Mace a aikin Haji da Umara

Bismillahirrahmanir Rahim. Wannan }asida ’yar }warya }waryar matashiya ce  akan hukunce hukuncen da mata sauka ke~anta da su a  haji. Don neman cikakken bayani sai a tuntu~i malamai ko littattafan da aka wallafa a wannan fage.

MAHIMMAN {A’IDOJI GUDA SHIDA

1.     Shara]in kar~uwar haji da umara a yi su don Allah, kuma yadda Manozn Allah (SAW) ya koyar. Sai a dage.

2.     Ba bambanci tsakanin yadda ake ayyukan haji da na umara a cikin abubuwan da suka yi tarayya (Shiga harama, [awafi, Sa’ayi, Abubuwan da aka hana maniyyaci,  Aski).

3.     Gaba]ayan hukunce-hukuncen mace kafin haji-kamar  kama-kai, shiga ta mutunci, nisantar mummunar cu]anya da maza..dss a lokacin haji da umara ma suna nan daram.

4.     Ba bambamci tsakanin namiji da mace a haji da umara sai a ‘yan wurare ka]an da bayaninsu zai zo.

5.     Ba bambanci tsakanin mace mai tsarki da mai al’ada ko bi}i a ayyukan haji da umara in ban da wasu ‘yan wurare da bayaninsu zai zo. AMMA hukunce hukuncen da suke kansu kafin haji– kamar rashin yin sallah, azumi dss-suna nan har lokacin haji ko da suna da ala}a da hajin  (kamar shiga masallacin Ka’aba, yin sallah a Mina, yin azumi in ba ku]in hadaya. Dss. Amma za ta rama azumi in ta yi tsarki.

6.     Mace mai jinin cuta (Istihala) hukuncinta ]aya da  mai tsarki a ayyukan haji da umara.

HAJI DA UMARA A TA{AICE

HARAMA: Wato “Kudirce niyyar shiga ayyukan haji, ko umara, ko duka biyun ha]a da yin wani aiki ko furuci dake da ala}a da su nan-take – kamar talbiyya ko ]aura ihrami – a MI{ATI.” ita ce Farkon aikin da yake da ala}a da haji ko umara kai-tsaye; kuma ita maniyyaci zai fara yi,.

UMARA A TAKAICE: Abubuwa hu]u ne suka yi ta; Harama, [awafi zagaye bakwai, Sa’ayi sau bakwai, Aski ko Saisaye.

HAJJI A TAKAICE:  Hajji iri uku ne; TAMATTU’I (a yi umara bayan an gama a yi hajji a tafiya guda) {IRANI (gwama umara da hajji) IFRADI (hajji tsura).

¨       Mai {irani da Mai Ifradi ayyukansu iri ]aya ne sai a wurare biyu: (1) Niyya (2) Mai {irani yana Hadaya.

¨       Gaba]ayan ayyukan hajji ana gudanar da su ne cikin Kwanaki biyar ko shida KACAL; (8 Zul-hijja-12 ko 13 gareshi). Amma kafin nan Mai Tamattu’i zai yi Umararsa. Mai Ifradi da Mai {irani kuma za su yi abubuwa hu]u; Harama daga Mi}ati, [awaful {udumi, Sa’ayi (sa iya jinkirta shi su yi shi tare da [awafil Ifadha) Ci gaba da zama cikin harama.

AYYUKAN HAJI DAGA (8) ZUWA (13) 

Rana ta Farko 8 ga wata: Ayyuka uku: (1) Harama da haji (ga mai tamattu’i, sauran kuwa dama ba su fita ba) (2) zuwa MINA, (3)Wanzuwa a Mina zuwa wayewar gari.

Rana ta Biyu 9 ga wata: Ayyuka hu]u (1) Tafiya Arfa (2)Wanzuwa a Arfa zuwa fa]uwar rana (3) Barin Arfa bayan an tabbatar rana ta fa]i (4) Kwana a Muzdalifa.

Rana ta Uku 10 ga wata: Ayyuka biyar  (1) Jifan Babbar Majefa (2)Hadaya ga mai Tamattu’i da {irani (3) Aski ko saisaye (4) [awafin Ifala (5) A dawo Mina a kwana.    Ranakun Hu]u, Biyar da Shida ; 11,12,13  ga wata: Ayyuka biyu a kullum; (1)Jifan  dukkanin majefai uku (2) Kwana a Mina (wanda ya so ya iya barin Mina ranar sha biyu 12).   [AWAFIN BANKWANA: shi ne }arshen abin da alhaji  yake yi lokacin da ya yi azamar tafiya garinsu.

MACE A AIKIN HAJJI DA UMARA 

Wurin tahowa: Dole  ta kasance tare da mijinta, ko maharraminta. A fatawar wasu malamai za ta iya bin amintaccen ayari in hajin farilla ne ban da na nafiala.

