KARATUN JAMAI’A

       Jami’a tana daya daga cikin wurare da suke ba wa mutum ‘yanci, ma’ana ba mai takura masa, kuma ba a damu da abin da yake yi ba. Amma kuma idan aka duba jami’a wuri ne mai hadarin gaske in dai har mutum bai yi mata da gaske ba. Jami’a mahada ce ta mutune daban-daban, daga wurare daban-daban wadanda tarbiyyarsu da al’adunsu suka bambanta; saboda haka ya kamata dalibai musamman sababbi su lura da wadanda za su zauna tare a matsayin abokai, kawaye ko makamancin haka; don akwai mutane da za su batar da mutum in har bai yi a hankali ba, ko kuma shi bai yi kokarin jawo su zuwa hanya ta daidai ba; domin wasu manufarsu ta shiga jami’a ba wai samun ilimin da suka je nema ba ne, a’a, su dai kawai su sami yadda za su yi su lalata tarbiyyar ‘yan uwansu matasa ne. A yanzu da yawa daga cikin dalibai suna jami’a, amma ba su da wata manufa mai nagarta ta kasancewarsu a cikinta, da za ka tambayi wani dalibin ka ce me zai karanta a jami’a, sai ya ce: Ai komai aka ba shi karantawa zai yi. Abin tambaya a nan shi ne: Shin wai yin jami’ar ne ya zama dole, ko kuwa manufa ce babu! Ya kamata mutane su san cewa yin jami’a ba wai zama dole ya yi ba, sai dai don manufar samun ilimi mai nagarta domin taimakon addini da al’ummar musulmi, musamman saboda kalubalen dake fuskantar musulmi ta fuskoki daban-daban a cikin gida da waje. In aka duba bangaren mata misali, na ha]u da wasu sa’o’ina da ba su sami kyakkyawar shawara akan abin da ya kamata su karanta ba, a cikin ire-iren wadannan dalibai sai ka ga mace ta je ta dauki kamar Civil Engineering; (abin da ya kunshi koyar da yadda ake yin tituna, gadoji, dss). Ko kuma irin su Political Science da makamantansu, ni kuma ina ganin cewa gudunmawar da mace za ta bayar ta irin wad annan kwasa-kwasai ba su dace da dabi’ar ‘ya mace ba. A halin da muke ciki a yau, al’ummarmu tana bukatar mata wa]anda suka kware a fannonin aikin asibiti kamar likitanci, nurse da unguwarzoma da makamantansu; saboda haka ne ma nake da burin karanta aikin likita, kuma nake fatan Allah ya cika min burina, ya taimakamin akan samun nasarar shiga da kwarewa a wannan fannin.

FATIMA HUSAIN FALAKI

Published in:  on April 7, 2009 at 12:34 pm Leave a Comment

Madubin Rayuwar Matasa

‘Yan uwana matasa Ina yi muku fatan alheri da sallama ta muslunci; Assalamu

alaikum. Bayan haka:

Saninmu ne mu matasa cewa akwai mu da son kwaikwayo da daukar salo na wasu fitattu a fagage daban daban, kamar ’yan bal, ’yan fim, makada, da mawaka dss. Amma idan muka tsaya muka yi tunani yadda ya kamata, za mu ga ba mu da taurarin da suka fice matasan magabatanmu na kwarai da suka shude; kamar Annabawa lokacin suna matasa, matasan sahabbai, da na tabi’ai dss. Idan muka dubi irin su Annabi yusuf, Nana Maryam, Nana A’isha, Aliyyu ibn Abi dalib, Ibn Abbas Allah ya yarda da su baki daya za mu ga ba karamar nasara suka ci ba a rayuwarsu, don haka sai mu bi hanyar da suka bi. A fitowa ta gaba in sha Allahu zan ba ku labarin wani matashi daga cikin sahabbai wanda nasarar da ya samu a rayuwarsa ta kai ya zama abokin sirrin manzon Allah (SAW) kuma dan aljanna tun yana duniya.

