Habaka Son Allah da Manzonsa a Zukatan ‘ya’ya

Habaka son Allah da manzonsa a zukatan yara ba karamin mahimmanci ne da shi ba, don wannan zai sa su rika bin Allah da manzonsa sau-da-kafa, a komai wanda wannan ya hada da biyayya ga iyayensu. Wasu daga cikin hanyoyin dasa wa yara ko habaka kaunar Allah a zukatansu su ne:

1. Iyaye su rika nuna son Allah a mu’amalarsu

2. A rika yi wa yaro bayanin waye

3. Gaya wa yaro ni’imomin da Allah ya yi masa

4. Gayawa yaro cewa komai Allah ne yake bayarwa

5. Gaya yaro kyautar da Allah ya shirya wa mai yi masa biyayya

 Zainab Ibrahim

Published in:  on February 9, 2008 at 11:16 am Leave a Comment

Wasiyyar Abil Walidil Baji ga ‘ya’yansa

Abu walid Albaji wani bijimin malami da ya rayu a karni na biyar ya yi wa ‘ya’yansa wata mahimmiyar wasiyya da ya kamata duk wani uba da malamin makaranta ya nazarinta, ya kuma amfana da ita wurin tarbiyyar ‘ya’yansa ko dalibansa.

Bara in dan tsakurowa mai karatu wani abu daga cikin wannan hamshakiyar wasiyya. 

  1. Ku kiyaye dokokin Allah a fili da boye.
  2. Ku kiyayi gina wani hukunci akan ilimin taurari, ko bokanci, domin wannan fitar da wanda ya gasgata shi yake yi daga addni, ya kuma shigar da shi cikin kangararru 
  3. Ba ku ba zulunci,  girman- kai,  hassada, gulma da munafunci 
  4.  Ku guji sauraron kade-kade; fitina yake haifarwa a zuci, da tunanin aikata sabo 
  5.  Kada dayanku ya fifita wani abin duniya akan danuwansa, sai ya rika yiwa danuwan nasa rowa saboda shi, ko ya juya masa baya, ko ya rika gasa da shi a ciki. Wanda Allah ya yi wa arzuki a cikinku to su ci tare da danuwansa, kar ya kadaita da shi, ya yi kokarin habaka dukiyar danuwansa, kamar yadda zai yi kokarin habaka tasa… ‘Yaruwa salon wasiyya salo ne na Annabawa da nagartattun bayi  a tarbiyya, kuma tasirinsa ya wuce duk yadda kike tsammani,  gwada shi ki ga bambanci. Allah ya sa mu dace  

 Batulu Aminu Dantata 

Published in:  on at 1:04 am Leave a Comment

MATSALAR RASHIN NUTSUWA

A cikin mutane akwai wadanda suke da bukatar kulawa ta musamman. Acikinsu akwai makafi, kurame, guragu, masu raunin  kwakwalwa da dai sauransu.Wadannan ana iya ganin raunin su a zahiri.  

Sannan akwai wadanda ba a ganin nasu raunin a zahiri sai idan anyi mu’  amala dasu sai aga cewar ba sa yin abubuwa yadda ya kamata. Imma dai  suna sabawa dokokin al’adunsu, ko kuma ba sa yi wa na gaba biyayya, ko  kuma halin bai dace da shekarunsu ba.

Kashi uku (3) zuwa goma (10) cikin dari na yawan yara suna da matsalar rashin nutsuwa. Sannan akan samu yara maza uku (3) masu matsalar kafin a samu mace daya (1).

ABIN DA YAKE HAIFAR DA SHI.

-Shan giya da shan taba ga matar da take da ciki, ko shan kwayoyi ba bisa ka’ida ba.

-Tabuwar kwakwalwa

– hatsarin abin hawa ko buguwar kai su kan jawo wannan.

-Abubuwan da ake karawa cikin abinci domin a hana shi lalacewa ko ya kara kyau (kamar kala).

-Cututtukan da ke saurin yaduwa.

-Gado, wajen iyaye ko kakanni.

-Bakwaini da wadanda kwakwalwarsu ba ta rika ba.

-Rashin samun bacci isashshe.

-Cin abinci mara kyau.

-Rashin kalubalantar abin  da ake yi.

-Nakudar/haihuwar da ta tsawaita kuma aka sha wahala.

-Matsalolin bayan haihuwa sune kamar sankarau, kumburin kai, jijjiga yayin zazzabi, ko rauni a kai.

-Matsalar da ake samu cikin kwakwalwa kan samu saboda rashin ko karancin wasu sinadarai da ake kira neurotransmitters.  