Wurin Harama: (1) Ba wasu kaya takamaimai da lallai sai da su za ta yi harama; ta iya yi da duk irin kayan da ta so,in dai  bai sa~a wa shari’a ba (2) Za ta rufe gaba]ayan jikinta in ban da fuskarta da tafukanta, sai dai idan akwai wa]anda ba maharramnta ba suna kallon ta, sai ta rufe fuskar tata. (3)  Ba laifi ta sa safar }afa amma ban da ta hannu.

Wurin [awafi: (1)[awafinta daga gefe za ta ri}a yi; kada ta cu]anya da maza (2) Idan ta yi nuni ga Hajarul Aswadi ya wadatar kar ta ce sai ta sumbace shi(3)Ba za ta shafi Rukunul Yamani ba (4) Ba za ta fito da kafa]arta ba (5) Ba za ta yi sassarfa ba (6) Raka’a biyun ]awafi a gurin  mata za ta yi; ba a bayan Ma}ama Ibrahim ba.

Wurin Sa’ayi: (1)Sa’ayinta daga gefe za ta ri}a yi; kada ta cu]anya da maza(2)Ba ta yin gudu  tsakanin korayen fitulu. Wurin Aski: Ba ta yin Aski }wal-}wal. Saisaye kawai take yi; Ta ha]a kitso ko gashin kanta wuri guda, ta datse ko a datse mata gwargwadon ga~a ]aya ta yatsanta na hannu.

 MACE  MAI AL’ADA A A HAJJI DA UMARA 

Wurin Harama: (1) Za ta yi harama kamar kowa, amma ban da sallar da ake yi wurin shigar, (2) Za ta ci gaba da zama cikin harama. Da ta yi tsarki sai ta ci gaba da umara ko haji. Wurin [awafi: (1) Ba za ta yi ]awafi ba har sai ta samu tsarki, (2)Idan Tamattu’i take yi, kuma har takwas ga wata ta yi ba ta samu ta yi umararta ba saboda rashin tsarki to, Tamattu’inta ya koma {irani; sai ta yi irin yadda yake yi, amma an yafe mata ]awafin }udumi. (3) Idan jini ya zo mata  tana cikin ]awafi sai ta yanke ta fita daga masallaci, in ta yi tsarki  ta sake sabo.(4) Idan bayan  ]awafi ne ya zo mata, to za ta iya yin sa’ayinta haka. (5) Idan ba ta samu damar yin [awafin Ifala (wato ]awafin hajji) ba, har lokacin tafiyarsu ya yi, kuma ba dama ta jinkirta ko a jinkirta mata, to wasu malamai sun yi  fatawar ta yi }unzugu ta yi  ]awafinta haka, kuma ba komai a kanta; saboda ba ta da laifi, kuma Allah ba ya ]ora wa bawansa abin da ba zai iya ba. Duk wanda ya koma  garinsu bai yi [awafin Ifala ba – mace ko namaji- to komai daren da]ewa yana cikin harama har sai ya je ya yi (6) An yafe mata  [awafin ban-kwana .     

Wurin Sa’ayi: Za ta jinkirta shi sai lokacin da ta yi ]awafi.

Wurin Saisaye: Ba za ta yi saisaye ba sai bayan ta yi tsarki ta yi ]awafi ta yi sa’ayi. 

ALLAH YA SA MA{ABULIYA CE!

Nura Abdullahi Madina: namadina@gmail.com 

 

 

 

 

 

  

 

 

Published in: on November 5, 2008 at 5:39 pm Leave a Comment

Dangin Iya da Baba

lokacin da matata ta halarci wani mahimmin kwas a ofishin “A1 Nana” game da salon Annabawa a tarbiyyar ‘ya’yansu,  da alakarsu da su, zubin rayuwarmu  da ‘yayanmu ya canza baki daya; musamman ta bangaren alakarmu da su, zama da su, da hira da su; saboda mun ga tsohon tsarin da muke bi ya yi hannun-riga da na wadannan manyan bayin Allah, ba ya ga matsalolin da yake rikito  mana iri-iri.  

Na fahimci zama da yara, da fita tare da su, da shiga da su cikin manya, duk yana daga cikin tsarin annabawa wurin tarbiyyar ’ya’yansu, kuma ba ya kawo raini kamar yadda da muka dauka, yana ma dada sa yaran su   kara kaunar mahaifan nasu, su kara hankali, kuma su koyi abubuwa da dama na rayuwa da zama da jama’a. 

Tun daga lokacin duk wani wurin ibada -kamar masallaci-sa-da-zumunci-kamar zuwa barkar haihuwa– da taimakon jama’a kamar aikin gayya, da su muke tafiya, sai dai idan akwai wani uzuri. Mun ga alfanun wannan   salo na annabawa matuka gaya, kuma ku gwada ku ga abin mamaki.

Daurin auren wani dan`uwana da aka yi kwanakin baya shi ne na farko da na tafi da su Muhammadu ’ya’yana, Ahmad saboda zumudin za’a tafi da shi    kauye daurin aure  ko  bacci bai iya yi ba sosai; don shi ne ma ya tashe mu sallar asuba.

