Hukuncin tsinewa ‘ya’ya

Annabi (SAW) ya ce kar ku yi addu’a ga kawukanku, ‘ya’yanku da dabbokinku in ba ta gari ba, kar ta dace da lokacin karbar addu’a…

Wata rana wani mutum ya kawo wa Abdullahi ibn Mubarak karar wani dansa, sai ya ce masa: Ka tsine masa ne? sai ya ce: ee! sai ya ce: to ai kai ka bata shi!    

Published in:  on June 15, 2008 at 4:03 pm Leave a Comment

Baba Ana Ganinka!!!

Wani mutum ya kira dansa zo ka rakani unguwa sai suka tafi suna ta tafiya yaro ya gaji sai yaze Baba: ina zamu ne? Sai yace mun kusa. Can sai suka isa wajen wata katuwar bishiyar mangwaro sai uban yace tsaya nan zan hau idan kaga wani ya taho ka fada min sai in sakko da sauri kaji?  Yaro yace: to. Uban ya tattare ya hau bishiya ya mika hannu kenan zai tsinki na farko kenan sai dan yace: Baba ga wani nan yana kallon mu maza sakko bai ga kowa ba sai yace da yaron: kace wani yana kallon mu ina yake banga kowa ba, sai yaro yace: Baba Allah yake kallon mu, sai yace ya gane cewa abinda yayi shirin yi ba dai dai bane ya kuma gode Allah da yasa dan ya rike abinda ake dasa masa

Published in:  on June 7, 2008 at 4:37 am Leave a Comment

Daga cikin amfanin da na gari

Annabi (SAW) ya ce: “Idan mutum ya rasu duk wani aikinsa ya yanke sai abubuwa uku: Sadaka mai gudana, ilimi mai amfani, da kuma DA NA GARI DA ZAI RIKA YI MASA ADDU’A”

Don haka iyaye sai a dage wurin tarbiyyantar ‘ya’ya tarbiyya ta gari.

 

Published in:  on May 29, 2008 at 8:24 pm Leave a Comment

Tasirin Tsine wa ‘ya’ya

Wani mutum ya kai kukan wani daga cikin ‘ya’yansa ga Abdullahi ibn Mubarak (R) , sai Abdullahi ibn Mubarak ya ce: “Ka tsine masa ne?” sai ya ce: “Gaskiya na tsine masa!” sai ya ce: “To ai kai ka bata shi!”   

Published in:  on May 23, 2008 at 3:35 pm Leave a Comment
Tags: ,

Rana zafi Inuwa Kuna

Wata rana na bakunci gidan wani mutum sai ya fito mana da abinci kamar yadda al’adar girmama bako take wurin bahaushe, can sai dansa ya fito yana kuka wurjanjan, ganinsa ke da wuya sai ya kama fada yana cewa yaran nan kawai su su zo su hana mutane sakat! sai kawai ya daga hanu ya dalla masa mari ya ce tafi ka ba ni wuri, sai yaron ya yi kamar zai ruga wurin uwarsa cikin gida, amma sai ya yi turus; ya rasa inda za shi, ashe uwarsa ce ta fara zabga  masa mari ya taho wurin uban ko  ya samu sauki amma ina? ai wannan shine an yi gudun gara an tadda zago, ko in ce “Rana zafi inuwa kuna” ‘yanuwana mahaifa Annabi (SAW) yana cewa: “Tausasawa ba ta taba kasancewa a cikin abu ba sai ta adonta shi, ba’a kuma zare ta daga cikin abu ba sai ya yi muni”

Hamza Aliyu Sakwaya

 

Published in:  on May 16, 2008 at 2:13 pm Leave a Comment

Dukkaninku Makiyaya ne

Annabi (SAW) y ace: ” Kowa ya saurara ya ji: Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowanneku sai an tambaye shi kiwon da aka ba shi… Namiji makiyayi ne game da mutanen gidansa, kuma sai an tambaye shi akan abin da aka ba shi kiwo, mace ma makiyiya ce a gidan mijinta, da ‘ya’yansa, kuma sai an tambaye ta akansu… (Buhari da Muslim)

Published in:  on May 7, 2008 at 7:29 pm Leave a Comment

Yaushe dubu daya take daidai da milyan daya?

Wata rana wani matashi ya dawo gida sai ya ga tarin jama’a a kofar gidansu, gabansa ya yanke ya fadi; ya dauka ko rasuwa aka yi, daga baya sai ya ga ashe wai kannensa biyu mata ake daurawa aure, bai san ma an ba da su ba ballantana daurin aurensu! da ya yi magana sai aka ce masa: “To in an gaya maka me za ka iya yi?!” bai san lokacin da hawaye ya fara shatato masa ba, ya fito waje hawaye shabe-shabe yana cewa: “Allah ya raba mu da talauci!”

