Duk da wadata da yalwar arzuki da kasar Saudiyya take ninkaya a ciki, sai dai mutum zai sha mamaki idan aka bincina masa kadan daga matsalolin da matasan kasar suke fuskanta gameda aure.
Budurwa ta kai shekara talatin ko arba’in, ko ma fiye ba ta taba aure ba, ya zama ruwan dare gama duniya a kasar, samari da ‘yan matan da suke ganin tsakaninsu da aure sai dai ko a aljannah kuwa Allah ne kadai ya san yawansu.
Abubuwa da dama ne suka hadu suka haifar da wannan matsala, amma dai za’a iya cewa kashin bayan matsalar shi ne T SADAR AURE inda wani dansa zai shiga makarantar faramare amma mahaifinsa bai gama biyan bashin da ya ci a auren mahaifiyar yaron ba!
Sadakin Riyal dubu hamsin (Naira milyan biyu da doriya) ba wani sadaki ne na gani na fada ba, tun da yakan kai har dubu dari!
Wannan a sadaki kawai kenan, ba’a maganar biki wanda shi ma guda ne babariba, don akalla yakan lankwame kwatankwacin abin da sadakin ya lamushe, kai wani lokacin ma har ninninkawa yake yi!
Sannan ga maganar gidan haya da tarkacen da za’a zuba a ciki, da motar bashi, da tafiya wani gari, ko ma wata kasa don a ci amarci da angwanci da tsinke (Honey Moon)…
Wannan kuma duk ba’a zo maganar karkon auren ba, don ita ma Magana ce mai zaman kanta.
Duba da yadda wannan matsala take nema ta illata al’ummar baki daya ta bangarori da dama, wasu kungiyoyin taimakon jama’a a kasar –musamman wadanda suke mayar da hankali akan rayuwar iyali- suka tashi haikan wurin murkushe ta, da salo, da dabaru iri iri, daya da ciki shi ne: Hada ma’aurata da dama a biki guda, tare da ba su gudunmawa ta musamman kafin, da lokacin, da kuma bayan auren don saukaka musu al’amura.
Za’a iya kasa irin wannan aure na taimakekeniya zuwa kashi biyu:
Na Farko: Wanda dangi, ko kabila, ko unguwa daya suke yi tsakanin ‘ya’yansu.
Na Biyu: Wanda cibiyoyin taimakon al’umma suke yi.
An fara wannan tsari karkashin irin wadannan cibiyoyi na alheri tun sama da shekaru goma da suka shude, kuma abin ya yi tasiri ba dan karami ba, shi ya sa ma kullum yake kara samun karbuwa tsakankanin matasa da iyayen angwaye da amarye duk da cewa ya saba da ala’adun larabawa.
A sati dayan nan da ya shude kadai an yi bikin aurar da matasa sama da dubu uku ta wannan hanya.
- Ranar Juma’a 10/6/2011 bikin aurar da “Marayu” 100 na farko karkashin gidan Marayu na Insaan a Riyadh.
- Ranar Laraba 22/6/2011 bikin aurar da matasa 800 (]ari takwas) a Jizan karo na takwas karkashin cibiyar saukaka aure ta Jizan
- Ranar Asabar 25/6/2011 bikin aurar da matasa dari biyu a Sharkiyya karo na farko karkashin cibiyar Wi’am a Dammam
- Ranar Lahadi 26/6/2011 bikin aurar da matasa dari biyu karo na tara a Ahsa’a
- Ranar Laraba 29/6/2011 bikin aurar da matasa 1000 (dubu) a Madina karo na uku karkashin cibiyar Usraty
- Ranar Laraba 29/6/2011 bikin aurar da matasa 1200 (dubu da dari byu) karo na goma sha biyu a Jiddah karkashin cibiyar Mawaddah.
Gudunmawar da ake ba wa wadannan matasa takan saba daga gari zuwa gari, hakanan yawa da karancin angwayen da amaren, amma dai a dunkule tana kunsar abubuwa kamar:
- Dauke musu nauyin taron biki wanda na bayyana a baya cewa yana lamushe dubunnan Riyal barkatai
- Kyautar kudi,kamadaga Riyal dubu biyar har zuwa dubu talatin
- Kyautar set ]in kayan ]aki (gado, kujeru, kwaba… dss)
- Kyautar kayayyakin lantari (Tukunyar sanyaya daki Ac- biyu zuwa sama- firinji, injin wanki, injin shara, rishon gashe-gashe dss).