An dade a danginmu ba’a yi daurin auren da ya kwashi jama’a irin wannan ba; don kusan duk ’yanuwa na kusa da na nesa ba wanda bai halarta ba.

A kan hanyarmu ta dawowa sai Mahmud ya ce: “Abba dama haka ’yanuwanmu suke da yawa?” sai na ce masa: “Ai dangi ne da ku kamar tururuwa” sai Ahmad ya kyalkyale da dariya, ya ce “Abba ita tururuwa dangi ne da ita da yawa?” sai na ce masa ba ka taba ganin shurin tururuwa ba ne, ai ’yan uwa ne da ita kamar me, shi ya sa, idan mutum yana da ’yan uwa da yawa hausawa suke cewa yana da dangi kamar tururuwa” Sai Muhammad ya ce: “Abba kuna diban kama da wanda aka daurawa aure amma kuma ni ban taba ganinsa ba sai yau, amma dai ba KANEnka ba ne?”   

Sai na ce masa “A’a kanena ne dai na dangi,  shi ma sunansa Musa, don haka TAKWARAna  ne;  amma ni   na  yi fuce da TANKO; ne saboda YAYYEna  dukkansu mata ne. Shi kuwa ya fi shahara da KALLAMU; ka san  hausawa su kan kira  mai suna Musa Kallamu ko KALLA.

Ni da Kallamu tare muka yi wasan-kasa, kuma da ma ni da shi  abokan wasa ne; DAN-MACE-DA-DAN-NAMIJI muke. Kenan TAUBASHIna ne. Shi kuwa     daya Taubashin nawa wato TALLE, YAN-MAZA-ZAR muke da shi. Ma’ana, da TSOHOna, da GYATUMAr Kallamu, da BABAn Talle, uwa daya uba daya; shi ya sa ma ba na wasa da shi Tallen; da yake ka san  a al’adar hausawa, ‘yan-maza-zar ba wasa tsakaninsu, sai tsakanin dan-mace-da-dan-namiji.

Sai Mahmud ya ce: shi kenan  da azumi, in za mu tafi tashe mun huta da sayen talle! Sai na ce masa, a’a  ai ba talle yake sayarwa ba, abin da ya sa ake kiran sa da haka  saboda  babarsa tana haifar sa, ko waiwayowa ba ta yi ta gan shi ba, ta ce ga garinku nan; (ta mutu)  abin da yasa  ake  ce masa Talle kenan.

Talle ya fi kowa farin-jini a danginmu; saboda da kusan zaman-doya-da-manja ake yi da a dangin. A haihuwarsa ne aka sasanta; shi yasa ma ake ce masa SADAU.

Allah da ikonsa ni kadai ne a gidanmu namiji; don haka ko kuda ba’ a so ya hau kaina, shi kuma Kallamu mace daya ce jal a gidansu. Ita ce ‘yar babarsu ta  karshe; don haka ita ma ’YAR LELE ce Wannan  ‘YAR’ AUTA  ta su Kallamu KANDE ake ce mata; saboda duk  yayyenta maza ne; kamar yadda  na gaya muku tun da fari, Amma sunanta na yanka, Fadimatu. Sai dai ko da za ku  ji a gidansu ana kiran: FADIMA, ko, FATIMA, ko  TUMA, ko FATI, ko ZARA’U, ko ZARA, ko BINTA, ko BATULA , ko BATULU, ko TA RASULU,   ita din dai ake nufi, saboda duk mai suna Fadimatu hausawa kan kira ta da daya daga cikin wadancan sunaye. Harwalau dai akan ce mata TA-SALLA, ko GOSHI, Ta-salla saboda ranar sallah aka haife ta, Goshi kuma saboda irin alherin da babarta ta samu lokacin da ta haife ta.

Ahmad ya ce: Abba me ya sa sunayen ‘yanuwanmu wasu iri, dama akwai “Annabi dan Asabe!” sai Muhammad ya ce: “ta yiwu sunan wani sahabin ne, Ladi ma ina jin sunan matar wani Sahabi ne!” sai Muhmud ya ce: “kar fa mu fadi abin da ba mu sani ba; abba ya ce ba kyau, ga Abba ba sai mu tambaye shi ba!?” sai na ce:   Yauwa Mahmud haka ya kamata, in mutum bai san abu ba ya tambaya, kuma  kada  ya fadi abin da bai sani ba.  Sai Muhammad ya ce In Allah ya yarda ba zan kuma ba. To Abba mecece amsar tambayar da Ahmad ya yi?” Sai na ce:   ‘Ya’yan danginmu ba a faya kiran mu da sunayenmu na yanka ba; saboda kusan dukkaninmu sunayen wasu manya aka sa mana a dangin; to saboda kara irin ta Bahaushe, shi ya sa ake dan sakayawa.