Khadija Muhammad Kabir Yunus

Published in:  on June 30, 2008 at 7:31 am Leave a Comment

Mahimmancin Lokaci a Rayuwar Matashiya

 Da sunan Allah mai tarin rahama da yawan  jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga mafi daukakar annabawa da manzanni; Annabi Muhammadu (SAW)       

Bayan haka zan yi amfani da wannan kofa domin jan hankalin ‘yan uwana ‘yan mata matasa game mahimmancin lokaci, da kiyaye shi. Ya ‘yar uwa hakika yana da matukar kyau ki san kimar lokacin da Allah (swt) ya tanadar gareki, haka nan  ki san yadda za ki yi tattalinsa; domin ki amfani kanki da al’ummarki da shi ki nemi guzirin tafiya lahira, kar ki zauna ki shantake kina sharholiya, da karance-karance marasa amfani, ko kallon fina-finai,  ko hotuna masu nuna tsiraici, ko tunane-tunane marasa kan-gado, ko maganganu wadanda ba su kamata ba. Wadannan duk ba za su amfane ki da komai ba, sai dai su kara dilmiyar dake a cikin halaka, da jawo miki da-na-sani.

Ki tuna lokaci ba ya jiran kowa.!Yi kokari ki ga kin amfana da lokacin da kike da shi, ki kasance a koda- yaushe cikin

·        Ambaton Allah, da

·        Yin kowace sallah akan lokaci,

·        Yawaita yin Nafilfili,

·        Yawaita karatun Alqur’ani

·        Karanta littatattafai na ilimi da zaki karu,

·        Sauranron kasa-kasai na wa’azi ko lacca wadanda za ki amafana da su duniya da lahira, ·        Yin zikirin safiya da maraice wadanda ake kira (Alma’athurat) da makamantansu.

·        Taya mahaifanki aiki a gida kamar girki, shara, yi wa kanne wanka dssMatukar kin kiyaye wadannan abubuwa, da shauran ayyuka na alheri da ban zayyana ba, ina mai yi miki albishir da in sha Allah za ki kasance cikin rayuwa ta jin dadi da samun biyan bukata, da samun kusanci da Allah (swt) tare da samun yardarsa, da samun karin kaunar iyaye da yardarsu, kuma ki rika jin cewa kina da amfani a wannan rayuwa, ba ‘yar rakiyar zuwa duniya b ace. Don haka sai ki kiyaye, ki guji zaman bata lokaci, ki zauna kurum ba tare da kin yi amfani kanki da wani abu ba; domin wannan shi zai kara jawo miki abin da zai cutar dake, da jawo miki wasu-wasi, da bacin rai da shakka. Saboda haka, nake gargadin ‘yan uwana matasa da su dage da yin addu’a kowane halin da suka sami kansu da su yawaita karanta wannan addu’a: “ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI WA A’UZU BIKA MINAL AJZI WAL KASALI, WA’A UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI,  WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA QAHRIRRIJALI” Idan har kina yawaita karanta wannan addu’a da bibiyar ma’anarta, insha’Allahu,  Allah (s.w.t) zai ya ye miki damuwarki, da bakin ciki, ko bacin rai.

Ya ‘yar uwa ta! Ya kamata a kowane lokaci ki kasance cikin shiri da tanadi domin wannan rana mai zuwa (Alkiyama). Kuma kada ki damu da wani abu na rayuwar duniya wanda ba tabbatacce ba, har ranki ya rinka baci akansa don baki same shi ba kiyi hakuri, hakika Allah yana tare da masu hakuri, kuma lallai babu wani tabbataccen abu sai aikin mutum na kwarai.Allah (s.w.t) yana cewa:  “wanda ya yi aiki na gari daga cikinku, namiji ko mace zamu raya shi rayuwa mai dadi, kuma zamu saka musu da mafi kyon abin da suka aikata”(Suratun-nahli)Allah yasa mu dace Amin

                                                                                                 MARYAM JAMILA MUHAMMAD 

Published in:  on February 7, 2008 at 11:39 pm Leave a Comment

Menene Sirrin NASARATA a karatun Boko?

‘Yan uwana matasa Assalamu alaikum.Ina yi wa Allah Ta’ala godiya bisa ni’momin da ya yi min ba iyaka, wadda daga cikinsu akwai kokari da hazaka a makaranta, har ya zamana bayan saurin fahimtar karatu da nake yi, in dai za a yi jarrabawa, to kuwa in sha Allahu ni ce zan yi ta daya,  sai dai kuma  wani ikon Allah, wannan ya sa nake jin dadin rayuwata ta makarnata, saboda kullum iyayena suna farin-ciki da ni, suna kara sona, sannan ga farin-jini da nake da shi cikin kawaye, saboda wannan hasken na karatu da Allah ya ba ni. 

Wata rana wata kawata ta tambaye ni: “Ke kuwa me ya sa kullum kike sahun gaba wurin fahimtar  karatu, da cin jarrabawa?”

