A Dinga Sara ana duban Bakin Gatari

‘Yar uwa! Kada ki manta da cewa duk mai rai fa zai mutu, kuma kowa zai shiga kabari, kabari kuwa dayan biyu ne, ko dai ya zama gidan ni’ima, gidan dadi da yalwa, kuma a fadadawa dan aljanna kabarinsa gwargwadon zira’i saba’in zai kasance cikin ni’ima har zuwa tashin alkiyama. Ko kuma ya kasance gidan azaba da kunci da wahala, za’a rika yi masa azaba tun daga kabarin ana kuma dukansa da guduma ta wuta. Kuma za’a kuntata masa kabarin a matse shi har kasusuwansa su rika kara, wanda da mutanen duniya za su ji da sun narke saboda tsananin firgita.Bayan kwanciyar kabari na iya shekarun da Allah ya kaddara, za’a tayar da mutane su tashi a firgice cikin dimuwa, kowa yana gudu ba tare da ya san inda ya nufa ba. Sannan a gurfanar da mutane a gaban Allah (SWT) wanda babu wani sarki a wannan ranar sai shi.Laa ilaha illallah! Hakika wannan rana ce ta tonon asiri, ranar tonon silili, ranar da babu abin da zai boyu sai an bayyana shi. Allah muna rokon ka ka kiyaye mu ka fitar da mu daga azaba, da tsoro da firgita na wannan rana, amin.‘Yar uwa bayan wannan hisabi, kowa za’a ba shi masaukinsa da ya dace da ayyukansa a mazauni na dauwama guda biyu; ko dai aljanna wadda fadinta ya kai nisan dake tsakanin sama da kasa. Ko kuma wuta mai tsananin zafi wadda har sashenta yana cinye sashe. Allah ka nisanta mu daga wuta, ka tserar da mu amin. Mai rabo shi zai shiga aljanna, Allah ka sa muna da rabo a cikinta da iyayenmu, da mazajenmu da ‘ya’ya da duk zuriyarmu, da duk musulmi baki daya. Marar rabo kuma wanda ya butulce wa ubangijinsa, ya bi son zuciyarsa, wannan wuta ce makomarsa. Allah (SWT) yana cewa:“Duk wanda ya kubuta daga wuta kuma aka shigar da shi aljanna hakika ya rabauta” (Ali Imran 85).Ya ke ‘yar uwa! Hakika bana shakkar cewa kina kaunar samun wannan babban rabo; don haka kada ki kuskura ki yaudari kanki, ko a yaudare ki, aljanna ta wadanda suka yi aikin kwarai ce, yin imani da ayyuka na kwarai su suke isar da mutum kofofin aljanna, kuma karantar Alkur’ani shi ne tsanin da ake hawa benayen aljanna.Saboda haka ‘yar uwa, ki nisanci duk wasu shaidanu da na ambata miki ire iren su a baya wadanda a ko yaushe suke son su ga kin yi wa Allah tawaye ki bata, kuma ki halaka. Ki toshe kunnuwanki daga duk wani kiran ‘yanci ko hudubar shaidan da za su rada miki, ki ce musu Ahir dinku.Ki zama baiwar Allah ta gari, mai tarbiyyantar da ‘ya’ya na gari wadanda za su zama manyan gobe. Ki zama babban jigo na gina wannan al’umma, kada ki zama hanyar ruguza ta.A karshe nake kara jaddada mana cewa yin riko da Alkur’ani da sunna shi ne zai kai mu ga gaci muddin mun rike su ba za mu bata ba, ba kuma za mu tozarta ba, a nan duniya, kuma a lahira mu samu sakamako mai girma. Allah ya sa mu dace Amin.Allah Ka nuna mana gaskiya kuma Ka bamu ikon bin ta, muyi aiki da ita,  Ka nuna mana karya Ka ba mu ikon guje mata. Allah Ka ba mu aljanna don rahamarKa, Ka nisantar da mu daga wuta. Allah Ka jikan iyayenmu da kakanninmu da ‘ya’yanmu da ‘yan uwanmu, da duk musulmi baki daya. Allah Ka yafe mana kura-kuran mu Amin. 

Safiyyah Hussain Falaki

Published in:  on February 9, 2008 at 1:19 am Leave a Comment

“Tufka da Warwara”

An karbo Hadisi daga Abu Huraira Allah ya kara yarda da shi ya ce:        

An tambayi manzon Allah (S.A.W) cewa:  Ya Rasulallah! hakika (wance) tana sallar dare, ta yi azumin nafila da rana, tana aikata ayyukan alkhairi, kuma tana sadaka, amma tana cutar da Makotanta (da harshenta)! Sai ya ce: “Babu alkhairi a gareta tana daga cikin ‘yan wuta” sannan aka ce (wance) kuma tana salloli wajibabbu, ta yi sadaka da dan abu kadan, amma bata cutar da kowa. Sai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ita yar aljanna ce”. (Bukhari fil adabil mufrad).

‘YAR UWA IDAN KIKA DUBA WANNAN HADISI ZA KI GA CEWA DUK ALKHAIRIN DA KIKA KULLA TO CUTAR KISHIYA YA WARWARE SHI. WANNAN SHI NE TUFKA DA WARWARA. ALLAH YA YA KIYAYE AMIN.

Ummu Huwailat

Jamilat Bint Abdul’Aziz Alkazauriyya. 

Published in:  on at 12:16 am Leave a Comment

SUTURA MUTUNCI

Assalamu Alaikum Wa rahmatullahi Wa barakatuh

Bayan haka, ya yar’uwata madaukakiya, ina fatan kina lafiya. Wannan wata  tsaraba ce nake dauke da ita, domin dai fatan mu shi ne mu gudu tare mu tsira tare.