Kun ga dai a gidan su  Kallamu  akwai wanda ake kira :

1-DAN-ASABE; saboda ranar Asabar aka haife shi.

2-DAN-TANI \ DAN-LITI; saboda ranar Litinin aka haife shi. 3-BALA \ DAN-BALA \ BALARABE ; saboda ranar Laraba aka haife shi. Amma an fi sanin sa da YAWALE; saboda mahaifiyarsa tana cikin aikin haji ta haife shi. Hajinta na bayu kuwa da  cikin Fadimatu ta yi, shi ya sa ma wasu suke kiran ita Fadimatun YABI, ita ma kuwa ranar laraba aka haife ta; don haka akan ce mata LARAI, wasu kuma su kira ta LARABA , wasu kuma BALARABA. Kai Fadimatu dai da sunaye ake iri iri!

Mu kuma a gidammu akwai:

4-LADI; saboda ranar Lahadi aka haife ta. 5-TALATU; saboda ranar Talata aka haife ta. Amma danginmu na karkara sun tsaya kai-da-fata akan wai ranar Litinin aka haife ta; don haka ma kwansu da  kwarkwatarsu TANI ko ATINE suke ce mata. 6- LAMI; saboda ranar Alhamis aka haife ta. 7-JUMMAI \ JUMMA; saboda ranar Juma’a aka haife ta.

Ba shakka Jummai ta sha-miya a duniyan nan ta Subahana; don ko GAMBOn TAGWAYEnta- ARUWA da MARKA- gaba yake da ni, ko da yake SAKOna ne; don ba wai can-can ya girme ni ba. Su kuwa ana kiran su da haka ne saboda lokacin damina aka haife su. Amma a makaranta an fi sanin su da Hasan da Husaina. Yaya Jummai – duk da ba dakinmu daya da ita ba- amma dai ta zama kamar mahaifiyarmu; da ma hausawa na cewa “Babbar Ya, Uwa

Sai Ahmad ya ce: “To Abba su waye KAKANIN KAKANInmu kuma?”     

Sai na ce: Mu dai TATTABA-KUNNEn Malam BARAU ne; don iyayenmu ne JIKOKInsa.

Muna zuwa nan sai Muhammad ya ce: Kash! Abba ga shi har mun karaso gida, kuma ba ka gama ba, ga shi tarihin da dadi! Sai Mahmud ya ce: Don Allah Abba in za ka tafi kasuwar ladin makoli ka tafi da mu sai ka karasa mana a hanya? Sai Ahmad ya ce Ee don Allah Abba ka tafi da mu  dama ina so in ga kasuwar kauye! Sai na ce: to shikenan, amma ban da wanda ya makara wurin shirin tafiya makaranta ko da sau daya ne, tsahon wannan satin, kun yarda? Suka ce EEEE!!! mun yarda.  Sai na ce: To,  Allah ya kai mu.

 

Da sati ya zagayo, tun da sanyin safiya su Mahmud suka je suka wanke mota tas suka goge, sannan suka yi wanka suka shirya, bayan mun karya kumallo tare da su, sai muka kama hanya, sai Ahmad ya ce: “Abba saboda lokaci ko za fara ci mana gaba yanzu? Sai Muhammad ya ce: Abba mun tsaye ne inda ka ce: kuna taba kunne, sai na ce masa a’a ko dai ba ka ji ba sosai, ce muku na yi: mu TATTABA-KUNNEn Malam BARAU ne; don iyayenmu ne JIKOKInsa.

Duk yaron da ya fara tsawon rai bayan an ta haihuwa a gidansu yaran suna komawa, hausawa su kan kira shi: “Barau” ko“BAWA” ko “DOGARA” in mace ce kuma su ce mata “AYASHE” To shi ma KAKAn iyayen namu daga nan sunan nasa ya samo asali, amma sunansa na yanka Sama’ila. Yana da danwa daya ana kiran ta KILISHI; saboda lokacin haihuwarta ya dace da lokacin da aka yi wa Babansu nadin sarauta, amma hakikanin sunanta, Bilkisu; shi ya sa ma ake  yi mata kirari da MAI GADON ZINARE.

Kaka Yusufu matansa hudu, ‘ya’ya talatin  daya babu, koda yake  kusan ashirn ba biyu sun riga mu gidan-gaskiya. Wadanda suke raye a yanzu kuwa su ne: Farko dai akwai wanda ake cewa:

1- MAI-KANO; Saboda Abdullahi sunansa.

2- GARBA\ SADAUKI; saboda Abubakar sunansa, kuma ana yi masa lakabi da SADDIKU.

3- SANDA; saboda Ummaru sunansa, kuma ana yi masa lakabi da FARUKU.

4- SHEHU; saboda Usmanu sunansa, kuma ana yi masa lakabi da ZUNNURAINI.

5- GADANGA SADAUKI; saboda Aliyu sunansa, kuma ana yi masa lakabi da HAIDARA.

6- SADIYA; saboda Halimatu sunanta.

7- ABU; saboda Zainabu sunanta.