- Set din gwal ga amarya.
- Kwasa-kwasai daban dabankansanin makama da yadda ake gudanar da rayuwar iyali, hada da shedar halarta.
- Kyaututtuka kala kala da sukan hada har da motar hawa sabuwa fil da gwala-gwalai dss. (ta hanya kur’ar mai rabo ka dauka).
Wadannan cibiyoyi sukan sa sharadai na wanda zai cancanta irin wannan tagomashi, ala misali sharadan cibiyar Usraty ta Madina sun hada da:
- Angwon ya zama dan Madina ko daya daga cikin kauyukanta
- Shedar auren da ba ta wuce shekara ba, mai satamfin kotu a jiki.
- Kada sadakin da zai bayar ya wuce Riyal 35000 (Dubu talatin da biyar. Kwatankwacin Naira milyan daya da rabi).
- Ya zama yana da aikin yi, kuma gundarin kudin shigarsa a wata bai wuce Riyal 3000 (dubu uku).
- Halartar kwasa-kwasai na musamman da cibiyar take gabatarwa ga masu shirin aure.
Duk wanda ya cika wadancan sharadai to ya cancanji wannan goma ta arzuki.
Ranar larabar da ta shude (29/6/2011) ne aka yi wannan gagarumin biki a Jiddah da Madina kamar yadda ya gabata, kuma Allah ya sa na samu damar halartar na Madinan tun daga farko har karshe. Tsarinsa ya burge ni kwarai, kuma na ga alamar ya ya kayatar da mahalarta. Abin sai wanda ya gani.
An yi taron ne a rufaffan dakin taron babban filin wasan kwallo na sarki Muhd. Ibn AbdulAziz dake Madina.
An kawata dakin kwarai da fitilu iri iri masu daukar hankali, kai har da fitulun kwai irin namu na gargajiya guda talatin da daya saboda tuna da!
An karaso da angwayen wurin taron bayan an kewaya garin Madina da su a cikin manyan motoci (masu cin mutane hamsin) guda goma, ga tarin babura nan na samari suna jagorantar motocin, cikin farin ciki da ‘yan wakoki da bushe bushe da mahaya baburan suke yi wadanda dukkanisu samari ne.
Bayan angwayen sun yi sallar Isha’i, sai suka shigo wurin taro a tsanaki cikin farin ciki, kowanennesu sanye da doguwar riga fara, da hula, da Gutrah (Rawani ko yafen kai irin na ‘yan Saudiyya) su ma duka farare, da Iqal (Kwarkwaro n da suke sawa a saman yafen) baki, sannan ga tsantsareriyar Mishlah (Alkyabba) ruwan madara kowanne ya zubo ta.
Sarkin Madinamai Martaba AbdulAziz Ibn Majid Ibn Abdul Aziz ya karaso dakin taron karfe 10:8 na dare, ana ta yi masa kirari, da ya zauna sai aka sanya wani bangare na kiran sallar masallacin manzo, sannan kuma sai taro ya fara.
Mashahurin makarancin nan, malami a jami’ar Musulunci ta Madina, kuma tsohon limamin Masallacin Manzon Allah (SAW) Dr. Muhammad Ayyub shi ya bude taron da karatun Alqur’ani, inda ya rangada tilawar ayoyi shaukun karshe na Suratul Furqan.
Sannan kuma sai wasu kwararrun mawakan gargajiya suka kasa angwayen kashi biyu, sannan suka jagorance su baki daya suna ta rera wakoki irin nasu na gargajiya, ga guda nan ana ta yi daga dakin taron mata inda amaren suke, sannan suka taho da su a wani tsari na layi da tafiya mai ban sha’awa, suka kewaya sarki da shauran mahalarta suka gan su, suka taya su murna, kuma saka yi musu addu’a ta alheri.
Bayan sun koma sun zauna sai wata kungiyar masu rawar gargajiya irin ta yan su (masu kamun kifi) suka zo suka cashe, sannan sai aka harba fitilu masu kyalkyali, duk don nuna farin ciki.