Bayanin da na ke dauke da shi kuwa shi ne: akan HIJABI irin wanda shari’a ta yarda mu yi amfani da shi. Ya ‘yar’uwata! ki tuna fa gargadin da Allahu (S.W.T) ya yi mana dangane da sanya HIJABI irin na musulunci, inda yake cewa a cikin Suratul-Ahzab aya ta (59) (يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِنْ جَلَابِيبِهِنَّ ذَلِكَ أَدْنَى أَنْ يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَحِيمًا) (59)Ma’ana: “Ya kai  wannan Annabi! Ka fadawa matanka da ‘ya’yanka da matan muminai, su kusantar da kasa daga manyan tufafinsu wannan zai fi sa a gane su, kuma kada a cutartar da su, Allah ya kasance mai yawan gafara, mai yawan jin-kai.” Da kuma fadin Allah (S.W.T) cikin Suratun-Nur aya ta (31) وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَى جُيُوبِهِنَّMa’ana:  “kuma su rufa mayafansu akan rigunansu.”Don haka ya ‘yar’uwata, jikanyar Nana Aisha! ki tuna fa lokacin da wannan aya ta sauka, matan sahabbai barguna suka  rinka lullubawa suna fita da su, don tsananin son Allah da Manzonsa, da kuma kokarin kiyaye dokokinsa.Kuma kina da masaniya akan cewar wadannan mata sun fi mu kyau da daraja da matsayi? Don su ne fa su Nana Aisha su Nana Zainab,  su Nana Ummu-salama, su Nana Fadima ‘yar fiyayyen halitta, da sauran matan sahabbai, (Allah ya yarda da su gaba daya). To, mu yau wane matsayi muke da shi? kuma wane kyau muke da shi? Da har za su hana mu bin dokar Allah (S.W.T)? don haka ne nake ganin ya kamata mu yi wa kanmu fada, mu kuma sake tunani, domin gyara wannan matsala mai matukar muhimmanci mu kuma nusar da ‘ya’yanmu da kannenmu akan suturar musulunci. ‘Yar’uwata! A nan ba ana nufin sai kin sayi yadi baki ko fari ko wata kala ta musamman kin dinka HIJABI  irin wanda ake kira HIJABI a yanzu ba, a’a ko wace irin sutura kika lullube jikinki da ita, zai iya zama hijabi, matukar dai ya cika sharuddan da musulunci ya gindaya. Ga su  kamar haka:-

1.  ya  kasance ya rufe miki jiki gaba daya.

2.  Ya kasance sakarsa tana da kauri, ba shara-shara ba.

3. Kada ya zama matsattse,ta yadda za’a iya ganin tudun abin da ya ke kasansa.

4. Kada ya zama tufafin alfarma ne.

5. Kada ya zama mai ado ko mai daukar hankali.

6. Kada ya yi kama da tufar maza.

7. Kada ya yi kama da tufar kafirai; domin duk wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, shi ma yana cikin su.

Kuma ya kamata mu kiyaye cewar:- hijabi ba wai ya shafi matan Aure ba ne kawai, a’a ya shafi duk wata mace da ta balaga, ma’ana yadda sallah ta wajaba akan ki, to haka hijabi ma ya wajaba akan ki.. Daga karshe ina mai fatan Allah (S.W.T) ya ba mu dacewa, ya sanya mu fi karfin zuciyarmu, ya kuma sanya mu cikin masu fifita tsarin Allah akan son zuciyarmu. Amin

                                                                                  Daga:-‘Yar uwarki: ASMA’U BUKHARI SAFWAN

Published in:  on February 8, 2008 at 4:03 am Leave a Comment

Hanyoyi 17 domin samun rayuwa mai albarka

Assalamu Alaikum warahmatullahi wa bara katuhuYana daga cikin abin da duk wani dan adam yake nema a rayuwarsa ta duniya, SAMUN ALABARKA; domin da haka ne zai samu rayuwa ingattacciya  mai cike da dimbin nasara da ci gaba, kuma hanya ce da za ta jawo wa ragowar iyalansa, da ma dukkan zurriyarsa samun albarka.Duba da mihimmancin wannan al’amari na ga dacewar in dan yi mana tsokaci game da abubuwan da suke sa mutum ya samu  albarka a rayuwarsa ta yau da kullum, dafatan Allah ya amfanar da mu, ya kuma datar da mu izuwa abin da ya ke shi ne dai dai .

Hanya ta Farko:  Fara komai da ambaton sunan Allah: Yana daga cikin abubuwan da suke jawo albarka a rayuwar mutum fara komai da ambaton sunan Allah, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Idan mutum ya shiga gidansa, yana mai ambaton Allah yayin shiga, da kuma lokacin cin abinci, shaidan  zai cewa abokansa:  “Ba ku da gurin kwana da kuma gurin cin abinci a yau”.Don haka ka ambaci sunan Allah; domin ambaton Allah shi ne abin da ya kamata musulmi ya yi kafin kowane aiki,  haka ma har a wurin tarawa da iyali, (jima’i) an so ka ambaci Allah kana mai cewa: ” Allahumma jannibnas-shaidana, wa jannibus-shaidana ma razaktana”, to idan Allah ya azurta su da da a wannan daren, to hakika zai albarkace shi, domin duk al’amarin da mabudinsa ambaton Allah ne, to kuwa albarka ba ta kaurace masa.

Zainab Jaafar Mahmud Adam

ummuaishatu@gmail.com 

Published in:  on February 7, 2008 at 12:35 pm Leave a Comment