Kananan Hukumomi Albishirinku

 

A irin marka-markar da ofishin “A1 Nana” yake tsalawa a fagen tarbiyya, zamantakewar aure, da abubuwan da suka shafi mata, mamakon alheransa ya fara shatata a kananan hukumomin Jihar Kano (44) ta hanyar wani kwarya-kwaryar shiri da ofishin mai bai wa mai girma  gwamna shawara akan ayyuka na musamman (bangaren mata) ya shirya.  

A wata zantawa da Mujallar iyali ta yi da shugabar wannan ofis  Haj. Mariya Sanusi Mahdi game da manufofin wannan shiri, da kuma abin suka yanke shawarar hada-kai da ofishin “A1 nana” don gudanar da wannan aiki, sai ta ce: Babbar manufar wannan shiri agazawa iyaye mata wurin inganta rayuwarsu ta aure, da taimaka musu wurin tarbiyyar ’ya’yansu, da kuma sa su a hanya  wurin neman na-kansu.

 

Game da abin da ya sa suka zabi su yi taimakekeniya da “A1 nana cewa ta yi: Mun yanke wannan shawara ne saboda, wannan ofis-A1 nana- ya yi fuce da nagartattun tsare-tsare, kyawawan manfofi, hanyoyin zartarwa masu tasiri da ban sha’awa, da aiki tukuru, ga kuma matukar burin da yake da shi na tallafawa mata mazauna karkara, da dai wasu tsare-tsare masu kayatarwa. Kuma ya yi mun gani.

Shi kuwa shugaban ruko na ofishin “A1 nana” Eng. Bashir Adamu Aliyu nuna farin-cikinsa ya yi game da wannan goron gayyata, ya kuma yi alkawarin in sha Allahu kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Da Mujallar iyali ta tuntube shi akan tanadin da ofishinsa ya yi gameda  wannan  shiri sai ya ce: Za mu fitar da cikakken bayani akan haka nan gaba,  amma dai za mu fi mayar da hankali ne akan: 

TARBIYYA: (Muhimmacinta fa’idojinta, hanyoyi, da dabarun yinta, kurakuren da suke aukuwa a cikinta, da hanyoyin magancesu 

ZAMANTAKEWA (Shawarwari ga iyaye danganeda auren `ya`yansu – zabi, nema, kayan aure da biki da tariya– Rayuwar iyali mafificiya -Hakkokin ma`aurata, zaman lafiya da taimakekeniya da sadaukarwa a rayuwar aure- Mace-macen aure-yawaitarsa, illolinsa, abubuwan da suke kawo shi da magungunansu)

SANA’O’I: koyar da wadannan sana’o’i (sabulun wanka, man shafawa, abincin jarirai, da maganin kwari). 

 

Published in: on April 5, 2008 at 2:04 pm Leave a Comment

Kwas na musamman don ‘yan mata

Bangaren matasa da ‘yan mata na wadannan cibiyoyi masu albarka (A1 families da Nana Asma’u Women Center), ya gabatar da kwas na matasa ‘yan mata (Teenage Program) na farko wanda a ka gudanar  daga ranar 30/12/2007 zuwa 01/01/2008.

snapshot03.jpeg  snapshot02.jpeg  snapshot07.jpeg

Manufofin wannan shiri

  • Samar da mata na gari masu imani da Allah da riko da koyarwar addininsu tare da wayewa ta zamani don gyaran al’umma.
  • Sanya ‘yammata a hanyar zama kwararru akan duk abubuwan da suka shafi mata a addininsu da rayuwarsu ta yau da kullum.
  • Dasa tushen samar da rayuwar iyali ingatacciya, ta buga misali.
  • Taimakawa iyaye wajen tarbiyyar ‘ya’yansu da gano irin abubuwan da suka dace da ‘ya’yan don karfafarsu a kai.
  • Gano da kokarin shawo kan matsalolin tarbiyya, alakar ‘ya’ya da iyayensu, da zamantakewar aure tun kafin su bayyana.
  • Samar da bincike da rubuce rubuce a kan hanyoyin tarbiyya da kura-kuran da ke afkuwa cikinta don magance matsalolin da su ke haifarwa a al’umma.

Abubuwan da shirin ya kunsa:

 Shirin ya kunshi laccoci da wasannin kwaikwayo (da harshen Larabci) da kacici-kacici (da harshen Hausa) da kuma mahawara (da harshen Turanci) baya ga horo na musamman a kan amfani da kwamfuta.

Shirin, wanda Mai bawa gwamna shawara a harkar mata, Hajiya Mariya Sanusi Mahadi ta bude, ya samu halartar ‘yan mata sama da 60 kuma dalibai na farko da wadannan cibiyoyi suka fara horaswa (trainers) ne suka gabatar da wannan kwas din gaba dayansa.  

Laccocin da aka gabatar, sun hada da:

  • Kissoshin Magabata Mata – Asma’u Bukhari Safwan,
  • Kula da kai (ko Tsaftar Jiki) – Binta Imam,
  • Lokacin balaga – Hassana Sani Darma,
  • Alaka da maza da Suturar ‘ya mace – Fatima Isma’il,
  • Abubuwa biyar kafin biyar – Hauwa Uba Sa’id
  • Abubuwan da Musulunci ke nema daga Matasa – Jameela Abdul Azeez
  • Jinin Haila da hukunce-hukuncensa – Sadiya Adamu Aliyu

Daga cikin muhimman abubuwan da shirin ya yi akwai jin ra’ayoyi, shawarwari da korafe-korafen yaran da suka shiga shirin da nufin samar da hanyoyin magance su.

Idan a ka ci gaba da bibiyar wannan fili za a samu karin bayani da kuma sakamakon wannan bincike da aka gudanar.

Da yardar Allah, nan gaba kadan, za mu gudanar da wani shiri na musamman don horas da iyayen wadannan yara da sauran iyaye game da hanyoyin tarbiyyar matasa da kuma sanar da su irin abubuwan da ‘ya’yansu ke korafi a kan su domin daukar matakan da su ka dace. 

A karshen wannan kwas din, an rarrabawa matasan kyaututtuka na littattafai, man shafawa, turare, man goge kaushi da sauransu.

Published in: on February 9, 2008 at 1:25 am Leave a Comment