Na yi tunani mai zurfi, sai na ga bayan taufiqi na Allah, da tsayuwar iyayena akaina HADDAR ALQUR’ANI MAI GIRMA tana daga cikin manyan dalilalai na samun wannan gagarumar nasara. Wasu bincike-bincike da aka yi na ilimi a Saudiyya sun nuna cewa daliban da suka samu kula ta musamman game da Alqur’ani tun suna yara, suna bai wa takwarorunsu da ba su samu wannan kulawar ba tazara a fahimtar ilimummuka na zamani, da rata mai tarin yawa a jarrawa.

Sannan na ji an ce Dr. Bashir Galadanci- mai bai wa gwamnan jaharmu shawara akan ilimi da kimiyya- ya ce: tun da yake  bai taba ganin daliban da suka fi alarammomi saurin gane kumfuta ba a cikin daliban da ya taba koyarwa.

Don haka nake bai wa ‘yanuwana matasa musamman mata da su dage da karatun Alqur’ani, da haddace shi, wannan zai kara musu basira da kwakwalwa da nasara a jarrabawa, kamar yadda nake bai wa iyayenmu shawara da su kara dagewa wurin ganin ‘ya’yansu sun samu rabonsu a Kura’ni kafin lokaci ya kure, musamman da yake Koyar da yara karatun Alqur’ani tushe ne babba daga manyan tuwasan musulunci; Ibn Taimiyya Allah ya jikansa ya ce: “Haddar Alqur’ani ita ce abin gabatarwa akan duk wani ilimi”  

Baya ga wannan kuma, ga tarin fa’idojin da haddar Kur’anin ta kunsa kamar:

1.  Samun budi a karatun zamani kamar yadda na fada a baya.

2.  Kasancewar Alqur’ani zai yi ceto ga ma’abotansa ranar Alkiyama kamar yadda manzo (s.a.w) ya ce: “Ku karanta Alqur’ani; domin zai yi ceto ranar alkiyama ga ma’abotansa ” (muslim).

3.  Mahaddacinsa zai sami daukaka a duniya da lahira.

4.  Wanda ya haddace shi zai zama daga cikin zababbun wannan alumma, saboda fadin manzo (s.a.w): “mafificinku shi ne wanda ya koyi karatun Alqur’ani kuma ya koyar da shi” (Bukhari).

5.  Samun lada mai yawa wurin karatunsa, kamar yadda Annabi (s.a.w) ya ce: “wanda ya karanta  harafi daya na Alqur’ani, yana da aikin lada daya, aikin lada daya kuma yana da lada goma ……… ” (Tirmizi)

6.  Iyayen da suka tsaya tsayin daka akan karatun ‘ya ‘yansu na Alqur’ani suna da lada mai yawa da babban sakamako a wurin Allah.

Alqur’ani littafi ne – duk da cewa yana da yawa- amma saukin hadda gareshi; saboda Allah ya sauwake haddarsa kamar yadda ya zo a suratul Qamar, kuma kamar yadda haddar tasa a aikace ta tabbar; don haka ‘yan uwana matasa kada ku yi kasa a gwiwa wurin dukufa wurin haddace Alqur’ani mai girma, musamman a wannan zamanin da haddar tasa ta kara sauki; saboda yaduwar makarantun hadda na zamani, da kuma na’urori daban daban na na kimiyya, kamar irin su kaset da rikoda, kumfuta, wayar salola dss, baya ga makarantun Allo da tsangayoyi da suka dade suna ba da gudun mawa a wannan fage; don haka kada wata ta ce: “Ga bikin zuwa babu zani” sai dai ta ce: “In ba ki yi ba ni wuri“!

A karshe ina godiya ga mahallicina  Allah da ya albarkace ni da haddace littafinsa mai girma, haka nan ina godiya ga makarantar Darul Arqam ta Kano wadda a cikinta ne na samu wannan haske, Allah ya ja zamaninta, ya kara mata daukaka, ya kuma taimaki shuwagabanninta da malamanta, ya kuma saka musu da alheri.

Kamar yadda nake mika godiya ta musamman ga babbar yayata da mijinta wadanda suke matsayin iyayena, don jajircewarsu da kulawarsu, da addu’arsu ne suka sa na samu, hada da tabbatuwar wannan haske na Kur’ani a zuciyata, Allah ya albarkanci rayuwarsu, ya ba su tsawon rai cikin bautar Allah,  koshin lafiya  da alheri, ya kuma saka musu da jannatul Firdausi ranar gobe Kiyama. Amin.

FATIMA HUSAIN FALAKI

Published in:  on February 6, 2008 at 11:21 pm Comments (2)