MAKKA BABBAN GARI HAR DA GONAR LANTARKI!!!

In ji wani dan Fulani lokacin da yaje kasa mai tsarki domin yin aikin hajji bayan jirginsu ya sauka a filin jirgin sama na sarki AbdulAziz dake Jidda (kasancewar akwai fitulu da dama akan doron titin filin jirgin).

Published in: on March 27, 2009 at 8:10 pm Leave a Comment

Tsallan Badake

Badake wani mutum ne da ya ga samu ya ga rashi, ko kuma a ce “ya bata rawarsa da tsalle” Yadda abin kuwa ya faru shi ne: ani sarki ne yake da wata ‘ya “Son kowa kin wanda ya rasa” ya ce ba zai aurawa kowa ba sai wanda ya tsallake wata tsohuwa, kuma wawakekiyar rijiya. Samari suna ta gwadawa amma kowa sai a dauko shi tsamo-tsamo. Rannan sai Badake ya zo ya gwada sa’arsa, aka yi ta yi masa washi, da kirari “Badake Badake!! Badake!!!, da kansa ya gama fasuwa, kawai sai ya zabura, ya sheko aguje, firrr kamar tsuntsu, ya shallake rijiyar nan! Sai aka yi ta iho, ana sowwa, ana yi masa tafi, ana kuma tila masa kasa, sai Badake ya fara cika baki yana cewa: dama wannan ’yar rijiyar ce don abin kunya kwana da kwanaki aka rasa mai tsallake ta! to ni ko da baya da baya ba sai in tsallake ta ba! Sai wasu suka ce gafara nan kai din me! wannan din ma sa’a ka yi! Kawai Badake sai ya tashi a fusace, ya nufi rijiya da baya da baya, su kama ’yan zuga sai ihu suke yi; Badake!, Badake!!. Badake ya taho da gudu da baya zai tsallake rijiya, sai ZUNDUUUM!!! ya fada” shi kenan ya ga samu ya ga rashi! Shi ya sa wanda ya samu kansa a makamancin halin wannan mutum sai a ce “ya yi tsallaen Badake. To, “ Allah ya kiyaye mu da tsallen Badake”

Published in: on May 20, 2008 at 2:51 pm Leave a Comment

Don kar Mage ta Cinye!

Shehu Jaha ya saba kullum ya sayo gari, ganyaye (na ci) da kuma kayan marmari ya kawo gida, ita kuma matarsa ta saba ta dafa ganyayen, kayan marmarin kuma ta aika wa kwarta kyauta!

Kullum dare idan Jaha ya hakimci don ya kwashi girki da kayan marmari, ba abin da matar nan take kawo masa sai gurasa tsura!

Abin dai yana ta daurewa Jaha kai.

Rannan dai sai ya yi ta maza; ya tsaga bullensa ya tambayi matar:

“Wai ni ina ganyaye da kayan marmarin da nake shigowa da su kullum; ina kike kai su?” Sai matar ta kada baki ta ce:

“Abin da ka samu ka godewa Allah wannan shi ne rabonka!!! duk lokacin da na dafa wani abu MAGE take cinyewa”

Jaha ya dan tsaya tsai yana tunani akan maganarta, sannan sai ya yi wuf ya zabura ya dauke GATARINSA da yake rataye a jikin garu ya wurga shi  cikin akwati ya garkame.  

Sai matar ta tambaye shi:

“Jaha lafiya menene na buye gatari kuma?”

Sai ya ce:

“Na boye shi ne don kada mage ta gani ta cinye!

Sai matar  ta cika da mamaki, har ta yi wata irin shewa ta ce:

“Mahaukaci ne kai! Mage tana cin gatari ne!!

Sai Jaha ya ce mata:“Wallahi da hankalina sarai, amma ke me kike gani; yanzu magen da za ta rika cinye girkin dirhami goma, da kayan marmari na dirhami goman (ashirin kenan), INA GA GATARIN DIRHAMI UKU!!?”

Published in: on February 16, 2008 at 5:36 am Leave a Comment

“Ko Uwaka Za ka yi”!?

Wata rana wani baywan Allah zai shiga ban-daki, sai wani dan karamin dansa ya tambaye shi:

“BABA ME ZA KA YI?”

Sai ya yi masa banza, to kin san yara da tambaya, sai ya kara tambayarsa

“BABA ME ZA KA YI?” 

Ya kuma yin shakulatin bangaro da shi, kamar dutse yake yi wa Magana.

Yaron nan dai bai hakura ba sai ya kara tambayarsa. “Baba me za ka yi”

Sai uban ya ka da baki ya ce: “UWAKA ZAN YI!” 

shike nan Magana ta fuce kamar yaro ya manta, wata rana babansa ya yi baki, ta kuma kamawa zai shiga ban-daki, sai yaron nan ya kuma yi masa irin waccen tambaya; “BABA ME ZA KA YI?” shi kuma uban sai ya yi masa banza, shi kuwa yaron sai ya kada baki ya ce: “KO UWAKA ZA KA YI?!”

Sai duk kunya ta kama mahaifin nasa a cikin jama’a.

DON HAKA a tarbiyya yana da kyau duk irin tambayar da yaro ya yi a ba shi amsa, kuma lallai ne a ba shi amsa ta gaskiya, kar a yi masa karya, kamar yadda wasu suke yi in yara sun  tambaye su, ko dai su hana su tambayar, ko su yi musu shiru, ko ma su gilla musu karya, sai bayan sun girma su yi ta kallonsu da abin.

Kamar idan sun ce musu ina kakarsu da ta mutu? sai a ce ta tafi unguwa za ta dawo!

Ko ta ina ake haihuwa? Sai a ce masa ta baki! dss 

Published in: on February 11, 2008 at 8:45 pm Leave a Comment

Ya saki mata BIYAR Lokaci Guda!

Wani mai gida ne ya dawo a fusace, Magana ba Magana ba sai ya ce ya saki uwar gidansa! to ita kuma tana zaman arzuki da abokan zamanta guda uku, sai ta biyun  tasu hankalinta a tashe ta ce mai gida yau kuma me zan gani!, sai ya ce ke ma na sake ki!, ta uku ta taso a sukwane,  ta ce haba mai gida a rika hakuri! sai ya ce ke ma na sake ki! Ta hudun ta zo tana kuka ta ce mai gida yanzu ka saki mata uku lokaci guda! Amarcin matan nan bai cece ta ba, kwai sai ya ce ke ma ki bi su na sake ki!  Haba ba  sai gida ya rude da kuka ba. Makociyarsu ta kasa hakuri ta shigo gidan, musamman da yake ba’a saba jin irin wannan koke-koke ba, ta dauka ma mutuwa aka yi, bayan ta fahimci abin da ya faru, sai ta ce: haba baban wane a rika abu da hankali mana! Sai  rufe min baki,  ke ma in mijinki ya dawo in dai ya yarda ki tafi gidanku na sake ki!!! Illar fushi kenan, me  ka sani na koyarwar Annabi sallallahu alaihi wa sallam game da wanda ya samu kansa a cikin fushi???  In ba ka sani ba, tambayi malamai.

Published in: on February 6, 2008 at 11:00 pm Leave a Comment