Bayan nan kuma sai Babban sakataren cibiyar ta Usrati, wadda ta tsara wannan biki, wato Dr. Abdul Bari Atthubaiti, limami a masallacin manzo, kuma babban alkali a babbar kotun Madina ya yi jawabin sa, inda ya godewa Allah bisa tallafin da ya yi musu na iya gabatar da wannan hidima ga matasansu, sannan ya yi bayanin mahimmancin irin wannan aiki a musulunci, ya kuma kwadaitarwa kan a rika bayar da gudunmawa don gudanar da shi, daga bisani kuma ya godewa mahukunta kasar musamman sarkin Madina, babban bako, kuma shugaban kwamatin gudanarwa na cibiyar bisa hadin kai da kaimi, da karfin gwiwa da yake ba su, da kuma duk wanda ya bayar da gudunmawa, ko ta shawara, ko tunani, ko kudi … ko fatan alheri, ko ma halarta wurin taron.
Sannan aka kuma yin wakoki, sai kuma wakilin kamfani Haadiya Abdul Ladif Jamil ya gabatar da jawabi a madadin kamfanoni da cibiyoyi da mutanen da suka bayar da gudunmawa.
Sai aka kuma yin ‘yan wakoki, aka sa jawabin sarki Abdallah na tagomashin da ya yi wa ‘yan kasar na bayar da kyautar Riyal dubu daya duk wata ga duk mai neman aiki har ya zuwa ya samu, sannan kuma sai aka yi raywarsu ta gargajiya da ake yi da takubba da sanduna.
Daga nan kuma sai aka yi kuri’ar mai rabo ka dauka na abubuwa uku:
- Motoci uku sababbi fil kirar Hyundai 2011
- Kayan daki (gado, kujeru, kwaba dss) guda goma
- Set din gwal guda biyar
An rubuta sunan kowane ango a jikin takarda, aka sa a cikin wani gilashi aka juya su baki daya, sannan wata ‘yar karamar yarinya da ba ta wuce shekara shida ba da aka caba wa ado ta zo- a bainar jama’a- ta dauki takarda daya daga cikin takardun nan dari biyar, ta kai wa mai gabatarwa, shi ma take a nan ya bude ya karanta sunan wanda ya ci mota ta farko, aka kira shi nan take sarki ya danka masa makullin motar, sannan ta kuma daukowa, aka karanto wanda ya ci ta biyu, shi ma ya zo ya karbi makullin…. Haka dai har zuwa kyautar karshe.
Daga nan sai aka bai wa mahaifin amaryar da sakadinta ya fi na kowacce karanci a wadanda aka yi musu bikin, inda ya rangwanta ya karbi Riyal dubu goma kacal! (Kimanin Naira dubu dari hudu da talatin)! An ba shi kyauta ne don ragowar iyaye su yi koyi da shi wurin karbar sadaki kadan kamar yadda ya yi!
Sannan kamfanin waya na STC shi ma ya bai wa kowane daya daga cikinsu kyauta, hakanan ma cibiyar Usrati (amma wadannan kyaututtuka ba a wurin aka raba su ba).
Dama kuma a jawabin Babban sakataren cibiyar liman Thubaiti ya bayyana cewa cibiyar Salih Al-Rajihi ta dauki nauyin kai gabadayan angwayen da amarensu haji bana, har da karin wasu ma’auratan dari biyar.
Wannan ita ma ba karamar dankwaleliyar kyauta ba ce, don jumullar kudin da ta ci: Riyal milyan bakwai da rabi (Riyal 5000×1500) (Kimanin Naira 322,500,000).
Idan ka san yadda zuwa haji yake yi wa matasan Saudiyya wahala, za ka san cewa in ba irin wannan damar ba, to wasu da dama daga cikin wadannan matasa ba za su iya sauke farali ba sai nan da shekaru masu tarin yawa in ma sun iya saukewa.
Daga nan kuma sai sarkin Madina ya mika kyaututtukan da cibiyar ta tanada ga wadanda suka bayar da gudunmawa da suka hada da kamfanoni, cibiyoyin agaza wa jama’a, da kafafan yada labarai, dss.