8- KULU; saboda Hauwa’u sunanta.

9– DIJE; Amma asalin sunan Khadijatu ne, kuma ana yi mata lakabi da KUBURA

10-RAKIYA, amma asalin sunan nata Rukayyatu ne. Koda yake an fi ce mata AZUMI;  saboda da ita, da Babanmu, duk a watan azumi aka haife su; shi ya sa ma za ku ji maimakon Ummaru Sanda, an fi ce masa  DAN-AZUMI  ko LABARAN .

Shi kuma Baban Talle ranar sallah karama aka haife shi; don haka za ku ga an fi sanin sa da SALLAU . Amma da a ce ranar sallah babba aka haife shi da  ALHAJI za a rika ce masa duk da bai yi aikin Haji ba,  kamar dai yadda za su cewa mace HAJIYA in a ranar aka haife ta.

Dukkanin ‘yan uwan mahaifin nan nawa, wanda ya girma da wanda ya girme shi, in namiji ne BAFFA nake ce masa, in mace kuma GOGGO, yanzu ma na fadi sunayen saboda ku san danginku yadda ya kamata.

Babata Hajiya SHATU sunanta. Tana da ‘yan uwa guda biyu; INNA Salamatu, da KAWU Jafaru. Amma asalin sunnan nata A’ISHATU ne, shi ya sa za ku ji wasu suna kiran ta da INDO.

Muna kan hanyarmu ta dawowa sai aka bugo min waya, sai Ahmad ya ce: Abba wa ya bugo maka waya,? Sai na ce masa Yaya Jummai ce tana son in je in  raka ta karamar hakumar Zaria, wani  kauyen kayau a jihar Kaduna a Najeriya; don ta halarci shagulgulan bikin KORAU da AUDI ‘ya’yan wasu   kawayenta ZAZZAGAWA da yake ita Allah ya sa mata sha’awar harka da kauyawa.

Sai Muhammad ya ce Abba! Da ma mata suna yin zagi? Sai na ce kunnenka ya fara dodewa ne Muhammadu  Zazzagawa fa na ce ba ZAGAGE ba.  Sai ya ce: La baba ai na ji sosai  ni dai na dauka duk daya ne. Sai na ce a’a shi zagage jam’i ne na ZAGI ; wato mai jan akalar dokin sarki, shi kuwa Zazzagawa ai tilonsa shi ne BAZAZZAGE ko BAZAZZAGI. Ai duk tafiyarsu daya da irin su: KANAWA, KATSINAWA, DAURAWA, SAKKWATAWA, ZAMFARAWA,  KABAWA, HADEJAWA, ARAWA, ADARAWA, KURFAYAWA, ABZINAWA, ZABARMAWA, YARABAWA, GWARAWA, YAMALAWA, AGALAWA, NUFAWA, LARABAWA, TURAWA da shauransu. Ka ga ai dukkaninsu  jam’i ne na mutumin  da hausawa suke kira: BAKANO ko BAKANE, BAKATSINE, BADAURI, BASAKKWACE, BAZAMFARE, BAKABE, BAHADEJE, BA’ARE, BA’ADARE, BAKURFAYE, BA’ABZINE, BAZABARME, BAYARABE, BAGWARE, BAYAMALE, BA’AGALE, BANUFE, BALARABE,  da BATURE.

Sai Mahmud ya ce: to amma me ya sa jam’in BAFILATANI ake cewa  FULANI, a jam’in BABARBARE kuma ake cewa BAREBARI  me yasa  ba’a cewa Fulanawa ko Barbarawa ba kamar yadda aka ce a can.

Sai na yi murmushi na ce a to  ban da abin Mahmudu ai komai kusan ana  samun togaciya a ciki.

Sai Ahmad ya ce: Abba su wadancan da Umma Jummai za ta je bikinsu ya sunansu na yanka, kuma me ya sa ake ce musu Korau da Audi?

Sai  na ce: Shi Korau sunansa na yanka Zubairu, amma saboda babansa ya rabu da babarsa da cikinsa shi yasa ake ce masa Korau. Shi kuwa Audi abin da ya sa ake kiran sa da haka; saboda babansa ya mutu ya bar mahaifiyarsa da cikinsa, amma sunansa na yanka Aminu, Amma an fi ce masa Muhammadu; da yake  akwai wasu tarin sunaye da duk wanda kuka ji ana kiran sa da daya daga ciki, to a wurin hausawa Muhammadu ne. Kamar irin su: AUWALU, SANI, SALISU, RABI’U, HAMUSU, SADISU, SABI’U, SAMINU, TASI’U, ASHIRU, INUWA, TUKUR, BELLO, NASIRU, NAFI’U, MUJTABA, MUSTAFA, GALI, SHAFI’U, KABIRU, SAGIRU, BASHIRU, NAZIRU, MUNNIRU, NURU amma sai suka canza wasalin “u” da yake gaban bakin “r” zuwa wasalin “a” sai ya koma:                   

