SHAYE-SHAYE TSAKANIN MATASA MAZA DA MATA

Ma’anar Shaye Shaye 

Duk lokacin da aka yi maganar shaye-shaye, ana nufin hadiyar kwayoyi masu sa maye ko ganyayyakin da shakarsu, ko cinsu kan fitar da mutum daga cikin tunani irin na ‘yan adam ya koma na dabbobi, Ko sheka wulakantattun abubuwa da mutumin kwarai bazai taba tunawa da suba a wajen abubuwa masu bugarwa da sa maye kamar:

1.     kwatami

2. solution

3. zargina

4. ganyen shayi

5. kashin kadangaru

6. maganin tari na yara dss.(Benelin)

SHIN ME YA JEFA YARAN MU CIKIN IRIN WANNAN?     

Ma iya cewa dalilai ne guda hudu ko biyar.

1.     kwaikwayon miyagun dabi’u ta hanyar kallon fina-finai ko tashoshin ketare ta hanyar gizo da sauran hanyoyin sadarwa.

2.     karance-karancen mujallun batsa marassa amfani

3.     watsi da tarbiyyar ‘ya ‘ya a sakarwa mata ko dan maraici a rasa mai dauka daga cikin dangin, ko rabuwa

4.     yawon almajiranci, tallace-tallace, da aikatau na kananan yara daga karkara zuwa birane.

5.     nunawa yaro gata don iyayensa na da wadata wadannan hanyoyi kowacce na iya jefa yara a cikin mummunar dabiar da zata iya gurbata tarbiyyar su.

To, tunda a zahiri ga shi an san dalilan gurbatar tarbiyyar, menene abin yi don a sami mafita?

LUBANA MUKHAR UMAR  

Published in: on February 10, 2008 at 4:32 pm Comments (1)

Hankoron jijjige matsala Ya kai ga karyar Cutar jijjiga!

Wasu matan suna da ragon azanci wurin magance masalar da suka samu kansu a ciki, sai su yi gudun gara su tarar da zago, ko su debo ruwan dafa kansu, ko su janyowa kansa abin fada har abada ana ganinsu da abin.  

Haka ce ta sa na yi tunanin fadakar da ‘yanuwana bisa wannan susanci da wasu mata kan fada ciki.  A wani lokaci ‘yan shekarun baya, a asibitin Murtala na Kano, bangaren ‘yan haihuwa, dakin ‘yan jijjiga, wani labara ya faru abin takaici, abin haushi, kuma abin dariya duk a lokaci guda. Wata rana ce wani mutum ya zo da matarsa a asibiti a demauce ita da   ‘yanuwanta kamar a sussume, suka ce jijjiga take yi.        

Ganin cewa matar kwana guda kenan da haihuwarta, sai ga unguwar zomar (mid wife) ta karbe ta ta kwantar da ita da nufin ta auna ta don ta tanadi bayanin da likita zai bukata game da ita Da unguwar zoman ta dauko abin awon jini wato (Blood pressure) to ba sai ta ga mata ta runtse idanunta ba, amma kuma tana ta karkada kafadunta da hannayenta ita wai ba ta yarda ba jijjiga take yi!Da unguwar zoman ta fahimci dawan garin,  sai ta ce: “duk wadanda suka kawo ta su kauce su ba da wuri” Sai suka kama gardama suna cewa: ai in sun bar ta ita kadai za ta fado. Duk sun gama gigicewa.Ita kuma ta tsaya kai da fata sai sun ba su wuri. Da kyar dai suka hakura suka fita.

Bayan sun ba su wuri sai ta ce da ita: “Haihuwa!!!” dan daure ki bar min wannan hannun don na auna ki amma kina iya girgiza waccan!

Abinki da rashin sani, gaular taki sai kawai ta bi umarnin; Ta canza hannun da take girgizawa! Wai ita za’a auna ta, sannan kuma ko karaya ta yi, sai ta dan bude idonta kadan don ta fahimci me ake son ayi mata. 

Da unguwar zoman ta fahimci haka, sai ta kirawo mijin wanda yake cikin mummunan tashin hankali ta tambaye shi, ko waani abu ya faru a tsakaninsu?

Da yake baya son fadan sirrinsa. Sai ya ce ai malama kin san ita rayuwa ba’a  rabuwa da ‘yan matsaloli!  

To a nan ta fede masa biri har wutsiya, ta ba shi tabbacin cewa matarsa lafiyarta lau, cutarta ta matsaloli ce ba ta rashin lafiya ba! sai dai da hadin kansa za’a bar ta a asibiti ta yini, ta nutsu, sannan a sallame ta. Ita kuma matar daga bisani aka ja hankalinta cewa nan gaba ba haka ake nuna fushi ba, ta yi kokarin warware matsalar tare da mijinta a gida ba sai ta yi abin da za’a kawo ta asibiti ba don hadarin da zai iya shigar da ita.Allah ya kyauta.

Sadiya Adamu Aliyu       

Published in: on February 9, 2008 at 12:05 am Leave a Comment