ALLAH YA GAFARTA WA WANCE !!!

Imamu Ahmad (Allah ya ji kansa) bai yi auren fari ba sai da ya kai shekara arba’in; da ya tashi aure sai ya fara tantance gidan da ya kamata ya hada zuriya da su, sai aka ce masa akwai ‘yan mata biyu a gidan, daya kyakkyawa ce, dayar kuma idonta daya, sai ya ce wacce ta fi hankali? sai aka ce mai ido dayan, sai ya ce: ita za ku aura min. Zamansu ya yi dadi sosai. Bai yi wani auren ba sai da ta rasu.

 Yake cewa: Almarwazi daya daga cikin daliban imamu Ahmad (Allah ya ji kansa) ya ce: wata rana imamu Ahmad ya ambaci iyalinsa bayan ta rasu sai ya ce: Allah ya gafarta wa wance, shekararmu ashirin tare amma ko sabani ba mu taba ba.

 

Published in: on March 27, 2009 at 8:24 pm Leave a Comment

Tarihin Malam Karami (Ibarahim Abubakar Ramadan

Marigayi Sheikh Ibrahim Abubakar Ramadan (Malam karami)  warin masaki ne da ba shi da akokin burmi a fagen da Allah ta’ala Ya yi masa fatahi a kai; shi ya sa rasuwarsa ta zama babbar asara ba ga jihar Kano kawai ba, har ma da  Nigeria baki daya.

Cibiyoyin “A1 Families” da “Nana Asma’u Women Center” na isar da sakon ta’aziyyarsu   ga daukacin al’ummar musulmi musamman mutanen Jihar Kano, tun ma ba matasa da makaranta Alkur’ani ba daga cikinsu bisa wannan babban rashi na  rasuwar wannan bijimin malami makaranci; Allah Ya jikan sa da rahama, Ya amfani bayansa, Ya albarkanci zuriyarsa, Ya kuma yi masa tukwici da gidan Aljannar Firdausi sakamakon gagarumar gudunmawar da ya bai wa al’ummar Annabi (SAW) a rayuwarsa.

Dole ne  wadannan cibiyoyi guda biyu su  ji rasuwar wannan malami radau a jikinsu, saboda baya ga gamammen amfaninsa  da alherinsa ga jama’a, yana ba da  hamshakiyar gudunmawa a fagagen da suka sare wa sanda, wato abin da ya shafi Tarbiyya, Matasa, (maza da mata) da  Zamantakewar aure.  

Allah ne kadai Ya san yawan samari da ‘yan matan da suka samu alherin duniya kafin na lahira, suka samu daukaka, suka kara daraja, kuma suka samu  garkuwa da  Alkur’ani mai girma ta hanyar wannan bawan Allah.

Bugu da kari, yawan gidajen da suke dundum a da, amma suka haskaka tangararan da lantarkin Alkur’ani ta hanyar karantarwarsa a cikin Kano da kewaye su ma Allah ya yi yawa da su. Don haka wadannan cibiyoyi suka dauki nemo hada da buga tarihin wannan malami a matsayin bashi ne a kansu da ya wabaja su sauke shi, don haka suka  tuntubi Dr. Muslim daya daga cikin fitattun  dalibansa, don ya rubuta mana tarihinsa  a takaice. Allah ya saka masa da alheri. Ga abin da yake cewa:        