                          NURA ABDULLAHI MADINA

Published in: on October 31, 2008 at 6:54 pm Leave a Comment

Wasa Kwakwalwa

Abokaina matasa da kananan yara ga wani wasa mai ban sha’awa da nishadi, da yake kaifafa kwakwalwa da saurin gano abu. Za’a iya yinsa a makaranta lokacin “break” ko a gida lokacin da ba’a komai 

Yadda tsarinsa yake: wadanda suke da sha’awar shiga wasan za su zauna wuri guda su jeru, ko su yi da’ira, sannan sai daya daga cikinsu ya tashi ya je can nesa; inda ba zai ji abin da za su fada ba,  su kuma sai su hada-baki akan  wani abu  (mutum ko dabba, ko gari ko ma dai menene, amma ya zama sananne ne ga dukkaninsu, har shi wanda ya tashin ) sannan sai su ce masa sun shirya ya dawo, idan ya zo, shi kuma sai ya yi kokarin gano abin, ta hanyar tambayoyi; zai rika tambayarsu daya bayan daya, kuma  duk wanda ya tambaya zai fada masa gaskiya, amma ba zai yi masa wani  karin bayani ba, in kuma bai san amsar ba, sai kawai ya ce bai sani ba. Haka za su yi ta yi har sai ya gano, sai ya zauna, wani kuma ya tashi, idan ya dauki lokaci mai tsawo bai gano ba (kamar a yi zagaye uku, ko biyu gwargwadon yawan masu wasan, da yadda suka yi yarjejeniya, shikenan ya fadi sai a gaya masa) Saurin gano amsar yana da alaka da hazaka da kwarewarka\ki wurin ya tambaya. GA MISALAI  *Wasu ‘yan mata ne a makarantar kwana, su goma bayan sun yi bitar karatunsu sun gaji, sai suka zauna don yin dan nishadi da wannan wasan, sai suka ce wacece za ta fara? sai  Nusaiba  ta ce ita za ta fara. Sai ta tashi ta tafi nesa, su kuma sai suka hada baki akan Nana A’isha matar manzon Allah (SAW) san nan sai suka kwalla mata kira ta dawo, ta zo ta same su sun yi da’ira tsaf, suka matsa mata ta zauna.

Ta fara tambaya. Ta tambayi ta kusa da ita (wato ta daya) ta ce mata: mace ce ko namiji? Ta ce mace. Ta tambayi ta biyu tana raye ko ta mutu? Ta ce ta mutu. Ta tambayi ta uku; A lokacin Annabi (SAW) take ko bayan lokacinsa? Ta ce a lokacinsa take. Sai da ce yauwa! na fara gano bakin zaren! Sannan sai ta tambayi ta hudu: tana daga matan Annabi(SAW) ko ba ta ciki? Sai ta ce a tana ciki. Sai ta ce da ta biyar:  Mahaifinta shi ne babban abokin manzon Allah(SAW) wanda har Allah ya ambaci abotarsu a Kur’ani, ko ba shi ba ne? Sai ta ce shi ne. Sai ta ce Nana A’isha (R.A) Sai suka ce haka ne. Sai wata ta kuma tashi. Haka suka yi ta yi cikin nishadi. 

*Sumayya ita ce ta karshe, kuma da yake tana da kokari kwarai, ga ta  gwanar tambaya, sai ta yi ta cika musu baki; tana cewa ita in ta yi tambayoyi da yawa ta yi uku za ta gano! Su kuma da  suka fi ta, sai suka hada-baki akan ita Sumayyar, da ta fara ta yi ta yin tambayoyi ba kakkautawa amma ina! Duk basirar da take ji da ita ta kwakkwafe ta wai ko ta gano  wanda  ko abin da suke nufi ba ta gano ba, har daga karshe ta sallama ta ba da gari. Sai suka ce ai ke ce! Sai  ta rike kai, ta  yi kamar ta yi kuka, su kuma suka yi ta yi mata dariya suna cewa maganin mai cika baki kenan. Bayan sun ji garau sai suka koma kan muraja’arsu.

*Nan kuma ‘yan samari ne suka je gidan su wani abokinsu ziyara, bayan sun ci abinci sai babar abokin nasu ta ce su yi wannan wasan, kuma ta gaya musu yadda ake yi. Sai suka fara. Ita kuma tana zaune tana jin su. Suka yi ta yi tana dada nuna musu dabarun yadda ake yin tambayoyi masu azanci.

A karo na kusa da  karshe sai  suka hada-baki akan tsohon shugaban America George Bush uban shi wannan na yanzu. Da wanda ya tashi ya dawo sai ya fara canka.

