Adadin Matan da ya halatta a Aura

Saboda kasancewar kyale mutum ya auri mata iya adadin da ya ga dama ba tare da iyaka ba, abu ne da zai iya kaiwa ga rudani, zalunci da rashin kula da hakkokin matan; Kuma saboda takaita mutum ga mace guda kadai zai iya kaiwa ga kokarin biyan bukatar sha’awarsa ta hanyar da a ka haramta; Musulunci ya halatta mutum ya auri mata har zuwa hudu, domin wannan shi ne iyakar adadin matan da mutum zai iya kayiye adalci tare da kula hakkokin matan, idan har ya na bukatar mace fiye da daya.

Fa’idar auren fiye da mace daya ta hada da:

  1. Wasu lokutan ya kan zama dole a yi haka kamr idan matar ta kasance tsohuwa ko ba ta da lafiya kuma idan ya hakura da ita ba zai iya kame sha’awarsa ba, kuma su na da ‘ya’ya tare da ita. Ke nan, idan ya ci gaba da zama da ita kadai, ya na tsoron fadawa  cikin sabon Allah game da sha’awarsa, kuma idan ya sake ta, zai raba ta da ‘ya’yanta. Don haka wannan matsala ba ta da wani magani sai auren mace fiye da daya.
  2. Aure wata hanya ce ta samar da alakoki tsakanin al’ummomi da yawa don haka auren mata da yawa na fadada alakoki tsakanin gidaje da dama da al’ummomi, don haka ne ma Manzon Allah (SAW) ya auri mata da dama. .
  3. Auren mata fiye da daya ya na bayar da kariya gare su ta hanyar samar da bukatunsu na ci da sha da makwanci da sha’awa da haihuwa da sauran manufofin Shari’ar Musulunci.
  4. A cikin mazaje akwai wadanda ke da karfin sha’awa ta yanda mace guda ba za ta iya biya masu bukatunsu ba, ko da kuwa sun kasance masu imani da tsoron Allah, kuma ba sa son fadawa  cikin zina, kuma su na so su biya bukatarsu ta hanyar da Shari’ah ta halatta. Don haka, sai Allah, cikin RahamarSa, ya halatta ma su samun mace fiye da daya ta hanya amintacciya.

Sheikh Ibn Uthaimin

Published in: on May 16, 2008 at 3:10 pm Leave a Comment

Matan da ya haramta a aura

Matan da ya haramta a aura sun kasu kashi biyu:

(1) Wadanda su ka haramta har abada – su ne:

(A) Mata bakwai (7) wadanda a ka haramta saboda dangantaka ta jini da mijin: kamar yanda ya zo a Suratun Nisa’i aya ta aya ta 23, kamar haka:

(i) Uwayewato mahaifya da kakanni mata ta bangarorin uwa da uba, ko mai nisansu; (ii)’Ya’ya mata – wato ‘yar mutum ta cikinsa da ‘yar dansa ko ‘yarsa, kome nisansu; (iii) ‘Yar uwa – wa ya ko kanwa, uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya;(iv) Gwaggwanni – wato ya ko kanwar uba, da kuma gwaggwannin babansa, da babarsa da kakanninsa (maza da mata); (v) Innoni/Yakumbo – wato ya ko kanwar uwa, da kuma innonin mahaifinsa da mahaifiyarsa da kakanninsa (maza ko mata); (vi) ’Ya’yan ‘Yan uwa maza – wato ‘yar wansa ko kaninsa (uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya) da kuma ‘ya’yan ‘yayansu maza ko mata dss; (vii) ’Ya’yan ‘Yan uwa mata – wato ‘yar yarsa ko kanwarsa (uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya) da kuma ‘ya’yan ‘yayansu maza ko mata dss.

 (B) Mata bakwai (7) wadanda a ka haramta saboda shayarwa: Su ne wadanda su ka haramta a sama kamar yanda Manzon Allah (SAW) ya ce: ((Shayarwa na haramta duk abin da dangantakar jini ke haramtawa)) da sharadin: (i) Yaron ya sha nonon matar (sha na koshi) a kalla sau biyar, (ii) kuma dukkanin shayarwar ta faru ne kafin yaye.