A shekarar 1986 na sami labarin wata sabuwar makaranta mai wani sabon zubi a karatun Al’kur’ani da ta bayyana a cikin garinmu Kano. Babana ne ya ba ni labarinta, ya kuma neme ni da in je in ga yadda take, ina zaton ma shi ne ya kai ni da kansa, ya kuma ara mini Alkur’ani bugun misira/sharkiyya (kamar yadda muke cewa a lokacin). Abin da nake iya tunawa a lokacin shi ne na je ina labe – labe domin kwarjinin mutanen, tun da ni lokacin ina karami, a shekarar ne na gama primary, amma sai na ga samari da ‘yan mata suna ta shige da fice da cikakken ‘yancinsu a makarantar, su ne ma suka cika ta, suna ta nishadi da gogoriyo a tsakaninsu wurin kwarewa wannan sabon ilimi na tajwidi da gyaran karatun littafin Allah Mai girma. Ba dai kamar gidan Asim da Ibn Amir, sai kuma gidan Khadijatul Kubra da Su Hafsa (R.A) dss. Wannan ya sa ni ma na saki jikina na shiga wannan takara ta alheri daga gidan Ibn Amirinis Shami. Haka muka zauna da wannan dattijon alheri, muka kurbi wasu ‘yan kofuna daga cikin tekun iliminsa na Alkur’ani da tarbiyyar da ya   kware wajen bayar da ita ga matasa; samari da ‘yan mata har ma da iyayensu. Wannan salo nasa da ya kamata a yi nazarinsa domin a kwafe shi, a dabbaka shi a cikin tarbiyyar manyan gobe. Wannan makaranta ita ce irinta ta farko a duka fadin kasar Najeriya iya sanina.  A lokacin akan sami malaman da suke karantar da Alkur’ani da tajwidi gwargwadon hali kuma a gargajiyance, an kuma samu wadanda suka karanto shi a kasashen larabawa ko larabawan suka zo suka koya musu, kuma suke kokarin koyawa almajiran da ke kusa da su. 

Amma a ce an bude kofar wani majalisi ga kowa da kowa, kuma mutane su yi tururuwa suna dannowa, tun ana lissafa ‘yan majalisin da gomomi har aka kai ]aruruwa kai har aka tafi dubbai to babu wanda ya yi wannan jan idon sai wannan bajimi.

Duk wanda ya san Kano a wadancan shekaru ya san ma’anar “jan ido” a wannan maganar. Haka wannan majalisi ya juye ya zama makaranta ginanniya, wadda ita ce irinta ta farko a Najeriya, saboda mahimmancin samari a wurin Malaminmu Allah Ya jikansa sai ya rada mata suna: “Shababul kur’anil Murattal”, wato “Matasa masu ingataccen karatun Alkur’ani”. Wannan shi ya sa da aka fara karantar da tajawidi a makarantun gwamnati shi ne shugaba na wannan bangaren na farko a cikin garin Kano a S.A.S, kafin bangaren ya juye ya zama makarantar gwamnati mai zaman kanta  kuma ya zama shugabanta na farko. Masu Magana suna cewa: “Juma’a da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta”. Bari mu kalli larabar Malam, tun da dai ga Juma’arsa ta yi kyau!

            Malam ya koyar a makarantun gwamnati na boko da na Arabiyya, kamar Aminu Kano commercial college, W.T.C, ta ‘yan mata, Aliya shahuci, S.A.S, sannan Abdullahi Bayero Tahfeez, wadda aka cire ta daga S.A.S, sannan makarantarsa da ya kafa ita ma: Sheikh Ramadhan Secondary School. dss.

A wannan gogayya ta aiki ya karantar da dalibai masu tarin yawa, wanda ba za su lissafu ba. Daga cikinsu akwai gwamnan Kano na yanzu, Mal. Ibrahim Shekarau, da irin su Secretary na hukumar alhazai na yanzu: Alh. Sani Lawan Kofar mata. A bangaren karatun Alkur’ani da na addini kuwa, ya gina manyan malaman Alkur’ani: irin su dan uwansa: Alh. Abdul kadir Abubakar Ramadhan, Mal. Auwal Shawish, Marigayi, mal. Abubakar Ibrahim Adam, mal. Tijjani Tanko, dansa mal. Mujtaba I. Ramadhan.

Haka akwai irin su Eng. Abdus Samad Isma’il, mal. Mukhtari Kunti, da wannan dan tsugulutun almajirin nan mai wannan kasida; Muslim Ibrahim, da su mal. Nura Abdullahi (Babban Editan mujallar Iyali), ga irinsu iyalinsa mal. Maryam Bashir, Mal. Batulu Isma’il,  Mal. A’isha Rabi’u, da ire – irensu tuli. Kai kusan – a birnin Kano har ma da kewayenta – duk inda ka sami makarantar Alkur’ani tsarekunmu ‘yan shekaru talatin zuwa arba’in, in sun kai mutum biyar, to in sha’Allahu za ka ga uku ko ma sama da haka  dalibansa ne, ko daliban dalibansa. Abin kuma bai tsaya a Kano ba kawai; domin   dalibansa sun yadu a fadin tarayyar Najeriya don yada wanan karatu, har sai da ya game gabashinta da yammancinta … ta yi rassa da ba wanda yake da hakikanin adadinsu” sai Allah.