ALAMOMIN SUKIRINIYA:

Yawan tabe tabe da wasa da duk abun da yake kusa da yaro

-Yawan magana barkatai

-Ba zai iya zama tsaf ba yayin daukar karatu ko cin abinci da sauransu.

-Mutsuniya a wajen da yake zama ko ya dunga zagaye daki haka kawai.

-Wadanda suka girma suna so su hada abubuwa da dama suyi su a lokaci guda.

GARAJE

-Basa yin tunani kafin su aikata wani abu.

-Gaggawar bada amsa kafin su gama jin tambayar.

-Shan wahala yayin jira akan layi ko jiran lokaci ya cika.

-Ba sa iya sauraron mutum idan yana yi musu Magana.

RARRABUWAR HANKALI

-Basa maida hankali akan abu daya.

-Rashin tsai da hankali akan abin da ya dace suyi.Yin abun da ba shi ya dace suyi ba.

-Rashin iya tsara ayyukan da ke gabansu, da kammala aikin da aka basu da kuma rashin iya koyon sabon abu.

-Yin aikin makaranta a gida yana basu wahala, suna mantawa ko su barshi a makarantar. -Ba wuya su dunga kallace kallace ko sauraron kararraki marasa amfani.

-Basa kula da ka’idoji sosai, kuma suna da sakaci da yawan yin kuskure.  

YADDA ZA’A MAGANCE SU.

TA HANYAR MAGUNGUNA

-Sunadaran neurotransmitters suna daukar sako daga kwakwalwa zuwa sauran jiki ta hanyar jijiyoyi.

-Akwai magungunan da za a iya sha domin su yalwata wadannan sunadarai su sa kwalkwalwa ta yi aiki daidai.

-Suna sa kwalkwalwa tayi aiki sosai wajen kara fahinta da nutsuwa. 

TA HANYAR BADA ABINCI MAI KYAU.

-Abinci mai kyau shine ginshikin ginin jikin dan adam. Cin lafiyayyen abinci yana kara koshin lafiya.

-Akwai kuma wasu magunguna kunshe da sinadaren da ke cikin abinci wadanda ake cewa dasu “food supplements”. Ana iya shan su domin su cike gurbin abincin da bamu ci ba da kuma sunadaren da muka zubar yayin sarrafa abincin namu. Wadannan magunguna suna matukar taimakawa masu matsalar rashin nutsuwa.           

TA HANYAR CANZA HALAYYA.

-Gyaran halayyar yaron.

-A bashi damar hutawa domin samun nutsuwa.  

DANAGANTAKAR IYAYE DA ‘YA’YAYENSU

Burin iyaye shine su koyar da ya’ya’yensu yadda za su san ciwon kansu. Da yawa daga cikin iyaye suna ganin duka ya zama dole ta yadda za a samu horaswa gamsashshiya. Ana son iyaye su jajirce su bida ya’yansu daidai gwargwado (baka matsanta musu kuma baka sakar musu ba). Kuma iyaye suyi abota dasu, su  rage yi musu tsawa, da duka sai a samu dangantaka ingantacciya.  

HORARWA

-Sanar da yaro sakamakon da zai biyo baya idan ya yi laifi.

- Horon da za a yi wa yaro idan ya yi laifi ya zama ya yi daidai da laifin.

-Ka yi abota da shi amma idan har yayi laifi to ka kwabe shi. Ka dinga hasashen lokacin da ya yi abu mai kyau don ka yabe shi.

-Kun dunga samun lokacin yin raha kai da su akan abun da ke faruwa kullum.

-Iyaye kada su yadda suyi musu a gabanshi dangane da yadda za’a horar da shi.

-Ya zama ana yi masa kyauta idan yayi abu mai kyau, a kuma horar da shi idan har yayi laifi.

-Ka yadda da halayyar da ta dace da shi da kuma kin wacce bata dace da shi ba.

-Ka dunga bin sa a hankali ka ga yadda yake samun canji a halinsa, musamman da halayyar da ta dace da burin da ake so a cimma.

-Ka tuna da cewa kana so ya zama mai kyakykyawar dabi’a saboda haka kai ma sai ka kwatanta wannan dabi’ar.

-Idan wani yana horar da yaro kuma wani ya shigo wajen, ka da yayi katsalandan a cikin lamarin.

-Ka ba shi abun lada idan yayi abu mai kyau, ko ka yabe shi, ko ka dafa kansa, ko ka bashi wani abu da zai ji dadi kamar su abin wasa, ko abun ciye ciye ko kudi.