Idan wadannan sharudda sun cika, to yaron ya zama dan wannan mata, kuma ‘ya’yanta sun zama ‘yan uwansa, ko da an haife su kafin ko bayan shayar da shi. Haka kuma, dukkan ‘ya’yan mijin da take shayar da dansa lokacin shayarwar sun zama ‘yan uwansa ko da daga wata matar suke ba ita ba. Amma ya kamata a lura a nan cewa, ‘yan uwan wanda a ka shayar din banda ‘ya’yansa, ba su da wata alaka da wannan shayarwar da hukun-hukuncenta. Don haka, ya halatta ga dan uwansa na jini ya auri matar da ta shayar da shi ko ya auri ‘yan uwarsa ta shawayarwa. Sai dai kuma ‘ya’yan dan da a ka shayar sun zama ‘ya’yan matar da ta shayar da shi da kuma uban dan da ta ke shayarwa a daidai lokacin da ta shayar da shi…

(C) Mata Hudu (4) wadanda a ka haramta saboda aurataiya: Su ne kamar haka:

 (i) Matan Uba wato matan mahaifinsa da kakansa (na uwa na uba) komai nisansa. Kuma da zarar an daura aure tsakanin mutum da wata mata, to ta haramta ga ‘ya’ayansa komai nisansu, ko da bai tare da ita ba. (ii) Matan ‘Ya’ya wato matan ‘ya’yansa komai nisansu, da sharadin dan ya tare da matar. (iii) Babar Matarsa wato mahaifiyar matarsa da kakarta, komai nisanta. Don haka, da zarar mutum ya auri mace, to babarta da kakanninta (na uwa da na uba) sun haramta gareshi, ko da bai tare da ita ba, komai nisan kakannin. (iv) ‘Ya’yan Matarsa da ‘ya’yan ‘ya’yansu (maza ko mata) da kuma jikanninsu komai nisansu, matukar dai ya tare da mata. Amma da saki ya afku kafin ya tare da matar, to wa]annan ‘ya’ya da ‘ya’yansu ba sa haramta gare shi, sawa’un an haife su kafin ko bayan ya aure ta.

 (2) Matan da su ka haramta a aure su zuwa wani lokaci – su ne:

 (A) ’Ya ko Kanwar Matarsa ko Goggonta wato na bangaren uwa ko uba har sai lokacin da su ka rabu da ita kodai ta rasu ko kuma bayan ya sake ta kuma ta kare idda.

(B) Matar da ke cikin Idda har sai ta kare iddar.

(C) Matarsa da ta shiga Harama – har sai ta kare aikin Hajji ko Umarar.

Sheikh Ibn Uthaimin

Published in: on at 3:07 pm Leave a Comment

Hukuncin Aure a Musulunci

Aure a karan kan sa halal ne, musamman ga wanda ke da sha’awa da iko; Sunna ce ta Manzannin Allah; Haka kuma, Manzo SAW ya yi aure, sannan kuma ya ce: ((Lalle ni ina auren mata, don haka duk wanda ya kyamaci sunnata, to ba ya tare da ni))

Don haka ne malamai su ka ce: “aure ya fi ayyukan nafila, ga wanda ke da sha’awa, domin shi ya kunshi ayyukan alheri da dama”.

Amma kuma a wasu lokuta, aure kan zama wajibi, kamar ga mutumin da ke da tsananin sha’awa kuma ya ke tsoron fadawa  cikin haramun idan bai yi auren ba. A nan, ya zama wajibi ya yi auren don kada ya fada cikin haram.

Published in: on May 7, 2008 at 7:34 pm Leave a Comment

Bayan wata daya jal da bikinsu…?

 A cikin watansu na farko bayan bikinsu, ango na ganiyar angwancinsa, amarya na cin amarcinta da tsinke, suna modar madarar  soyayya, saboda shakuwa da kaunar dake tsakaninsu kamar sa cinye juna….. Kai abin dai ba’a cewa komai. Suna cikin wannan aljanna duniya sai KWATSAM ba sai mahaifin angon nan ya nemi ya saki matarsa ba! abu kamar almara, ashe wai da gaske yake! Angon  ya dauka wani mummunan laifi amaryar ta yi wa mahaifin nasa, ko mahaifiyarsa, ko wani daga cikin magabatnsu, ko kuma wata muguwar illa ce ta bayyana a gareshi game da ita… Uban ya ce duk ba daya, “Dalilin da ya sa na ce ka sake ta; saboda wanta da yake auren kanwarka tun shekaru da suka shude ya sako min ita don rashin mutunci; ni kuma  duk wanda ya yi min kan kara sai na yi masa na itace! Don haka kai ma ka sakar musu ‘yarsu” da yaron ya ji wannan ne 