Daga ayyukan Malam ban da wadanda suka gabata:

Yana fassarar Alkur’ani a masallacinsa makarantarsa ta “Shababu” a ko wacce rana, hakan nan a watan Ramadan, sannan yana da darussa a lokuta daban – daban.

Tafsirin azumi a gidan gwamnatin jihar Kano

Shi ne limamin juma’a a masallacin Juma’a na Sharada tsawon shekara 12 .

Alkalancin  musabakar karatun Al-kur’ani ta Jiha da ta kasa kimanin shekara goma sha biyar kuma shi ne malami na farko daga yammacin Afrika da ya yi alkalancin musabakar            Al-kur’ani ta duniya a kasar Masar . 

 

Shugabancin hukumar jin dadin al-hazai ta jihar Kano a shekarar 2005 har zuwa lokacin da  Allah ya karbi ransa a shekarar 2008. Kafinnan ma kuma ya yi aiki a cikinta.

“HALAYENSA: Wanna Shehi ya kasance mutum mai kan-kan da kai, mai saukin mu’amala, mai dadin zama, mai kyawun halaye, mai yawan kakaci (Sakin Fuska)”. Malam yana karbar gaskiya daga duk inda ya same ta, yana abota da duk wanda ya

fuskanci Allah ne a gabansa daga cikin malaman Addini da sauran manyan mutane, kuma daga kowane bangare na fahimtar addini suke, shi dan kadiriyya ne, amma yana tafiya tare da ‘yan Tijjaniyya, da ‘yan Ahlus sunnah, da sauransu. Malam bai san ta’assubanci ba, wato rikon kankamo da ra’ayi, mutu ka raba, a’a shi Malam ina da dalili ne, ina da Masalahar al’umma ne. Shi ya sa za ka iya zama da shi lokaci mai tsawo ba ka san yana darika kaza  ba sai dai an gaya maka. Malam ya kai matuka a hakuri, yana da juriya da shanye wautar masu wauta, wadanda ba su san matsayinsa da darajarsa ba, ballantana na gida.

.5) Malam ya yi wallafe – wallafe na ilimummuka, na san daya – na ma taba mallakarsa da jimawa – ina tuna yana Magana ne kan sifat ko makharijil Huruf, sunansa dai: “Nibrasus Sair”. Kuma Malam ya ba ni labarin wasu wadanda ya yi a wasu mas’aloli na hukunce – hukunce, amma dai a sanina duka bai buga su ba, in ban da wancan da na fada da farko. Allah Ya datar da magadansa su fito da su ga al’umma domin a amfana shi ma ya amfana.

6) Malam ya tarbiyyantar da matasan wannan al’umma ta Kano tarbiyyar da akwai karancin a samu wani mutum ko wata cibiya ta karatu ko ta tarbiyya da ta yi irinsa in ma har an samu, saboda halayensa da dabi’unsa da salonsa na musamman da Allah ya ba shi, shi kuma ya kyautata amfani da su a wannan fage na alheri.

ILIMINSA: Allah Ya hore wannan dan tahaliki ilimin Alkur’ani, karatunsa, gyaransa, tafsirinsa, da sauransu. Komai na Malam sai ya rina shi da rinin Al’kur’ani. Ya haddatar da mutane Alkur’ani barkatai bila adadin, ya kara wa matasa samari da ‘yan mata farashi ta wannan hanyar abinda ba zai kiyastu ba. Bayan wannan Malami ya san yaren larabci, bai je waje karatu ba, amma ba ya fargabar yin larabci tare da larabawa. Malam yana bincike mai zurfi a mas’alolin fikihu da sabanin mazhabobi, haka nan sabanin akidoji. Ya kasance yana rubutu a wadannan matsaloli a farko – farkon malantakarsa. Malam ya kware a ilimin gadon gidansu: ilmul Falak da Hisabi da dangoginsa. Allah kuma Ya yi masa baiwar rubutun hannu, in ya tsantsara rubutun larabci sai ka rantse inji ne ya buga.

