HUKUNCIN KORAR YARO DAGA MASALLACI !!!

Tambaya:    Menene hukuncin korar YARO daga masallaci, ko daga sahun farko don BABBA ya maye gurbinsa? **   

                                                                                         Ba Suna

 Amsa:   Idan yaro ba ya cutar da kowa – da aikinsa ko maganarsa to bai halarta a fitar da shi daga masallaci, ko a dawo da shi sahun da yake baya da wanda yake tsaye a cikinsa ba, koda kuwa a bayan liman yake kai tsaye; saboda a sunna wanda ya fara zuwa wuri shi ya fi cancanta da shi, kuma Annabi (SAW) ya hana mutum ya tashi danuwansa daga wurinsa shi don ya zauna a wurin, masallatai kuma gidajen Allah ne, bayin Allah (baba da yaro) daya suke a cikinsu. Hadisin da Annabi (SAW) yake cewa “Masu hankalin cikinku ya zama su suke biye da ni a sahu” kuwa ba ya nuna a rika korar yara daga sahun farko koda daga su sai liman kamar yadda wasu malamai suka dauka. Wannan hadisi yana kwadaitar da manyan ne kan su je masallaci da wuri don su samu tsayawa a bayan liman. Sannan korar su daga sahun da suke zuwa na baya zai haifar da matsaloli kamar: Taruwarsu a wuri guda wanda wannan zai sa su yi ta wasa da hayaniya lokacin sallah Za su rika kin Masallaci Za su rika in masallata, musamman mai korar su.

Shiekh Ibn Uthaimin

Published in:  on March 21, 2009 at 12:10 pm Leave a Comment

Hukuncin karin gashi

Tambaya: Mene ne matsayin aske gashin kai ga mace ba tare da dalili ba? Kuma menene hukuncin karin gashi?

Maryam Husain Falaki

 Amsa: Gashi ado ne ga mace da Allah (SWT) ya ba ta, hukuncin aske  gashi ga mace na da halaye guda uku: 1-Ta aske shi saboda wata masifa ta faru a gareta kamar mutuwa da waninta, wannan haramun ne; domin Annabi (SAW) ya ce: ba shi ba matar da take aikata haka, kamar yadda Imam Bukhari da Imam Muslim suka rawaito daga hadisin Abu Musa Al’ash’ari Allah ya yarda da shi. 2-Ta aske shi domin wata larura kamar rashin lafiya. A wannan hali tana da dammar yin haka, babu komai a anta. 3-Ta aske shi ba tare da wata larura ba, mafi yawan malamai suna ganin cewa wannan laifi ne, ba ya halatta, domin canza kama ne. Gameda matsayin karin gashi a musulunci kuwa? Amsa ita ce: Baya halatta ga mace ta kara gashinta. babu bambanci wurin haramci tsakanin gashin mutum da waninsa, ya tabbata a cikin hadisai da dama Annabi (SAW) ya la’anci mace mai kara gashinta. Allah Shi ne mafi sani.  

 

 

Dr. Muhd. A. Abubakar

 

Published in:  on May 20, 2008 at 2:33 pm Leave a Comment

Tambaya 0004

Tambaya: Mene ne matsayin aske gashin kai ga mace ba tare da dalili ba? Kuma menene hukuncin }arin gashi?

**Maryam Husain Falaki

 Amsa: Gashi ado ne ga mace da Allah (SWT) ya ba ta, hukuncin aske gashi ga mace na da halaye guda uku:

1-Ta aske shi saboda wata masifa ta faru a gareta kamar mutuwa da waninta, wannan haramun ne; domin Annabi (SAW) ya ce: ba shi ba matar da take aikata haka, kamar yadda Imam Bukhari da Imam Muslim suka rawaito daga hadisin Abu Musa Al’ash’ari Allah ya yarda da shi.

2-Ta aske shi domin wata larura kamar rashin lafiya. A wannan hali tana da damar yin haka, babu mai a kanta.

3-Ta aske shi ba tare da wata larura ba, mafi yawan malamai suna ganin cewa wannan laifi ne, ba ya halatta, domin canza kama ne. Gameda matsayin }arin gashi a musulunci kuwa? Amsa ita ce: Baya halatta ga mace ta }ara gashinta. babu bambanci wurin haramci tsakanin gashin mutum da waninsa, ya tabbata a cikin hadisai da dama Annabi (SAW) ya la’anci mace mai }ara gashinta.

 Allah Shi ne mafi sani.

 Dr. Muhd. A. Abubakar

 

Published in:  on May 3, 2008 at 10:05 pm Leave a Comment

Tambaya 0003

 

Tambaya:

Mace ce mijinta ya ba ta  maganin zubar da ciki ba ta sani ba,  kuma cikin nata ya zube. Don Allah malam: Menene hukuncin wannan miji, kuma menene hukuncin aurensa da wannan matar, kza’a iya cewa ya yi kisan kai,  wane  mataki ya kamata ta dauka, kuma menene hukuncin zubar da ciki a musulunci?

Maryam Usman

BISMILLAHIR     RAHMANIR         RAHIM

Alhamdulillah, Wassalatu Wassalamu ala Rasulillah, Wa ba’adu:

‘Ya’ya ni’ima ce daga Allah Subhanahu Wata’ala. Annabawa da bayin Allah na kwarai sun roki Allah da ya ba su’ ya’ya. Kashe yaya don jin tsoron talauci ko kunya, ko wahalar reno al’ada ce ta jahiliyya; sawa’un jahiliyyar zamanin yanzu ko ta da.In har kana son sanin girmar ni’imar da Allah ya yi maka ta ‘ya’ya, ka tambayi wanda ko wadda ba’a taba yi masa haihuwa ba.

