Da’awa cikin Dabara

‘Yanwana Mata Assalamu alaikum wa rahmatullah.

Bayan haka:

Duk inda musulma take ya kamata ta zama mai afani, mai kokarin isar da sakon Allah a duk inda ta samu kanta, musamman ga makusantata, iyalinta, kawaye, makota, da sauran jama’a.

Akwai hanyoyi da dama na isar da wadannan sakwanni, daya daga ciki ita karkata akalar zance zuwa wani abu da zai amfani masu sauraro.

Yawanci hirar farko da ake bude fage da ita a wurin tarurrukanmu na mata – kamar suna, biki, tariya dss- ita ce take wawashe yawancin lokacin zaman.

Alal misali in hirar wani fim aka fara, sai ki ga ita za’a yi ta yi har zuwa wani lokaci mai tsaho kafin a canza.

Haka nan in hirar “yau” ake; tsadar kayayyaki da shauransu, ko hirar wani anko da ya fito. dss.

‘Yar uwata yi amfani da wannan damar wurin bude fage da abin da zai amfani mutane don ki isar musu da sakon da kike so, amma fa ki yi la’akari da irin mutanen, da kuma irin taron.

Misali: bayan an gaggama gaisawa an huta, sai ki fara jan ta kusa dake da hira…

· “Ke kuwa a ganinki me ya sa yanzu cikin shege yake yawa tsakanin ‘yan mata”?

· “ke kuwa  wace mace ta fi burge ki a duniya”…. Me ya sa…?

·“A ganinki me ya sa yawancin ‘yan wuta mate ne?”

·    “Wa ya ji labarin da aka fada jiya a taskar labarai wata mata ta yi kokarin kashe mijinta…?” me ya sa ku a ganinku irin wannan take faruwa yanzu a cikin al’ummarumu, bayan da ko kusa ko alama ba bu su?”

· “Me ya sa zuwa gurin bokaye da ‘yan duba yake kara yawa ne musamman tsakanin mata?”

·  “Wa yake da masaniya game da kare hakkin kananan yara da ake ta yamadidi akansa?”

·“Ya mace za ta iya sa mijinta ya rika zama a gida?”

Da shauransu

Nan da nan sai ki ga hankalin mutane ya karkata kan abin da kika kawo, ke kuma ta hanyar hira, sai ki shigar musu da sakon da kike son shigarwa.

In kuma abin da kika kawo na tattaunawar bai ba su sha’awa ba, sai ki canza wani.

Fatima MK Yunus (Ummu Ibn Taimiyyah) 

Published in: on February 8, 2008 at 11:38 pm Leave a Comment