 dalilin sai ya ce: baba da binciki aka yi aka ga me ya hada su, maimakon wannan mataki” uban sai ya kada baki ya ce: “Wato ’yan ubanci za ka nuna, da cikinku daya ai da ba sai na ce ka sake ta!” Dan ya ce wallahi ba haka ba ne… ya yi juyin duniyan nan da mahaifinsa, ya ce sam. Ya yi kuka kamar hawayensa ya kafe, amarya kuwa cutar yau daban ta gobe daban saboda zulumi, kullum sai su zauna su yi dan koke kokensu, su dan yi ‘yan shawarwari su tashi. Rannan  ya je ya samu baffaninsa ya gaya musu halin da ake ciki, suka tausaya matuka, suka je suka yi ta bai wa dan’uwan nan nasu baki, amma kamar turi, suka ce  masa to su dai wannan abu ya fi karfinsu. Ya kuma  tsurewa, amma  dai bai karaya ba, sai ya garzaya wurin wani aminin mahaifin da shi kadai yake iya sa shi ya yi abin da bai niyya ba, da ya yi masa bayani, sai ya ce tashi mu tafi ta kwana gidan sauki! 

Ango ya yi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha don murna, har da zai yi wa amaryarsa waya  ya yi mata albishir, sai dai ya dakata ya ga yadda za ta kaya. Da ya je ya same shi, dan mutumin nan ya hada girar sama da ta kasa ya ce kwata-kwata ba za ta saku ba. Wato har da kai za’a hada baki a ci min mutunci?! Da dai ya ga ba sarki sai Allah, shi ma sai ya ce: “dana sai dai in taya ka da addu’a, amma abin ni ma ya fi karfina!” Angon  nan kamar ya barke da zawo, ya nufi gida a dimauce kamar ya yi hauka.

Daren nan kwanan zaune suka yi suna ta shawarwari, da asussuba sai ya ji bugun kofa ba-ji-ba-gani, yana budewa sai ya ga kannesa ne da suke ciki daya a firgice. Ya ce masa lafiya?! Sai ya ce: Umma jiya ba a gida ta kwana ba! Baba ya kore ta saboda wai tafiyar hawainiyar da kake yi wurin zartar da dokar da ya ba ka ta sakin wance

Ango ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir

Raj’un” ya shiga gida, matar ta taso hankalinta a tashe ta

ce masoyina mai ya faru? Ya ce ba komai, bara in je

masallaci in dawo, yana salla amma hankalinsa ba yana

wani wuri, bayan ya gama zikrin safiya, sai ya kasa komawa

gida, sai ya nufi gidansu don ya tabbar menene

ha}i}anin abin da yake faruwa.

Da ya shiga falon uban sai ya tarar da shi fuskarsa a murtike

kamar an aiko masa da mutuwa, kafin ya ce masa

“Ina kwana” sai cewa ya yi wallahi in ba ka saki yarinyar

nan cikin gaggawa ba a bakin auren uwarka! kuma

yanzun nan ka je ka kawo min mukullin gidanka – da

yake dama uban ne ya gina masa– ango dai ya ga abin

ya fuce “min sharrin” ya kai “ma hala}a” sai ya tafi gida,

idonsa jawar saboda kuka, ya je ya samu amaryarsa, ya

kwashe labari baki ]aya ya gaya mata, don haka yanzu

dai ba wata mafita illa su dangana su rabu, su yi wa juna

addu’a alheri….. Haba take amaryar ta yanke jiki ta fa]i,

yana shafa mata ruwa yana yi mata fifita, yana ba ta

ha}uri, yana ce mata komai }addara ce ta Allah….!

Shi ma yana share nasa hawayen da hankiji. Suna

cikin wannan hali sai ga uban a kansu, ya ce rubuta

takardarta ka ba ta “mu kowa ya ci tuwo da mu miya

ya sha!” wasu da suke tare da uban suna ta ba shi

baki, amma kamar dutse suke yi wa magana, yaron

nan dai da ya ga ba sarki sai Allah, ya ]auki takarda

da biro, ya rubuta mata saki ]aya, suka rungume juna

a gaban mutane suna ta kuka, amma uban nan ko a

jikinsa, sai da ya ga ya ba ta takardar nan hannu-dahannu

sannan ya tafi ya kyale su.