Danganeda tambayoyinki kuma:

1. Ina hukuncin mijin da ya bai wa matarsa maganin zubar da ciki, sai ta sha ba tare da saninta ba, kuma cikin ya zube? Amsa: Zubar da ciki a kowane mataki yake; (watannin farko, tsakiya, ko karshe) – ba tare da wata larurar da shari’a ta yarda da ita ba – ya haramta a zance mafi inganci na malamai, sawa’un wanda ya yi sanadin zubar da cikin daya daga cikin iyayen dan ne ko waninsu.

2. Menene hukuncin aurensu? Amsa: Aurensu ya na nan daram.

3. Shin za’a dauka ya yi kisan kai? Amsa: Ya dogara bisa ga halin da aka zubar da cikin; idan cikin ya kai wata hudu ko sama da haka, to za’a iya cewa ya yi kisan kai, tun da yaro a wannan lokaci ya na da rai, kamar yadda ya zo a Hadisi na hudu na Arba’una Hadis.In kuma cikin bai kai wata hudu ba, to ya yi babban laifi, amma ba za a ce ya kashe rai ba, don kuwa a wannan hali yaro ba’a hura masa rai ba.

4. Wane mataki ya kamata ta dauka? Amsa: Ita dai ba ta yi laifi ba, tun da dai ta yi shi ne bisa rashin sani. kamata ya yi kuma ta yi wa mijinta nasiha da ya tsoraci Allah, ya yawaita istigfari da ayyuka na gari. Ita kuma nan gaba sai ta sa hankali, kar ta sha wani magani ba tare da shawarar likita ba. Allah ya kiyaye na gaba.

5. Menene hukuncin zubar da ciki a musulunci? Amsa: Hukuncin zubar da ciki a musulunci haramun ne; sawa’un sabon ciki ne, ko tsoho. Amma in akwai wata larurar da shari’a ta gamsu da ita, to ana iya zubar da ciki. Alal misali: Bakin likitoci ya zo daya akan cewa; in ba’a zubar da cikin nan ba, uwar tana iya rasa ranta, ko za ta jirkata, ko wani abu mai kama da haka, a irin wannan halin, ya zama dole a zubar da cikin don a ceci ran uwar. Wallahu A’alam.

Dr. Bashir ibn Imam Ali       

 

Published in:  on April 16, 2008 at 12:31 pm Leave a Comment

Tambaya ta 0002

 Tambaya: Menene matsayin kaffarar wanda ya yi rantsuwa, da ya tashi kaffara ya yi azumi, ba tare da duba abubuwanda aka ce ya yi kafin azumi ba?                                 Maryam Husaini Falaki

***

Amsa: Kaffarar wanda ya yi rantsuwa kuma ya warware ta ita ce: ciyar da miskinai guda goma, ko ba su tufa, ko kuma ‘yanta bawa, kuma yana da zabi wurin gabatar da kowanne daga cikin abubuwa guda uku da aka ambata, idan kuma ya kasance ba shi da halin da zai yi daya daga cikinsu, sai ya yi azumin kwana uku.Saboda haka, danganeda wannan tamabayar, idan ya zamana ya yi azumin ne domin rashi, to kaffararsa ta yi; babu komai a kansa, amma idan ya kasanace ya yi azumin ne tare da cewa yana da halin da zai iya ciyar da miskinai, ko ba su tufa, kaffararsa ba ta inganta ba, ya wajaba a gareshi ya ciyar da miskinai goma, ko ya ba su tufa, domin abin da ya yi ya sabawa fadin Allah a cikin Alkur’ani (Suratul Ma’ida aya ta 89)

Allah shi ne mafi sani.

Dr. Muhd. Alhaji Abubakar
 

Published in:  on March 31, 2008 at 9:03 am Leave a Comment

Tambaya ta 0001

Tambaya: Idan mace mai haila ta yi tsarki sai ta yi wanka bayan sallar asuba ta yi sallah kuma ta dauki azumin wannan ranar, shin za ta rama ko azuminta ya yi?

Amsa: Idan mace mai haila ta yi  tsarki kafin fitowar alfijir ko da da minti daya ne, amma dai ta tabbatar da tsarki, idan har a cikin Ramadan ne, to wajibi ne gare ta ta dauki azumi. kuma azuminta ya inganta ba sai ta rama ba,  domin ta yi azumi ne a cikin tsarki ko da kuwa ba ta yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, kamar yadda namiji idan janaba ta same shi ta hanyar jima’i ko mafarki, yake sahur ya dauki azumi, alhali bai yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir kuma azumin sa ingantacce ne.Dangane da wannan, ina so in fadakar da mata game da wani al`amari shi ne idan haila ta zo wa mace, alhali ta yi azumin wannan rana; wasu mata suna zaton cewa, idan haila ta zo bayan an sha ruwa kafin ta ci wani abu, ko kuma bayan faduwar rana da kankanin lokaci cewa azumin ta ya karye. A`a azuminta yana nan, kuma ingantacce ne (ba sai ta rama ba).

Sheik Muhammad Sahel Al-Uthaimeen

Published in:  on February 6, 2008 at 11:11 pm Leave a Comment