (gurguwa-gurguwa) ga ta  kuma mummuna ta inna naha!!! Sai na ce: Allah na yi maka godiya bisa abin da ka kaddara min!

’Yan uwana sun ta zargina akan haka, ni kuma sai kara kyatata mata da mutunta ta nake yi, haka dai har ta kai ba ta bari na na fita saboda }aunar da take min.  Na daina zuwa majalisai  don fifita abin da take so (na na zauna kusa da ita), kuma  don kada ta ji wani abu a zuciyarta.

Haka na ci gaba da zama da ita tsahon shekaru goma sha biyar, wani lokacin (idan ina tare da ita) kai ka ce ina kan garwashi ne, saboda kin da nake mata,  amma ban taba nuna mata ba, har dai Allah ya dauki ranta, don haka ba wani aiki da na fi sa rai da shi a lahira irin wannan na kiyaye abin da yake zuciyarta na kaunata (duk da ba son ta nake yi ba)

Ibnul Jauzi ya ce: Sai na ce wa mutumin nan: haka mazaje suke, amma menene amfanin rakin wanda aka jarraba, da korafi, da nuna kiyayya kuru kuru. Hanyar dai da na gaya maka ita ya kamata ka bi; na ka tuba, ka yi hakuri, ka roki Allah ya yaye, kuma ka tuno zunuban da ka yi wa Allah har ka samu kanka a cikin  wannan hali sakamakon haka.

Idan ka samu yayewa da waraka to, in kuma ba haka ba, to yin hakuri bisa abin da Allah ya kaddara ibada ne, kuma ka rika kokarin nuna mata soyayya a zahiri ko da ba soyayyarta a zuciyarka, yi kokari ka tabbata akan haka.

Shi sasari ba shi ne mai laifi ba ballantana a zarge shi, kamata ya yi ka shagala da wanda ya garkama maka sasarin.  A sauka lafiya.

صيد الخاطر ص: 399