Ya zan zama Likita?
Assalamu alaikumu
Sunana Yayaha Abdullahi ina matukar sha’awar karanta likitanci, don haka don Allah wadanne shawarwari likita zai ba ni, kuma ina son in zai yiwu a yi min bayani filla-filla na bangarorin da lokunan da likitanci ya kunsa don na zabi bangaren da na fi sha’awa, kuma zan iya shi yadda ya kamata.
Na gode Allah ya saka da alheri
ws
***
Wa Alaikumusssalam Warahmatullah,
Wanda duk yake sha’awan aikin likita, dole ne tun daga sakandare ya dage ma English, Mathematics, Chemistry, Biology da Physics. A o’ level ba’a yafe ma ko daya. A a’ level kuma za ka yi Chemistry, Biology da Physics. Physics din ka iya yin wani darasi maimakon shi.
Inka shiga jami’a, aikin likita zaka koya a dunkule ta yanda zaka iya aiki a ko wani fanni na aikin likita amma ba a matsayin kwararre ba. Kwarewa yana daukan akalla shekaru hudu bayan biyar na jami’a.
Filayen kwarewa suna da yawan gaske amma a dunkule akwai wadanda suke alaka da duba marar lafiya kamarsu duba mata (Obstetrics & Gynaecology), duba yara (Paediatrics), aikin fida (Surgery) da duba cututtukan ciki (Internal Medicine). Wadannan ma akwai raberabensu na zurfafa kwarewa ta inda za ka zabi gaba ka kware kamar su kwakwalwa, zuciya, huhu, hanta, koda, ’kashi, jini da sauransu.
Akwai kuma likitoci da ke kwarewa a fannin bincike ba tare da sai sun ga marar lafiya ba. Suke da hakkin duba hoto ( X ray, Scan da sauransu), jini, fitsari, bayan gari, kaaki da kuma guture na wani gaba da aka samu ta hanyan aiki da sauransu.
A takaice abun da zan iya cewa kenan sai dai shawara kawai, shi aikin likita yana bukatan juriya da kula.
Allah ya sa mu dace.
Wassalam.
Dr. Abubakar Said Yagi
Dana yana zagi na a gaban baki ya zan yi da shi
Yana daga cikin abubuwan da yara suke samun kansu a ciki, yayin matakin yarinta shine dabi`ar zagi, kuma wannan dabi`ar takan samu ne sakamakon wasu abubuwa da suke bujurowa yaro a wannan mataki da yake ciki, don haka wannan yaron a bisa yadda akayi bayani zagin bai zamo masa dabi`a ba, ta yadda ko yaushe yake yinsa, sai dai kawai yana yinsa ne a wani guri mai matukar girman gaske, don haka sai a bi wadannan matakan kamar haka :
1- Lallai ne a samu lokaci a ringa zama da wannan yaron domin kokarin sanin abubuwan da suke damunsa, da kuma kokarin nuna masa baci da munin wannan dabi`a da yakeyi yayin da yaga baki a gidansu.
2- A wannan mataki da yara suke ciki sukan so suyi wani abu da zasu ga sun birge ko a yabesu ko kuma suja hankalin mutane zuwa garesu, musamman ma idan yaga bako, dan haka zai iya yin wannan mummunar dabi`ar domin cimma daya daga cikin wadancan abubuwan da aka ambata, dan haka sai iyaye su yi kokarin saita yaro ta yanda zai kosar da kishinsa da abubuwa masu kyau .
3- Akan sami wasu yaran basa son suga baki ko kuma a je dasu wajan baki, dan haka da zarar anyi baki a gidansu, ko ya sami kansa a gurin baki to zai yi wani abu da Malaman Tarbiyya suke ce masa ( daukan fansa a matakin yarinta) don haka sai yaga menene zai yi wanda yasan bai kyauta ba, saboda ya huce fushinsa da damuwar da yake ciki sakamakon halin da ya samu kansa a ciki, don haka sai iyaye suyi kokarin cusa wa yaro son baki a zuciyar sa, da kuma bin duk wata hanya da ta dace da hankalinsa da kuma shekarunsa .
4- Yana da matukar amfani ya kasance duk ranar da akayi baki ko ya samu kansa cikinsu kuma bai yiwa babarsa abinda ya saba yi mata ba, to ta samu wani abu da tasan yana tsananin sonshi ta bashi shi kyauta, kuma lallai ne ta gaya masa dalilin da yasa ta yi masa wannan kyautar,
Wadannan sune yan shawarwarin da nake ganin zasu iya yin amfani, kuma lallai ne iyaye maza su ringa shiga irin wannan matsalar domin su taya iyaye mata tarbiyyar yaransu, domin alhakin kula da kuma tarbiyyar yara bawai a wuyan iyaye mata kadai yake ba, kamar yadda ya zama wajibi iyaye su tsaftace bakunan su daga irin wadannan munanan dabi`u, domin yara sukan koyi abubuwa da yawa a wajan iyayensu .
Allah ya sa mu dace,
Dr. Ibrahim Abdullahi Sani R\lemo
Neman Shawara 0001
Neman Shawara: Assalamu alaikum, da Allah ina son a taimakamin da shawara game da wata matsala da na samu kaina a ciki, kuma tana cimin tuwo a kwarya!
Yarinya ce da ni ‘yar shekara biyar take uzzuramin da kuka fiye da misali,
wani lokacin takan kai awa hudu tana kuka! har sai kaina ya yi ciwo,
in ta fara kuka ba ta dainawa sai an yi mata abin da take so,
wani lokacin in ta fara kuka da daddare ga shi dai ta data, amma sai an goya ta za ta yi shiru; in ba haka ba sai ta kwana tana yi! Ta hana kowa bacci a gidan!
Don Allah wace shawara za’a taimaka min da ita don maganin wannan matsala?