Nana Khadija Uwar Muminai

 

Assalamu alaikum. ‘Yan uwana yara  zan ba ku tarihin wata babbar mata cikin iyayen muminai.  Sunanta Khadijah bintu Khuwailid. Ita ce farkon matan Annabi (S A W) Ita ce farkon wadda ta fara muslinta, Ita ce kuma ta haifawa Manzon Allah (S A W) duka ‘ya yansa ban da Ibrahim. ‘Ya’yan nata su ne: 1) Abdallah, 2)Alqasim, 3) Zainab, 4) Rukayya, 5) Ummu kalsum, 6) Fadima. Yanzu ina so wani ko wata ta ba mu tarihin wata Sahabiyar a takaice kamar yadda ni ma na takaita.

Amina M. Muslim.

 

Published in:  on April 18, 2008 at 2:21 pm Leave a Comment

Nana Khadija Uwar Muminai

 

Assalamu alaikum. ‘Yan uwana yara  zan ba ku tarihin wata babbar mata cikin iyayen muminai.  Sunanta Khadijah bintu Khuwailid. Ita ce farkon matan Annabi (S A W) Ita ce farkon wadda ta fara muslinta, Ita ce kuma ta haifawa Manzon Allah (S A W) duka ‘ya yansa ban da Ibrahim. ‘Ya’yan nata su ne: 1) Abdallah, 2)Alqasim, 3) Zainab, 4) Rukayya, 5) Ummu kalsum, 6) Fadima. Yanzu ina so wani ko wata ta ba mu tarihin wata Sahabiyar a takaice kamar yadda ni ma na takaita.

Amina Muhd. Muslim. 

Published in:  on March 31, 2008 at 9:00 am Leave a Comment

Wa zai Canka!?

Mai kokari kawai nake so ya yi Magana.

Af! Assalamu alikum, shekarata takwas, kuma sunan matar Annabi ta farko ne da ni; Khadija, kuma a Madina aka haife ni, kai  Allah na gode maka!

Ga wasu sunaye guda hudu na wasu manyan mutane a musulunci:

1- Abubakar Saddik.

2- Ali bin Abi Talib.

3- Umar Bin Khattab.

4- Usman bin AffanTambayata a nan ita ce:

  •  Su wanene wadannan mutanen? Annabawa ne ko Sahabbai? Ko malaman makaranta?  
  • Menene taken kowanne? 
  • Na Jera wadannan sunayen gwargwadon harufansu na farko, ku kuma ku jera su gwargwadon daraja da kuma zamanin kowanne daga cikinsu. 
  • Hada kokarin bara da na bana ki nemo amsa. Ina jiran ki Wassalamu alaikum.

Kawarku Khadija Muhd. Muslim

Published in:  on February 9, 2008 at 1:29 am Comments (1)

Imamu Shafi’i lokacin yana dan Yaro

Assalmu alaikum abokaina na Najeriya da na Madina,

Kun kuwa san yadda imamush shafi’a yake lokacin yana dan yaro?

To zan gaya muku, amma kafin nan barain fara gaya muku wanene shi ma tukuna IMAM ASSHAFI’I, sunansa (MUHAMMAD BIN IDRIS) Wani babban malami ne da aka Haifa a garin “Gazza”, wanda yake a Kasar “Palastine” -inda a yau yahudawa kullum suke kashe musulmi- a shekara ta (150) bayan hijira, ko da yake iyayensa mutanen Makka ne, kuma ‘yan Kabilar Kuraishawa ne, Kabilar Manzon Allah (s.a.w).

Ya nemi ilimi a wurin malamai masu yawa, a garuruwa daban – daban, musamman Makka da Madina. Daga cikin manyan malamansa da akwai Imamuna Maliku.Iliminsa ya kai ya kawo, ya tumbatsa har ya kafa mazahaba wadda ta zama daya daga cikin manyan mazahabobin Ahlussunnah wal jama’a guda hudu. Ya kuma rubuta littattafai masu yawa. Ga shi da yawan ibada, kullum sai ya yi sallar dare, ga shi da tawalu’u matuka da gaske, ba ya ganin kansa komai! Har Allah ya dauki ransa a shekara ta (204) bayan hijirar Manzon Allah (s.a.w).

Allah ya jikansa ya amfane mu da ilimummukansa.

Imamu shafi’i tun yana dan yaro an ce himma ce da shi kamar me, ga basira da hazaka, ga ladabi da biyayya, duk inda aka aike shi nan da nan zai yi sauri ya dawo, Babarsa tana son sa sosai saboda kirkinsa da kokarinsa. Ni dai Imamush Shafi’i yana burge ni, in sha Allahu sai na zama irinsa, na san kuma kuna so, to sai mu dage, kuma muce baban ninmu su rika yi mana addu’a.

Abdallah Muhd. Muslim (shekara 12).

Published in:  on February 8, 2008 at 3:39 am Leave a Comment

Kawalle ga ‘yan Nasihohi

Assalamu alaikum wa rahmatullahi.Farko dai Ina farin cikin da bude bangare na musamman a wannan shafi mai albarka, wanda zamu dinga haduwa da juna a cikinsa.

Ina yi wa ‘yan uwana yara nasiha wadda za ta amfane su insha Allah:

1-  Kiyaye yin salla a kan lokacinta; domin ita ce babbar ibada bayan kalmar shahada.

2-  Bin iyaye; domin hakkin yana da girma a musulunci, musamman iyaye mata.

3-  Kwazo a dukkanin karatuttuka musamman karatun Al’Kur’ani Mai girma; domin ilimi shi ne hasken rayuwar duniya da lahira. Jahili a cikin duhu yake duhu yake dundum!Wannan shi ne karshen nasihata a yau, sai wata haduwar.

Ma’assalama.

 Amina Muhd. Muslim (Ummi) shekara 10

Published in:  on February 7, 2008 at 12:28 pm Leave a Comment

Ni dai kullum na yi sallah sai na yi wa IYAYENA addu’a

‘Yanuwana yara Assalamu alaikum Sunana Usaidu, shekarata goma da rabi, ina karatu a makarantar Darul Arqam a Kano.

‘Yan uwana yara nasihata gareku ita ce: Mu sani cewa, bin iyaye wajibi ne, Saboda Allah da manzonsa sun yi umarni da a bi iyaye.

Iyaye su ne sababin zuwan mutum duniya. Sun sha wahala wurin rainonsa, su ne kuma suke daukar  dawainiyar dinka masa kaya, ba shi abinci da abin sha. To ashe kenan duk wanda bai bi iyayensa ba ya yi asara a duniya da lahira. 

Don haka ‘yan uwana yara; nasihata garemu ita ce:

  • Mu bi iyayenmu, Mu kyautata musu,
  • Kada  mu saba musu,
  • Kada mu ki jin maganarsu,
  • Kada mu ki zuwa aikensu.

Ni dai kullum idan na yi sallah sai na yi musu addu’a. Kuma ‘yan uwana yara ku rika yin haka.

Abokinku Usaidu Muhd. Babangida  

Published in:  on February 2, 2008 at 3:16 pm Leave a Comment