Yanzu dai tuni har sun rabu! Kuma Allah ka]ai ya

san irin mawuyacin halin da kowannesu yake ciki!

FA[AKARWA GA IYAYE:

 

 

Sau tari irin wannan

 

 

Published in: on April 17, 2008 at 11:00 am Leave a Comment

Allah ya kawo ranar da wance za ta je Unguwa!!!

 Ko shakka babu cewa agalabiyyar maza ba sa son matansu su rika yawan fita unguwa barkatai, kuma da ma wannan shi ne abin da shari’a ta yi umarni da shi; wato mata su zauna a gida (in ba wata lalura ba) amma shi wannan gogan namu kullum addu’arsa Allah ya kawo ranar da matarsa za ta tambayi unguwa, ya yi sauri ya bar ta idan ya ga ma ta jima ba ta tambayi unguwa ba, har tayi yakan yi mata ya ce: “wance ba ku da biki ko suna ne?” Ko kun san me yasa kullum mijin nan burinsa matar ta ce za ta je unguwa? Saboda ita a ka’idarta in kika ga ruwa ya taba jikinta to na sama ne, ko tsarki za ta yi, ko wankan tsarki, ko kuma alwala, in ba haka ba, in za ta shekara zancen wanka bai taso ba, ballantana a yi maganar ado da kwalliya, amma duk ranar da za ta tafi unguwa in ta caba ado sai ki dauka a ranar aka kawo ta dakin miji,  shi kuma yana so ya riga ganinta a cakare,  ba kullum kamar an  tono ta daga rami ba, yana ganin ta yana firgita!

A ganinki me yasa wannan mata ta zabi kullum ta rika zama busu-busu, in dai ba unguwa za ta ba, kuma wace shawara za ki bai wa irin wadannan kazaman  na ga-ni-kashe-ni

 

Published in: on April 16, 2008 at 12:35 pm Leave a Comment

KISHI

  • KISHI gishirin soyayya idan ya yi yawa ya baci; a dinga cizawa ana busawa.
  • KISHI kumallon mata idan ya taso miki ‘yar uwa ci gauta, ko lemon tsami, ko goro, ma’ana a nan ita ce  ki dinga HAKURI; in mutum ya yi hakuri sai ya dafa dutse ya sha romonsa, hakika Allah yana tare da masu hakuri.

                                                                 Gambo Shehu

Published in: on February 11, 2008 at 8:32 pm Leave a Comment

MATA IYAYEN GIJI!

Babu kokwanto cewa duk wanda Allah ya daukaka a addini ko a duniya to da akwai sa hannunmu mu mata, ko ta hanyar tarbiya a matsayin uwaye, ko kuma karfafa guiwa da taimako a matsayin mai daki. Ga wasu ‘yan shawarwari domin karfafa guiwar mai gidanki har hakansa ya cimma ruwa ya sami yardar Allah a gidan aljanna.

1-  Ki san bangaren da mai gidanki yake da wata baiwa, kwarewa … domin ki  karfafe shi, ki ba shi shawarwari, ki yabe shi, tare da yi masa addu’ar dorewa da kariya.

2-  Ki san bangarorin da yake da rauni a cikinsu domin ki taya shi magance su. Kar ki ingiza mai kantu cikin ruwan mutuwar jiki da kasala da cutar son duniya.

3-  Daga himmar mai gidanki sama, ki taimaka masa ya shiga cikin – ko ma gaba-gaban – masu rige-rige cikin ayyukan alheri, ya zama mai amfanarwa ne ga al’ummar Annabi (s.a.w).

A karshe, kar ki manta cewa: Allah ba ya tozarta duk wani kokarin mai kokari ko mai kankantarsa. Allah ya ce: Tashi in taimake ka! Saboda haka kada ki rena duk wata dama da kika samu cikin alheri. Ko ya motsi yake ya fi labewa.