Sannan kuma ya je, shi da liman Thubaiti babban sakataren Usrati suka yi hoto su da angwayen don tarihi.
Bayan an ci abincin dare, kowane ango ya je ya dauki amaryarsa ya yi gaba.
|
Sarkin Madina AbdulAziz ibn Majid, daLimamin Haramin Madina Dr. AbdulBari Athubaiti, da wasu daga cikin angwaye a Madina. |
A hirar da na yi da jami’in yada labarai na Usrati, Ustaz Nadim Bakhsh ya bayyana min cewa jumullar gudunmawar da ma’auratan suka samu daga cibiyar Riyal milyan shida ne (Kimanin Naira 258,000,000)- ban da kudin kai su hajji- kamar yadda ya bayyana min cewa kudin da aka kashe a wurin taron ya doshi Riyal 500,000 (Kimanin Naira: 21,500,000)
Yanzu abin tambaya a nan shi ne:
- Ina wadannan cibiyoyi suke samun kudaden da suke yin irin wannan hidima?
- Menene tasirin irin wannan gudunmawa a cikin al’ummarsu?
- Me za mu koya daga irin wannan hobbasa a kasashenm?
Game da tambaya ta daya, to suna samun kudinsu ne daga:
- Daidaikun mutane kowa dai dai karfinsa. Misali: motoci biyu daga cikin ukun da aka yi kura’ar mai rabo ka dauka a Madina, set din gwala-gwali biyar, set din kayan daki guda goma, daidaikun mutane ne suka dauki nauyin hakan kamar yadda aka bayyana a wurin taron.
- Cibiyoyi da kungiyoyi taimakon jama’a, kamar cibiyar Salih Al-Rajihi, wadda ita kadai ta dauki nauyin bikin aurar da matasa (maza da mata) dari takwas a Jizan, da dari biyu a Ahsa’a. da kai gabadayan na Madina har da karin dari biyar hajji. A wurin bikin aurar da wadancan matasa 800, babban sakataren kwamatin amintattu na wannan cibiya ta alhaeri ya bayyana cewa duk shekara cibiyarsu tana kashe Riyal milyan goma shatakwas (kimanin Naira milyan dari bakwai da saba’in da hudu) wurin aurar da samari da ‘yan mata 4000 (dubu hudu) a sassa daban daban na Saudiyya. Ka tuna aurar da matasa daya daga cikin tarin ayyukansu.
- Kamfanoni daban daban kamar kamfanin Haadiyah Abdul-Ladif Jamil na wata ‘yar kasuwa a kasar. Wannan baiwar Allah mai suna Haadiyah- ta hanyar wannan kamfani nata- ita ta bayar da kusan rabin gudunmawar da aka baiwa matasan a Madina a bikin bana, don said a ta bai wa kowane ango da amarya mahimman kayayyakin lantarki da suke bukata a gidansu (Ac uku, firinji daya, injin wanki daya, injin shara daya, rishon gashe gashe daya… dss) don haka a bikin Madina na bana kadai ta bayar da kyautar: Ac 1500, firinji 500, injin wanki 500, injin shara 500, rishon gashe gashe 500. Bugu da kari, ba a Madina kadai take bayar da irin wannan gudunmawa ba, har da wasu daga sassan kasar, kamar yadda ba bana ta fara ba.
- Zakkah (Manyan malaman Saudiyya sun bayar da fatawa cewa za’a iya ba irin wadannan cibiyoyin zakka don gudanar da irin wadannan ayyuka).
Ya kamata wasu tambayayi biyu su haifu daga wannan tambayar ta farko, wadannan tagwayen tambayoyi su ne: Ya aka yi wadannan masu kudi suke ciyar da dukiyoyinsu a irin wadannan ayyukan alheri, kuma ya aka yi irin wadannan cibiyoyi suke iya gamsar da kamfanoni da masu kudin har suke iya yi musu marka-markar kudi haka?
Gameda da abin da ya shafi karfin halinsu wurin ciyar da dukiyoyinsu ta wannan hanya, ni a ganina akwai dalilai da dama da suka sa suke yin haka. Ga wasu daga ciki:
- Imaninsu da alkawarin Allah (SWT) cewa wanda ya ciyar ta farkinSa zai ninninka masa, da fadin Manzon Allah (SAW) cewa “Kudi bai taba raguwa ba don an yi sadaka da wani bangare nasa).