-Uwa da uba su suke da hakkin su horar da ya’yansu.

-Ka gaya musu abun da kake so su yi ba wanda ba ka so su yi ba.

-Ka tabbatar sun gane umarnin da ka basu, kayi ta nanatawa har su fahimta.

-Ka saurari yaro a tsanake, ka dunga duban fuskar yayin da yake yi maka magana.

-Ka samar da su wasu alamomi a fuska (kamarsu harara, zare ido, daure fuska, da sauransu) wadanda za kayi amfani da su yayin da suka yi wata dabi’a mara kyau.           Wadannan su ne kadan daga cikin bayanai game da yara masu matsalar rashin nutsuwa. Iyaye zasu amfana da shawarwarin da suke cikin wannan takardar domin rage wannan matsalar dake tattare da ya’yansu. Allah ya taimaka, Amin.

Dr. Hasana Sani Darma

Published in:  on January 30, 2008 at 9:27 pm Leave a Comment

Gabatar da Tarbiyyar Musulunci

Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, bayan haka:Saninku ne iyaye, malaman makaranta, da masu damuwa da gyara da kuma  ci gaban al’umma cewa Tarbiyya ita ce tubalin ginin dan adam, ko dai tubalin gini, ko kuma tubalin toka. Duk wata tarbiyya da ba ta musulunci ba, ko wadda ta ci karo da ita, to tubalin gininta na toka ne, ko ba jima, ko ba dade sunanta rushashshiya, tarbiyyar musulunci ita ce  daki-bari, kadaura babbar inuwa, kowa ya rabe ta sai ya huta, ballantana wanda ya tashi a cikinta. TO        

(1)Me ake nufi da Tarbiyya a Musulunci?Tarbiyya a Musulunci tana nufin “Gina cikakken Mutum Sannu a hankali; don bin umarnin Allah da na  manzonsa, da neman yardar Allah, da samar masa da nagarciyar rayuwa duniya da lahira, bisa tsari irin na musulunci”

(2)Menene hukuncin gina yaro Akan tarbiyyar Musulunci?Gina yaro akan tarbiyyar musulunci wajibi ne, kuma hakki ne daga daga cikin hakkokin yaro akan maifansa (ko walliyansa)Dalilai akan Haka: 

  1. Daga Kuri’ani: Fadin Allah Ta’ala: (يا أيها الذين آمنوا قوا أنفسكم وأهليكم نارا وقودها الناس والحجارة، عليها ملائكة غلاظ شداد لا يعصون الله ما أمرهم ويفعلون ما يؤمرون) (التحريم: 6)

Ma’ana: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku dauki matakin kare kanku da iyalinku daga wuta masu tsaronta wasu irin mala’iku masu karfin bala’i da tsananin gaske, ba sa sabawa Allah abin da ya umarce su, kuma duk abin da ya umarce su shi suke aikatawa”.

  1. Daga Hadisi; Fadin Annabi (SAW) “ألا كلكم راع، وكلكم مسئول عن رعيته… والرجل راع على أهل بيته، ومسئول عن رعيته، والمرأة راعية على بيت بعلها وولده، وهي مسئول عنهم… (متفق عليه)  Ma’ana: ” Kowa ya saurara ya ji: Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowanneku sai an tambaye shi kiwon da aka ba… namiji makiyayi ne game da mutanen gidansa, kuma sai an tambaye shi akan abin da aka ba shi kiwo, mace ma makiyiya ce a gidan mijinta, da ‘ya’yansa, kuma sai an tambayeta akansu… (Buhari da Muslim)
  2. Daga Maganganun Magabata Managarta

Abdullahi dan Umar Allah ya yarda da su ya ce da wani mutum: “Ka ladabtar da danka; don Allah zai tambaye ka a kansa; me ka koya msa, shi kuma za’a tambaye shi irin biyayya da kyautatawar da ya yi maka”  “الفقيه والمتفقه للخطيب البغداي: 1/49)

  1. Daga Hankali:
  • Ingataccen addinin musulunci ba zai samu baa sai da tarbiyya ta gari ta musulunci.
  • Yawan alheren da ta kunsa
  • Ita mafita a yanzu, kamar yadda ta kasance mafita a da.

(3)Mecece mabubbugar tarbiyyar Musulunci?Mabubbugar tarbiyyar musulunci, ita mabubbugar muluncin kansa (Alkur’ani da ingatattun hadisan manzon Allah SAW)‘Yan Rakiya:

  • Tarihin magabata mantarta
  • Rubuce rubucen  wasu malaman musulunci da suka yi tun shekaru aru-aru
  • Bincike-bincike, da rubuce- rubucen malaman wannan fage

Lallai a tace duk wani abubuwan da wadannan abubuwa uku suka kunsa da rariyar Alkur’ani da ingatacciyar sunnar Manzon Allah (SAW)

(4)Wadanne ne tuwasun Tarbiyyar Musulunci?