Ya tambayi na daya; dan adam ne ko ba dan adam ba ne? Ya ce dan adam ne. Ya tambayi na biyu: A nan gurin yake ko ba’a nan yake ba? Ya ce ba a nan yake ba. Ya tambayi na uku: ya taba rike wani babban mukami a rayuwarsa ko bai taba ba? Ya ce masa ya taba. Ya tambayi na hudu: musulmi ne ko kafiri? Ya ce kafiri. Ya ce da na biyar: Shugabancin kasa ya yi ko wani mukamin daban? Ya ce shugabancin kasa. Ya ce da na shida: A Amerika ne ko a turai ko a Afrika? Ya ce a Amerika. Sai ya ce Clinton! Sai  aka ce a’a. Sai ya tambayi na bakwai; Yana raye ko ya mutu? Ya ce yana raye. Ya tambayi na takwas; lokacin da yake yakin neman zabe ya yi wa Amerikawa alkawarin cewa yakar musulunci ka’in da na’in shi ne daya daga cikin manyan  ayyukan da zai sa a gaba  in suka zabe shi? Ya ce ya taba fada. Sai ya ce  George Bush Uban  Bush na yanzu. Sai suka ce haka ne.

Sai uwar ta ce to ai yanzun ma kamar shi ne yake mulkin, ko ma in ce gara shi,  don kusan Amerika ba ta taba yin wawan shugaba, lusari makaryaci, mai nuna gabarsa ga musulunci da musulmi firi falo ba irin Bush  na yanzu. Ya tashi haikan yana yakar musulmi da muslunci da sunan yaki da ta’addanci. A karshe Allah tona asirin kafiri;  ya matsa bakinsa shi da kansa ya ce (Yakin Cross) yake yi (Ma’ana yaki da musulunci)! Dan karamin misali: Mutanen Iraqi MILYAN GUDA! Aka kashe a cikin shekaru biyar kacal da kasar ta yi karkashin mulkin mallakarsa! Amma har biki ya yi musamman larabar da ta fuce na cika shekaru biyar a Kasar! Kun gani ko ‘ya’yana! Don haka mu ci gaba da addu’a aniyarsu ta bi su, kulle-kullen da suke yi wa musulunci su koma kansu!‘ suka ce amiiin! 

Sai ta ce to yanzu sai ku tashi ku tafi gida kada a zo ana nemanku. Sai karamin cikinsu ya ce Umma to ai ni ban yi ba! Sai ta ce don Allah yi hakuri mantawa na yi. Bisimillah: suka hadu akan ZUMA, ita ma  ta shiga cikinsu wannan karon,  Da ya dawo ya fara ita:  Matum ne, ko guri, ko abin ci, ko abin sha? Ta ce Abin sha. Ya ce da na biyu: A kwai abin da ya fi shi zaki? Ya ce babu. Sai ya ce zuma. Sai suka yi ta yi masa kabbara suka ce haka ne. Ita kuma  ta kara masa da Naira 50 saboda bajintar da ya nuna wurinn saurin gano amsar, don kuma ta karfafa masa gwiwa. Yanzu kuma sai ku gwada.        

Published in: on at 6:51 pm Leave a Comment

Tona asirin Iyali

Wani bawan Allah daga cikin nagartattun bayin da suka shude yayi nufin sakin matarsa,sai wasu suka je suka tambaye shi “kai kuwa mai yasa za ka sake ta? sai yace “mai hankali baya tona asirin matarsa!” bayan ya sake ta, sai suka kuma zuwa suka tambaye shi cewa mai yasa ya sake ta? sai yace,”mai ya hadani da matar wani!”

Published in: on September 5, 2008 at 4:38 pm Leave a Comment

Tsallan Badake

Badake wani mutum ne da ya ga samu ya ga rashi, ko kuma a ce “ya bata rawarsa da tsalle” Yadda abin kuwa ya faru shi ne: ani sarki ne yake da wata ‘ya “Son kowa kin wanda ya rasa” ya ce ba zai aurawa kowa ba sai wanda ya tsallake wata tsohuwa, kuma wawakekiyar rijiya. Samari suna ta gwadawa amma kowa sai a dauko shi tsamo-tsamo. Rannan sai Badake ya zo ya gwada sa’arsa, aka yi ta yi masa washi, da kirari “Badake Badake!! Badake!!!, da kansa ya gama fasuwa, kawai sai ya zabura, ya sheko aguje, firrr kamar tsuntsu, ya shallake rijiyar nan! Sai aka yi ta iho, ana sowwa, ana yi masa tafi, ana kuma tila masa kasa, sai Badake ya fara cika baki yana cewa: dama wannan ’yar rijiyar ce don abin kunya kwana da kwanaki aka rasa mai tsallake ta! to ni ko da baya da baya ba sai in tsallake ta ba! Sai wasu suka ce gafara nan kai din me! wannan din ma sa’a ka yi! Kawai Badake sai ya tashi a fusace, ya nufi rijiya da baya da baya, su kama ’yan zuga sai ihu suke yi; Badake!, Badake!!. Badake ya taho da gudu da baya zai tsallake rijiya, sai ZUNDUUUM!!! ya fada” shi kenan ya ga samu ya ga rashi! Shi ya sa wanda ya samu kansa a makamancin halin wannan mutum sai a ce “ya yi tsallaen Badake. To, “ Allah ya kiyaye mu da tsallen Badake”