Bazan iya karewa ba, sai dai saboda yadda Allah ya yi dabi’ar rayuwa, komai ya yi farko dole ya yi karshe. Kamar yadda Allah Ya nuna mana wannan karo, yadda muna zaman – zaman mu a Madina muna sa ran Malam zai zo – kamar yadda aka saba – tare da tawagar ma’aikatansa na hukumar alhazai, kwatsam sai aka ce mana Malam wai “Ya rasu!!! ranar litinin 2/6/2008 wanda ya yi daidai da 27/jumada Sani/ 1429 AH”. Ya rasu ya bar “‘yaya 36 tare da matan Aure Hudu, kuma yana da Jika 52″. Malam ya rasu bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi, ya yi jinyar sati uku a wani asibiti a Jamus. Ya rasu yana da shekara sittin da hudu (64).

Babu abin da za mu ce sai dai Inna lillahi wa inna ilaihi Raji’un, Allah ne ya ba mu aronsa, kuma shi ya dauki abinsa, zuwa ga rahamarsa da yalwar falalarsa in sha Allah, Allah ya ba mu hakuri da mu da ‘ya’yan cikinsa da matansa da danginsa da sauran almajirai da masoya da al’ummar da ta tafka rashinsa.

Muna yi wa Allah kyakkyawan zaton ba zai tozarta wannan hamshakin aiki da ya gabatar ba, musamman ma mun fara ganin alamu ; tun da ranar laraba 11th June, dansa wanda ya yi digiri a karatun Alkur’ani a jami’armu ta Madina garin Manzo, wato dan uwa Malam Mujtaba, ya dasa daga inda Marigayin ya tsaya a Makarantar samarin Alkur’ani. Allah ya sanya wannan makaranta ta zama sadaka jariya a gare shi.

‘yan uwa sai a zage a yi tanaji domin irin wannan ranar. Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.

Fadakarwa: A wannan tarjama na karu sosai da tarjamar da dan uwa Muhammad Abubakar Ibrahim ya rubuta, kuma ya turo min bayan na nema ta hanyar M. Mujtaba, da kuma dan abinda na iya tunawa daga wata doguwa kuma daukakkiyar hira da M. Nura Abdullahi (Edita) ya taba yi da Malam a gabana, duka Allah Ya saka musu da alheri. Sai kuma abin da yau da gobe na tsinta a wurin Marigayi ko waninsa.

Muhammad Muslim Ibrahim

Abu Abdallah, Madina

Published in: on October 31, 2008 at 6:48 pm Leave a Comment

MAGANIN SAURO

Wata rana an yi wani tsoho wai shi barau,rannan zai yi barci sai ya fesa maganin sauro a dakinsa,da ya tabbatar maganin ya kashe sauron, sai ya kwanta,to yana cikin barci sai wani rigimammen sauro ya zo yana mai kuka a kunne.sai yace a ransa;[wannan sauron sai na yi maganinshi]. sai ya dauko maganin ya fesa a kunnensa, yace na dai yi maganinka.

Kaga wata shiririta a wajen dan tsoho,wannan fesa maganin da yayi a kunnensa shi yasa aka bashi gado a asibiti na kwana biyu har da  karin ruwa

Published in: on September 19, 2008 at 4:37 pm Leave a Comment

Tona asirin Iyali

Wani bawan Allah daga cikin nagartattun bayin da suka shude yayi nufin sakin matarsa,sai wasu suka je suka tambaye shi “kai kuwa mai yasa za ka sake ta? sai yace “mai hankali baya tona asirin matarsa!” bayan ya sake ta, sai suka kuma zuwa suka tambaye shi cewa mai yasa ya sake ta? sai yace,”mai ya hadani da matar wani!”