  1. Na farko Imani da Allah da rukunansa guda shida, da kuma yankunansa
  2. Shari’ar Musulunci
  3. Ingataccen ilimi mai amfani

(5)Rukunan Tarbiyyar Musulunci?

  1. Mai yin tarbiyya: sharadinsa ya zama ya dace da wannan gagarumin nauyi; don haka lallai ya zama Musulmi, mai hankali, yana da sani da kuma fahimta na yadda zai iya tarbiyyar, mutumin karki, tsayayye mai hikima, da juriya, yana jin nauyin da aka dora masa, kuma a shirye yake da ya dauke shi yadda ya kamata
  2. Wanda za’a yi wa tarbiyya: lallai a yi la’akari da shekarunsa, da abin da zai iya yi, da kuma (jinsisa- namiji ko mace)
  3. Wurin yin tarbiyya: wadanda suka fi mahimmanci su ne: masallaci, makaranta, iyali, alummar da suke kewaye das hi, da kuma kafafan watsa labarai”

(6)Manufofin Tarbiyyar musulunci da Magaryar tukewartaManufofinta a dunkule:

1.   Gina ilimi

2.   Gina cikakken musulmi

3.   Gina mafificiyar al’umma a bayan kasa

4.   Gina wayewa da ci gaba ta musulunci mafificiya

5.   Tabbatar da tsira, zaman lafia, da kyakkyawar rayuwa duniya da lahira gad an adam.Babban Abin da take nufin Tabbatarwa: Bautar Allah shi kadai ba tare da abokin tarayya ba, a rayuwar mutum shi kadai, da kuma rayuwarsa da jama’a   

(7)Mahimmanci da Fa’idojin Tarbiyyar Musulunci:A dunkule:

1.   Yadda shari’a ta ba ta kulawa ta musamman

2.   Yadda manyan bayin Allah; Annabawa, sahabbai, magabata manatarta,  manyan malamai das auran nagartattun bayin Allah suke ba ta mahimmanci na musamman.

3.   Yawan alhairan da take kunshe da su duniya da lahira

Filla-filla:Fa’idojinta Game da mutum shi kansa:

1.   Zai san kansa, kuma ya fahimci menene aikinsa a wannan duniya

2.   Tabbatar da babbar manufar samar das hi (kadaita Allah da bauta)

3.   Bautawa Allah ta hanyar abubuwan alheri da ya koya a cikinta

4.   Samun nagartacciyar rayuwa duniya da lahira

5.   Samun ladan duk wanda ya yi koyi da shi

6.   Zai rika jin cewa shi ba dan rakiyar zuwa duniya ba ne

7.   Kowa zai rika son sa yana girmama shi

Fa’idojinta game da mahaifa da ragowar dangi:

8.   Biyan hakki, da sauke nauyin da ke kansu

9.   Rabauta da biyayyar ‘ya’yan, da kuma kubuta daga saba musu

10.              Samun damar iya sarrafa yaran

11.              Kima da darajarsu za ta karu, ga kyakkyawan Ambato; saboda wadannan ‘ya’yan na gari masu tarbiyya.

12.              Dalili ne na samu dauka da mangarciyar rayuwa a duniyarsu da lahirarsu

13.              Ba za su rika jin kunya, da jin cewa da haihuwar wannan yaro gara barinsa ba

14.              Samun lada ta fuskoki da dama

Fa’idojinta Game da sauran jama’a:

15.              Yaduwar alhairai, da albarkoki, da umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna

16.              Samun zaman lafiya mai dorewa

17.              Karanta yawan barna a cikin al’umma

18.              Samar da taimakekeniya da soyayya tsakanin jama’a,

19.              Samun ayyukan yi fululu, da maganin zaman banza

20.              Habaka tattalin arzuki

21.              Raya kasa, da tabbatar hilafar dan adam a cikinta yadda ya kamata

22.              Fa’idantuwa da ‘ya’yan baiwa

23.              Rinuwar zamantakewar al’umma da rini irin na ingatacciyar rayuwa ta musulunci.

Fadakarwa: Duk wani alheri a cikin kowace irin tarbiyya, to akwai irinsa ko wanda ya fi shi a tarbiyyar musulunci.Macece manufar yin wannan fadakarwa?