- Nemankudi da manufa, ma’ana sun san me yasa suke neman kudi, kuma yin irin wadannan ayyuka da kudaden nasu yana daga cikin manufofinsu na nemansu, don haka lokacin da suke ciyar da kudinsu ta wannan hanyar suna jin cewa suna cimma wani mahimmin buri ne a rayuwarsu.
- Alamar cewa suna kwatanta cin halak da fitar da hakokkin Allah a dukiyarsu, domin wanda yataradukiyarsa ta hanyar haram bai fiya samun dacewar yin irin wadannan kyawawan ayyukan ba.
- Tarbiyantarsu da aka yi akan bayarwa, ba akan karba ba
- Tausayi da rahama da jinkan talakawa dake zukatansu. Dss
Gameda yadda irin wadannan cibiyoyin suke iya gamsar da su har su iya damka amanar kudadensu a hannunsu kuwa, ni a ganina wannan yana komawa zuwa abubuwa da dama wasu daga ciki su ne:
- Kyakkyawar niyyar wadannan cibiyoyi. Bahaushe yana cewa wai “Farar aniya laya”
- Amanarsu. Zai wahala ka ji an ce irin wadannan cibiyoyi sun ci amanar wanda ya ba su kudi su yi aikin alheri da shi, ko su raba a tsakaninsu.
- Masu gudanar da su ba da wannan aikin suka dogara ba, don duk manyan ma’aikatan wuri za ka ga suna da harkokinsu daban, kai wasu ma masu kudin gaske ne.
- Tsari da iya gudanarwa; domin idan mutum ya bayar da kudi a yi wani abu da shi, ko shi da kansa aka ce ya kashe kudin nan, da wahala ya iya kashe su yadda ya kamata, kuma ta hanyar da ta dace kamar yadda su za su yi, don haka idan mutum ya ba su kudi ba ya jin cewa za’a barnatar masa, ko banzatar masa da dukiya.
- Kiyaye sharuddan da mai kudin zai bayar; idan mutum ya ce ga kudi a gina rijiya, to fa ba yadda za’a yi su yi wani abu da shi daban- kamar gina masallaci- sai sun nemi izininsa, ko kuma su dawo masa da kudinsa idan ba za su iya cika sharadinsa ba.
- Yin komai a bude ba tare da rufa rufa ba; kowace shekara suna buga rahoto na musamman gameda da abin da suka samu da abin da suka kashe, da ayyukan da suka yi- hard a hotuna da maganganun wasu daga cikin wadanda suka amfana- da abin da suka sa gaba a shekara mai zuwa, da kudin da zai ci, su yada kowa ya gani, sannan kuma sukan rubuta rahoto na musamman ga wanda ya ba su kudi mai kauri su yi masa bayani filla-filla na yadda suka kashe kudin, kuma su tambaye shi idan ya amince da yadda suka kashe, ko kuma yana da gyara a kai.
- Tallata kamfanonin da suka ba su gudunmawa a jaridu da mujallu, da shafukan yanar gizo, da sanarwarkanhanya ta hanyar sanya sunayensu da tambarinsu da bayanin cewa wadannan kamfanoni ne suka dauki nauyin wannan aiki. Suna yin haka a duk sanarwar da za su fitar mai alaka da shirin da za su yi. (Amma ban ga suna rubuta sunayen daidaikun mutane ba, sai dai kamfanoni, ko cibiyoyin taimakon jama’a).
- Girmamawa wa]anda suka bayar da gudumawa da ba su shedar yabo, a wurin taro.
Gameda da tambaya ta biyu kuwa- Manene tasirin irin wadannan gudunmawa a cikin al’ummarsu?
Gaskiyar lamari irin wannan gudunmawa da sharye shirye suna da tasiri matuka a rayuwarsu, daga cikin irin wannan tasirin akwai:
- Yaduwar soyayya da kaunar juna tsakanin jama’a, don haka za ka ga akwai karancin gaba da hassada da keta tsakanin mawadata da matalauta, saboda mawadaci zai yi wa talaka abin da ko mahaifinsa ba zai iya yi masa ba. Za ka jima kafin ka ji talakan Saudiyya yana zagin mai kudi.