Published in: on September 5, 2008 at 4:38 pm Leave a Comment

Wasiyyar Qais Ass’ady (R.A) ga ‘ya’yansa

Lokacin da  Qais ibn Asim Assa’dy (RA) -daya daga cikin Sahabbai– yake cutar ajali, ya tara  ‘ya’yansa  ya ce musu: “Ku yi  aiki da abin  da zan gaya muku; don ba wanda za ku yi aki da maganarsa da ya fi ni son ya gaya muku abin da zai amfane ku. Idan  na cika kada ku yi min kururwa; don na ji Annabi (SAW) yana hana a yi wa mamaci ihu,  kuma shi ma da ya rasu ba’a yi masa ihu ba, ku yi min likkafani da kayan da nake sallah da su, ku shugabantar da manyanku … ku nemi na-kanku, don ku wadatu daga mutane, ba ku ba maula; don maula ita ce hanya mafi kaskanci da mutum zai bi don samun na abinci…”   

 

 

Published in: on May 21, 2008 at 2:02 pm Leave a Comment

Gidan Annabi (SAW)

Anas dan Malik  (RA)  ya ce: Annabi (SAW) yana daga cikin mutanen da suka fi kowa kyawun hali, wata rana sai ya aike wata bukata, sai na ce WALLAHI BA ZA NI BA! Amma a raina ina da niyyar zuwa, sai na je na hadu da yara a kasuwa muka yi ta wasa, ban ankara ba sai na ji Annabi (SAW) ya danke ni ta keyya, da na waiwaya sai na ga yana dariya! Yana cewa “Kai dan Anas kama hanya ka tafi inda na aike ka” sai na ce masa to manzon Allah bara in tafi. Ya ce shekarata (10) ina yi masa aike aike bai taba ce min don me ka yi kaza, ko ba ka yi kaza ba (Muslim

Published in: on March 26, 2008 at 10:57 am Leave a Comment

Gidan su Abu Huraira

Abu Hurairah (RA) Duk lokacin da zai fita, ko ya dawo gida, sai ya je bakin kofar dakin mahaifiyarsa ya ce: “BABATA Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Sai ta ce: “Wa alaikumus Salam wa rahmatullahi wa barakatuhu DANA” Sai ya kuma cewa: “Allah Ya rahamshe ki; saboda tarbiyyar da kika yi min ina karami, ita kuma sai ta ce: “Kai ma Allah Ya rahamshe ka, ya saka maka da alheri, ya kuma yarda da kai; saboda biyayyar da kake min bayan ka girma” Daga cikin biyayyar da ya yi mata bayan ya girma: Akwai: 1- Rokon Annabi (SAW) da ya yi, kan ya yi mata addu’a ta musulunta, ya yi mata, kuma ta musuluntar. 2- Shi yake jigilar kai ta, da dakko ta daga ban daki; da yake makauniya ce. Bai je haji ba har ta rasu.

Published in: on March 20, 2008 at 6:44 pm Leave a Comment

“Me ya hada ni da Matar wani!”

Wani bawan Allah daga cikin nagartattun bayin da suka shude ya saki matarsa, kafin ta gama idda sai wasu suka zo takanas suka tambaye shi Me ya hada ku da wance ne har ka sake ta?

Sai ya ce: “

Mai hankali ba ya tona asirin matarsa”

Bayan ta gama iddar-ke nan ta fita daga hannunsa- sai suka kuma yi masa waccan tambayar dai, sai ya ce:

“Me ya hada ni da matar wani!”

Me ake koya a wannan kissa?

Published in: on February 9, 2008 at 12:46 pm Leave a Comment

Tukwicin Annabi ga dan Abbas

Wata rana Abdullahi ibn Abbas yana gidan kanwar mahaifiyarsa, kuma matar Annabi, wato Nana Maimuna, sai ya zuba wa Annabi ruwan alwala a buta, sai ya ce wanene ya zuba min ruwan Alwala, sai ta ce dan ‘yata ne Abdullahi, sai ya doki kafadarsa ya ce “Ya Allah ka fahimtar da shi addini ka sanar da shi Ta’awili.

Me ake koys s wanna kissar?

Published in: on February 3, 2008 at 6:11 pm Leave a Comment