“Ku kyautata Allah yana son Masu kyautatawa” (Bakara: 195)
¨ “Wanda ba ya girmama manyanmu,kuma ba ya tausayin kananamu ba
shi daga cikinmu” (Sahihul Jami’a)
¨ Annabi (SAW) ya ce: “Ku rika musayen kyuta (a junanku) sai soyayyar
(dake tsakaninku) ta karu.(Sahihul Al’adabul Mufrad)
¨ Annabi (SAW) yana ziyartar ‘ya’yansa a gidajen mazansu. Kai ma ka rika yin haka nan, sai ka dace da sunna, kuma soyayyar dake tsakaninku ta kara habaka.
Allah yana son Masu kyautatawa
SHAWARWARI!!!
Aljanna tana karkashin dugadugan mahaifa (mata) (Ahmad da Nasa’i)
• Don isar da sakon nasiha, ga mijinki,ko mahaifinki rika ajiye masa KASET din da ya kunshi wannan sakon A CIKIN MOTA kusa da wurin sa kaset (ba tare da kin gaya masa ba)
• Annabi (SAW) yakan taya matansa aikin gida.
• Me kake so ka zama a nan gaba?
• Kyautatawa danka yana karami,sai ya kyutata maka in ya girma
RIKA AIKAWA DA KAWAYENKI WADANNAN SAKWANNI TA WAYA !!!
Tsoron Allah shi ne tushen nasara a zamantakewar aure da tarbiyyah.
“Kar ku manta da mutuncin dake tsakaninku (Bakara:237 ) .
Namiji da bangaren HAGU na kwakwalwarsa yake tunani, mace kuma na DAMA. Ya za ki amfana da wanan bayanin a zamanki da mijinki?
Zama baiwar mijinki, sai ya zama bawanki
“Idan muslumi ya ciyar da iyalinsa don neman lada a wurin Allah, ta zama sadaka (Bukhari: 5351).
Gangancin yaro kuskure ne.
Wanda ya wahala yana yaro, in ya girma zai huta.
SHIN A SHIRYE KUKE KUWA?
¨ Shin kun shirya tafiya garin da ba dawowa?
¨ Shin kun shirya tafiya gidan da sai an cika jaka a ke zuwa?
¨ Shin kun shirya amsa tambayoyin da basu da iyaka?
¨ Shin kun shirya barin masoyanku?
¨ Shin kun shirya sa fararen kaya wadanda ba dugon baki a jikinsu?
¨ Shin mai kuka tanadarwa bakonku wanda ba zai yi sallama ba in zai shigo?
¨ Shin kun tanadi guzurin tafiya na inda bakon zai kai ku? Wal’ iyazu billah wa inna lillahi wa inna ilaihi raji‘un Wayyo mutuwa! Mutuwa!! Mutuwa!!!
Allah ka sa mu cika da imani
SAUDA M. SANI GGSS Garko
Azumin Arafa Da Sauran Azuman Nafila
An karbo daga Abu Qatada Al-ansari Allah ya yarda dashi ya ce;An tambayi Annabi Muhammad [S.A.W] akan Azumin ranar Arafa,sai yace;”yana kankare zunuban shekara biyu,shekarar da ta wuce da shekarar dake gabarta”.Sai kuma aka tambaye shi akan azumin ashura,sai yace”yana kankare zunuban skakarar da ta wuce”,sannan aka kara tambayar shi akan azumin ranar litinin sai yace;”wannan shine ranar da aka haife ni,ranar da aka turo ni,kuma shine ranar da aka saukar mini da wahayi”
Muslim ne ya rawaito.
Alqasim Ahmad Elnafaty
Muhimmancin Sahur
Cikin abubuwan da mai Azumi ya kamata ya lura da su akwai Sahur don fadin Annabi Muhammad(S.A.W);”kuyi sahur don a cikin sahur akwai Albarka”
Haka zalika Annabi(S.A.W) ya ce [banbancin azuminmu da azumin masu littafi shi ne cin sahur]
masu littain nan sune yahudu da nasara, don sun kasance basa cin sahur,sai dai su ci abinci tun da dare sannan su tashi da azumi da wannan abincin da suka ci
Addu`ar Shan Ruwa
Yana daga cikin sunnah idan Mutum ya zo bude baki yace:”zahabazzama`u wabtallatil uruqu wasabatal ajru insha`allah”
Addu’a makamin mumina
Assalamu Alaikum Warahmatullah
‘Yar uwa a musulunci, hakika Addu’a tana da tasiri a rayuwarmu, musamman mata.
Yar uwata, Addu’a fa karki manta ita kanta ibada ce domin Allah (S.W.T) yace: “ku roke Ni zan amsa muku” suratu gafir.
Don haka duk abin ya same ki ‘yar uwa gaya wa Allah. sai ki sami maganin matsalar ki.
Sannan Annabi (S.A.W) ya ce: (Addu’a makamin mumini ce) kin ga ashe ba ki da wani abin kamawa wanda ya wuce Addu’a.Allah ya sa mu dace Amin.
Asma’u Bukhari Safwan
Me Za ki Iya yi a Minti Daya?
‘Yar uwa musulma, hakika ya kamata ki sani cewa lokaci yana da matukar muhimmanci; bai kamata ki sake ki yi asarar ko da minti daya, ke ko dai dai da sakan daya ba ma ba tare da kin aikata wani abin da zai amfane ki ba a cikin sa.
Na jarraba naga cewa cikin minti daya zaki iya aikata alhairai masu yawa.
Safiya Husain Falaki
Ladubban yin Sulhu Tsakanin Masu Gaba
Gaba tsakanin musulmi babban zunubi ne; domin Allah ya wajabtawa musulmi son juna da kyautata wa juna, shi ya sa gusar da wannan zunubi ta hanyar yin sulhu tsakanin masu gaba ya zamo ibada ce da Allah yake so. Ga wasu ladaddakin wanda ya aikata wannan alheri.
1- Rabauta da rahamar Allah: Allah Ta’ala yana cewa a cikin ma’anar wata aya: ((Hakika muminai ‘yan uwan juna ne ; saboda haka ku sulhunta tsakanin ‘yan uwanku, ku kuma ji tsoron Allah domin ya rahamshe ku)) (Hujurat: 10).
2- Samun soyayyar Allah ; domin duk wanda ya kyautatawa ‘yan uwansa Allah yana son sa kamar yadda ya ce a ma’anar wata aya: ((Ku kyautata, domin kuwa Allah yana son masu kyautawa)). (Bakara: 195). Sulhu kuwa kyautatawa ne ga ‘yan uwa musulmi.
3- Samun ladan yaye wa musulmi matsala da gusar musu da wata cuta ; domin tabbas sabani tsakanin musulmi yana dauke da cutar da su duniya da lahira. Allah ya azarta mu da yi masa biyayya da kuma taimakon bayinsa.
Rabi’atu Aliyu Umar (Umm A’isha).