Nafisatu Abubakar (Umm Abdallah)

Published in: on February 9, 2008 at 11:33 am Leave a Comment

Soyayya a Ma’aunin Shari’a

Gabatarwa:

Ma’anar So:  So ga bil adama shi ne karkatar zuciya da juyawarda izuwa wanda ake so, sakamakon wani abu da ya janyo karkatar zuciyar kamar kyon halitta, ko na dabi’u da halaye,  ilimi da kwarewa a wani abu dss. Zuwa wanda take, ko yake so. Irin wannan so shi ake kira so mai dalili (Conditional love)Irin wannan so yana karuwa, kuma yana raguwa, sakamakon cancanzawar sababan da suke gudanar da shi.

Akwai so da ake ce masa marar sababi (Unconditional love) Wannan irin so wasu suna ganin karya ne, wasu kuma suka ce cuta ne; shaidan ne yake sanya shi da izinin Allah a cikin zukatan da suka gafala, suka bar gurbin da shaidan zai cike shi da irin wannan nau’i na “so” zan ci gaba da wannan kasida nan gaba.ws

Fatima Isma’il Ibrahim

Published in: on February 8, 2008 at 2:35 am Leave a Comment

ASIRIN MALLAKE MIJI

Da yawa mata sukan rusa addinisu ta hanyar zuwa wurin bokaye da ’yan bori da sunan nemen asirin da za su yi don su mallake mazajensu, ba su san mallake namiji wani abu ne mai matukar sauki ba; ba ya bukatar sai sun yi kantafi da addininsu. Wata baiwar Allah mai hankali da za’a kai ’yarta daki, sai ta ba ta asirin da za ta yi ta mallake mijinta sai yadda ta yi da shi, amma wannan asiri ba binne ba ne, wata wasiyya ce mai tsadar gaske ta yi mata, da wannan ’ya ta bi wannan wasiyyar mahaifiyarta, ba sai miji ya zama bita-zaizai ba. Ga abin da take ce mata: ‘Yar leleta yau ne fa za ki bar gida ki je wani bakon wuri, wurin wani mutum da ba ki saba da shi ba, kuma karkashin shugabancinsa da kulawarsa za ki zauna, don haka ki zama baiwarsa; sai ya zama bawanki! ‘Yata ta kaina ki lamunce min wasu halaye guda goma tsakaninki da mijinki, za su zamar miki taska, da jari mai tsoka, kuma duk inda kika shiga sai ala-son barka. Ki zama mai hakuri da abin da kika samu. Tsakaninki da mijinki na ji na bi, kada ki rika zama cikin dauda da annakiya, ko ki zauna kina wari kamar jaba. ‘Kar ki yarda mijinki ya ganki gaja-gaja, kada kuma ki sake ya shaki wani abu a jikinki sai kanshi mai dadi. Ki rinka rangada kwalli; kar ki zauna ido kamar nama, kuma ki sani ba ki da turaren da da ya fi ruwa; don haka ki rika sirfa wanka akai-akai. Kada ki yarda lokacin cin abincisa ya yi ba ki gama ba; kin san yunwa yanzu ta sa mutum ya fusta. Kar kuma ki rinka buruntu ko kwaramniya lokacin da yake bacci; kin san haka babu dadi. Ki zama gwana wurin gudanar masa da gida; ki rika sa ido sosai akan komai na gidan kina alkinta masa dukiya, ki kuma rinka kula da iyayensa da ’yanuwansa hada da sa ido sosai akan ’ya’yansa da yaransa Kada ki yarda a ji wani sirrinsa a bakinki, kada kuma ki yarda ki saba masa; domin in kika tallata sirrinsa, ba ki san irin kafar ungulun da zai yi miki ba, in kuma yana sa ki abu kina ki, za ki rika kona masa rai. Kada ki yarda ki rika murna in yana bakin-ciki; don wannan rashin sanin yakamata ne, kada kuma duk ki yi wata iri; ki yi ta nunkufurci in yana cikin farin ciki; don za ki gurbata masa farin-cikinsa, ki kuma kona masa zuciya. Ki sani iya tsananin girmama shi din da za ki rika yi, iya girmamawar da za ki rika samu a wurinsa, hakanan iya goyan-bayan da za ki rika ba shi, iya tsawon-ran zamanki da shi. Ki sani cewa ba za ki taba samun yadda kike so a wurinsa ba, sai kin gabatar da yardarsa akan yardarki, kin kuma fifita abin da yake so, akan son ronki, a cikin komai. Allah ya sanya alheri

Published in: on January 30, 2008 at 9:31 pm Comments (1)