(8)Illolin rashin gina yaro akan tarbiyyar Illolin rashin ginda yaro akan tarbiyyar musulunci yawansu ya isa, amma a takaicen takaicewa, duk kishiyoyin alhairan da aka ambata na gina yara akan tarbiyya ta musulunci.

(9)Fagagen Tarbiyyar MusulunciKasancewar tarbiyyar musulunci tana kokari ne na gina mutum don ya zama kamar yadda Allah da manzonsa ta kowace fuska suke sonsa, to kowane fage da zai ba da gudunmawa wurin wannan gine, fage ne daga fagagen tarbiyyar musulunci. Kamar 1.    Bangaren imani2.    Zuciya da ruhi3.    Bautar Allah4.    Kyawawan dabi’u5.    Ilimi6.    Hankali7.    Jiki8.    Zamantakewa9.    Sana’a10. Jagoranci. Dss

(10)Tsakanin Tarbiyyar musulunci da watarta:Ita Tarbiyyar Musulunci

  1. Daga Allah take, cike fal da annuri na shari’ar musulunci
  2. Ita ce tarbiyyar Annabawa da nagartattun bayi ga ‘ya’yansu
  3. Ta dace da “fidrar’ dan adam
  4. Ba kuskure a cikinta; don asalin da aka gina ta akai shi ma ba kuskure a ciki
  5. Tana da tabbas da izinin Allah
  6. Dole ce akan kowane musulmi da musulma su yi wa ‘ya’yansu
  7. Ita a karan kanta ibada ce
  8. Daukaka da darajar manufofinta da magaryar tukewarta
  9. Tana dacewa da kowane lokaci, zamani, wuri, da kuma yanayi
  10. Ba ta tsayawa (tun kafin haihuwar mutum, har karshen rayuwarsa
  11. Ta kunshi kowane sako na rayuwa, da kowane bangare da sashi na mutum
  12. Komai tana ba shi hakkinsa yadda ya dace da shi
  13.  Sashinta yana taimakawa shashi
  14. Zai yiwu a aiwatar da ita cikin sauki
  15. Ta hada tsakanin dad a yanzu
  16. Ba tufka da warwara a cikinta
  17. A bayyane take, ba ta da wahalar fahimta
  18. Tana bin komai daki-daki sannu a hankali
  19. Tarbiyya ce da take nusatar da baiwa da karfin da yake cikinsa wurin da ya dace.
  20. Ita ce kadai za ta iya samar da irin mutumin da ya cancanci halifancin Allah a ban kasa. dss

Ta haka za ki san tarbiyyar musulunci warin masaki ce a ba ta da abokin burmi.

(11)Salo daban daban na Tarbiyyar MusulunciDaga ciki akwai:

  1. Addu’a
  2. Mace ta gari
  3. Kyautatawa
  4. Sa ido
  5. Bin abu sannu a hankali
  6. Koyarwa (a ilmance)
  7. Koyarwa a aikace
  8. Wasiyya
  9. Wa’azi
  10. Buga misalai
  11. Amfani da hanyoyin kara fito da bayani
  12. Ba da kyakkyawan misali
  13. Tattaunawa
  14. Zaman tattaunawa tsakanin iyali
  15. Labari
  16. Abokantakar yaro
  17. Samarda “dan sandan ciki”
  18. Ciyar da yara daga halal
  19. Kwadaitarwa da tsoratarwa
  20. Sakawa da alheri da ukuba.

  (12)Abubuwa Masu Tasiri a Tarbiyya

  1. Kaddara
  2. Addini
  3. Wurin da mutum yake raye
  4. Mutanen da mutum yake cikinsu
  5. Gado (shi kuma hawa uku)
  • Gadon abubuwan da suka shafi halitta
  • Abubuwan da suka shafi hankali da tunani
  • Gadon abubuwan da suka shafi halaye da dabi’u

(13)Mahimman abubuwan da za su taimaka mana wurin gina ‘ya’yanmu akan Tarbiyyar musulunci1.   Dogaro da Allah da neman taimakonsa2.   Ilimi3.   Himma da tashi tsaye4.   Fahimtar dabi’u  da bambamcen da ke tsakanin ‘ya’ya5.   Bin hanyoyin da suka dace don tarbiyyantarsu.ربنا هب لنا من أزواجنا وذرياتنا قرة أعين واجعلنا للمتقين إماما  وصلى الله على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم(24/10/1428) الموافق (4/11/2007) Muhammad Nur Abdullahi namadina@gmail.com

Published in:  on at 7:37 pm Leave a Comment