Published in: on May 20, 2008 at 2:51 pm Leave a Comment

Gidan Qais ibn Asim Assa’dy (RA)

 Lokacin da  Qais ibn Asim Assa’dy (RA) -daya daga cikin Sahabbai– yake cutar ajali, ya tara  ‘ya’yansa  ya ce musu: “Ku yi  aiki da abin  da zan gaya muku; don ba wanda za ku yi aki da maganarsa da ya fi ni son ya gaya muku abin da zai amfane ku. Idan  na cika kada ku yi min kururwa; don na ji Annabi (SAW) yana hana a yi wa mamaci ihu,  kuma shi ma da ya rasu ba’a yi masa ihu ba, ku yi min likkafani da kayan da nake sallah da su, ku shugabantar da manyanku … ku nemi na-kanku, don ku wadatu daga mutane, ba ku ba maula; don maula ita ce hanya mafi kaskanci da mutum zai bi don samun na abinci…”  

 

Published in: on April 16, 2008 at 12:33 pm Leave a Comment

Illar Tallace-Tallace ga ‘yan mata

Hakika talauci ko kuma yawan barace-barace kan sanya iyaye dorawa ‘ya’yan su talla ko dai ya zama haka din ne basu da abin da hannu wanda za su dogara a kan sa ko kuma ya zama uwa ta sa buri a kan ‘yar ta cewa idan ba ta hanyar talla ba, ba inda za ta samu abinda za ta yiwa ‘yar ta kayan daki.
Wani lokaci akan samu uba bashi da sana’a mai karfi da zata rike shi da iyalin sa bay a wadatar da su. Don haka sai ya zamo abin da ya ke kawowa ba ya wadatar dasu . don haka sai su iyaye mata su dorawa ‘ya ‘yan su talla don neman abinda za su tallafawa kansu.
Dun inda ka shiga a manyan biranan mu da kauyuka, za ka iske yara maza da mata suna ta garamrambar tallace-tallace na abubbuwa daban-daban
Mafi yawan mu daga nan suke lalacewa daga mazan har mata. Su kan shiga lungu-lungu rariya-rariya sune kasuwanci wuraran gyaran motoci tashoshin motoci da kuma wuraren gine-gine, wanda daga nan idan aka samu lalatatu suka lalata yaran maza ne ko mata da yawa an sha samun wadanda daga nan suke sake samun ciki.
    Za ka iske yara tun daga shekara bakwai har goma sha suna yawon talla shaguna da wuraren taruwar maza don Allah yau da gobe me ake zato zai faru. Sai shaidanu su fara yaudarar ta da kalmomi masu dadi ko kudi daga nan sai su sami damar biyan bukatar su da ita. Daga nan kuma iyaye su fara da na sani ana neman yadda za’a zubar da cikin ko kuma a rufa abinda za’a samu wani a daura mata aure da shi ba tare da ya san abinda ake ciki ba ‘yan watanni sai a ce ta haihu, shi kuma yace sam bai san haka ba don ba nasa bane. Ta tattara ta koma gaban iyayen ta. Abin kunya dai ya samu ! an kuma tozarta dokar Allah an ci amanar yarinya wajen rashin kula da tarbiyyar ta.
    Saboda haka ina kira ga iyaye akan suji tsoron Allah a kan ‘ya ‘yan su, su sami cewa amana ce a ka dora a hannun su. Kuma za’a tambaye su a rana sakamako. Ya zo a cikin Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “kowannen ku makiyayi ne, kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa, shugaba makiyayi ne, namiji makiyayi ne a kan iyalinsa, mace mai kiwo ce game da mijinta da ‘ya’yansa, saboda haka kowannenku mai kiwo ne kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa. (Bukhari)
    Ina kira ga iyaye a kan lallai su kula da hakkin ‘ya’yansu da tarbiyyarsu, da kuma mutunci, kada neman abin duniya ya sa idonsu ya rufe har su cutar da ‘ya’yansu su kuma cutar da kansu. Shin daidai ne mu jefa ‘ya’yanmu mata cikin halaka ta hanyar tallace-tallace, alhali babu ma wani abin kirki da suke kullawa?  
    Kuma wajibi ne muyi la’akari da kalubalen da ke fuskantar mata musulmi a yau saboda rashin karatun ‘ya ‘yan mu mata muna fuskantar wulakanci da tozartarwa da abin takaici duk lokacin da muka je asibiti ganin likita. Ya kamata mu yi wa kanmu kiyamul laili.
A maimakon mu bar ‘ya ‘yan mu suna yawon talla, mu sasu a makarantar lslamiyya da ta zamani don su sami ilimi da zasu taimaki kansu da ‘yan uwansu mata musulmi.
     DAGA SAFIYYA HUSAIN FALAKI

Published in: on March 28, 2008 at 3:31 pm Leave a Comment