- Hadin kai da dunkulewa tsakanin gabadayan al’umma; domin kuwa su dai wadanda ake bai wa wannan gudunmawa masu karamin karfi ne, amma kuma duk inda aka gabatar da irin wannan shiri za ka ga sarkin yankin shi ne yake jagorantar shirin, sannan kuma malamai da limamai, da alkalai, da sauran manyan mutane na yankin manyan baki, su kuma masu kudi su ne masu bayar da gudunmawa, ga talakawa nan kuma wadanda suka samu wannan taimako, sannan ga ragowar mutanen gari nan da suke taya su murna, kowane bangare yana yi wa dayan addu’a da fatan alheri.
- Rage matsalar rashin aure, tsakanin matasa. Na fada a baya cewa ta kai akan samu samari da ‘yan matan da suke hakura da aure, kamar yadda za ka ga mata da yawa sun wuce shekara talatin, har sun doshi arba’in amma ba wanda ya taba kula su da niyyar aure, amma ta hanyar irin wannan shiri, da kuma wasu shirye shiryen da dama ana samun raguwar wannan bala’i.
Sai tambaya ta karse; Me za mu koya daga irin wannan hobbosa?
Gaskiya abubuwan da muke koya a irin wannan suna da tarin yawa, zan fadakar akan wasu kadan daga ciki wa la’lla su yi mana amfani:
- Neman dukiya ta hanyar halal; domin wanda yataradukiya ta hanyar haram da wuya ya samu dacewar yin irin wadannan ayyuka kamar yadda na fada a baya.
- Yan abu don Allah, ba don siyasa, ko neman suna, ko neman daukaka da bautatar da talakawa da cutatatar da su don an ba su wani abu daga dokiyar da Allah ya ba wa mutum ajiya ba. Ko kuma taimakawa mutum da nufin kai ma ya taimaka maka a nan gaba. Ba shedar zukatan irin wadancan bayin Allah nake yi ba, don shinan gaibu sai Allah, amma dai yadda suke al’amuran nasu akwai alamar Allah a ciki, don za ka ga hidima ta milyoyin Riyal amma ba za ka san wanda ya yi ba, kai har shardantawa ma suke yi cewa kada a fadi sunansu. Ko a bikin da na halarta ranar Laraba a Madina, take a nan sarki ya bayar da sanarwar cewa wani bawan Allah ya bayar da kyautar karin motoci biyu sababbi ga angwayen- bai fadi sunansa ba-
- Ciyar da dukiyoyinmu tafarkin Allah madaukakin sarki, kamar ta hanyar irin wadannan ayyuka, gina masallatai, makarantu, asibitoci, haka magunanun ruwa, daukar nauyin dalibai da masu bahasi, samar da ayyuka ga matasa dss, maimakon kashe kudi a abubuwan da in ba su cutar ba, to amfanin da suke da shi bai taka kara ya karya ba in har akwai shi, kamar batar da dukiya a fagen wasanni, kade kade da raye raye, tarurruka marasa asali a addini, ci banza ci wofi, ko gantali kasashen duniya, saya wa matasa kwaya don bautar da su a fagen siyasa, kashewa matan banza dss. Daga cikin abin da ya kamata a yi tsokaci a kansa a nan akwai mugun nufin da wasu suke da shi wurin ciyar da dukiyoyinsu, sai su ba wa mutum kudi da yawa –watakila ma ba zai iya sarrafa su ba- su je wai ya je ya yi aikin alheri, amma a hakikanin gaskiya ba wannan ne a ransu ba, so suke su bata shi, su samu bakin maganar cewa kowa “Kowane gauta ma ja ne, sai in bai sha rana ba” “Malamai” aka fi danawa irin wannan tarkon don mugun nufi!