Bugu da kari, wata baiwar Allah ita ma ta koka da yadda mahaifanta suke watsi da ita, saboda mijinta ya talauce! Ta ce ada da suke da abin hannunsu, komai sai abin da ta ce a gidansu, musamman ma ga shi ita ce babba a gidan, amma da “yau” ta ci su da yaki sai ya zamana, wani lokaci ko sa ranar kannenta da suke ciki daya sai dai ta ji a sama! Ta ce wannan abu yana damuna fiye da misali, a ce talauci ya zabge mata daraja haka a idon iyayenta! Shi kuma wannan wani karamin ma’aikaci, kwatsam sai ya bar wannan aiki ya buge da wata kaskantacciyar sana’a da yake zaton zai yi saurin samun kudi ta ita, da aka tambaye shi, sai ya ce, ya yi haka ne saboda gudin fiushin mahaifiyarsa, saboda kannensa da yayyensa duk mawadata ne, don haka idan sha’ani ya taso– kamar biki ko suna– su kan ba ta kudi da yawa, shi kuma abin da yake iya ba ta bai taka kara ya karya ba, ita kuma sai ta yi ta fada har barazanar tsine masa take yi in bai yi mata irin yadda ‘yan’uwansa suke yi mata ba, ya yi mata duk wani bayani amma bata yarda ba, shi ya sa ya yanke shawarar shiga wannan sana’a ta kaskanci ko shi ma ya samu kudi don ya kara kima a idon mahaifiyarsa, kuma ya huta da zagi da tozartawa a gaban kannensa ba iyaka!

Published in:  on April 27, 2008 at 2:56 pm Leave a Comment

A tsine!!!?

 Wani shugaban makaranta ne ya tambayi uban wani yaro me ya sa bai biya ku]in makaranta ba har yanzu? sai ya yi }arya ya ce: [anana bai kawo min takardar ba. sai ]an ya ce – da }arfi: “La ila Masalli ila A TSINE!!!”  sai duk kunya ta kama uban (Me ka\kika koya?)

 

Published in:  on April 21, 2008 at 9:10 pm Comments (1)

Ba duka ne kadai magani ba

wata rana wani malami mutumin Najeriya yana zaune a masallacin Annabi Tsira da aminci su tabbata agareshi, akusa dashi akwai wani Balarabe yana karatun Qurani, sai malamin ya hango wani yaro aguje yazo ya sunbanci Babansa yana farin ciki, amma mutuminnan yai kunnen uwar shegu da yaronnan ko daga kai baiyi ya kalleshi ba, bai kuma ce uffan ba . 

   Da yaron yaga haka sai ya juya ya tafi. can wajen sallar magriba sai ga yaronnan ya dawo yasake gaida Baban nasa kamar yadda al adarsu take wato ya sunbance shi

nan-da-nan  Babansa shi ma ya rungume shi ya zaunar da shi suka ci gaba da hira irin ta yaro da Babansa.

    Malamin nan yana kallon duk abinda yake faruwa, amma abinda ya dare masa kai shine yadda Uban yaron yaki ce masa : Bata dahu ba balle ta kone, a karon farko amma yanzu ya kula da shi sosai. Da aka jima sai Malamin nan ya matsa kusa da mutumin nan ya tambayeshi dalilin haka, sai Uban yaron yace:- Yaron ya san laifinsa bai je makaranta bane sai maza ya ruga yatafi da ya dawo kuwa muka shirya.

     To yaku Iyaye ashe akwai matakai da yawa na tarbiyya da zamu yiwa yayanmu kafin aje ga duka? 

kamar su;-

rashin kallo.

ishara da fuska.

kifta ido.

karamar harara.

Kin fita dashi unguwa.

Hana shi rabin kudin alawar da ake bashi zuwa makaranta, misali in Naira goma ne sai abashi Naira biyar.
      Daga Hamza Aliyu Ibrahim.

Published in:  on April 1, 2008 at 5:44 am Leave a Comment

TSOTSON HANNU

Menene Tsotson Hannu?

Tsotson Hannu shi ne sanya dan-yatsa da yara suke yi a bakinsu suna tsotsa.

Jarirai da yara sukan sa babban dan yatsa, ko yatsu guda biyu a bakinsu suna tsotsa.

Me yasa suke tsotsan hannu?

  • Tsotson wani abu ne da ya zama wajibi a wurin yaro, don ta haka ne zai ci abinci kuma ya rayu.
  • Duk jaririn da bai samu biyan bukatar tsotsansa ta hanyar ciyarwa ba, to zai tsotsi ‘yan yatsun sa.
  • Tsotson hannu yana sa yaro ya samu gamsuwa ta wani dan lokaci.
  • Tsotson hannu yana ba wa yaro damar kama kansa; wato maimakon ya yi kuka sai ya jefa dan yatsansa a baki ya yi ta tsotsa.
  • Tsotsan hannu ya na kwantar sa hankalin yaro. 

ILLOLIN TSOTSON HANNU

Dr. Hasana Sani Darma 

Published in:  on February 10, 2008 at 4:18 pm Leave a Comment