- Rashin dogara da gwamnati a komai. Wani abin da zai ba ka sha’awa a nan shi ne duk irin wannan hidindimu ba gwamnati ce take yi ba, sai dai kawai daidaikun jami’an gwamnati wanda ya yi niyya, kuma yana da hali, shi ma ya bayar da abin da zai iya – kamar a bara sarkin Madina shi ma ya bayar da kyautar motoci biyu- ko a rika dauka a albashinsa duk wata. To idan har a kasa irin Saudiyya kasar da ‘yan kasarta suke samun duk wani abin more rayuwa dai dai gwargwado, kasar da fetur ya fi ruwa arha, amma duk da haka ba sa dogara kacokan akan gwamnati, ina ga mu da abubuwa da dama na lalurar rayuwa ba su wadata ba, ko ma babu su baki daya, bugu da kari, kullum ita kanta gwamnatin kuka take yi cewa ba za ta iya ba; sai an tallafa mata! Don haka danuwa maimakon kullum a zauna a dakali a yi ta takaici, ko a shiga gidan radio a yi ta babatu cewa gwamnati ba ta yi kaza ba, ko taki yin kaza, duba abin kai da sauran abokana za ku iya yi domin ku taimaki kanku da al’ummarku ko da gwamnati ba ta shigo ciki ba. Alhamdu Lillahi akwai wadanda suka fara irin wannan kokarin, kuma kullum ci gaba suke samu.
- Kokarin dogaro da kai. Yana daga cikin abubuwan da za su konawa mai hankali rai a ce wai matsalar mahaifiyar mutum ko kanwarsa, ko matarsa, ko dansa ko kanensa, ko makocinsa… dss, amma saboda akidar “Allah ya ba ku mu samu” da ta yi katutu a zakatan da yawa daga cikinmu, wai jira yake wani banasare daga kasar turai, ko balarabe daga kasar larabawa ya zo ya taimaka masa! Bayan zai iya tabuka wani abu! Wannan alama ce ta mutuwar zuciya da rashin kishin kai da kulafuci. Don haka ya kamata mu rika kokarin warware matsalolinmu da kanmu ba sai mun jira wasu ba, kuma na tabbata za mu iya da izinin Allah.
- Kafa cibiyoyin taimakon jama’a masu zaman kansu da bayar da taimako ta hanyarsu. A cikin al’ummarmu akwai wasu da Allah ya datar da su, suke iya ciyar da dukiyarsu ta hanyar alheri, kamar ciyarwa, kudin magani, kudin makaranta, taimakawa malamai, kai mutane hajji da umara, dss sai dai abin la’akari a nan shi ne, da zarar Allah ya karbi ransu, ko wadatarsu ta yi kasa, sai wannan aikin alherin ya yi rauni, ko ma ya tsaya. Wani bawan Allah a daya daga cikin jahohin arewacin Nijeriya ya sanya daruruwan marayu makaranta mai tsada, kuma ya dauki nauyin biya musu kudin makaranta, duk shekara yana kashe milyoyin kudi a wannan aikin alheri, amma yana rasuwa mafi yawancin yaran karatun ya gagare su, har makarantar kasan kasa suka kasa zuwa! Irin wannan da cibiya ya kafa mai kula da wannan ya samar mata da hanyar samun kudi, da da wahala wannan aikin alheri ya mutu da mutuwarsa, Don haka ina kira ga masu halin da Allah azurta su da zuciya ta yin irin wannan taimako da su rika bude cibiyoyi, su sa masu amana, kuma kwararru wurin gudanarwa don gudanar da ita, kuma su sama musu hanyoyin samun kudi masu dorewa. Wasu cibiyoyin a Saudiyya manyan otel suke ginawa a kusa da harami, wasu kuma noma, wasu kuma su sayi hannun jari, wasu kuma sayen kadarori, wasu su ribar rubuce rubucensu dss. Na je wata makaranta a Afrika ta kudu a shekarun baya, sai naga wanda ya gina ta, ya gina wani babban gidan mai a jikanta, ya kuma mallaka mata shi, don ya zama daya daga cikin hanyoyinta na samun kudin shiga. Wannan hanya ta burge ni sosai!
- Bayar da kulawa ta musamman ga raunana a cikin al’umma. Na farko dai wadanda ake bai wa wannan taimako masu karamin karfi ne, sannan kuma a ba’a manta da nakasassu ba, don bara waccan kungiyar kula da nakasassu ta Riyadh babban birinin Saudiyya mai suna (Harakiyya) matasa (maza da mata) dari da biyu ta aurar, bara
Wasu daga cikin angwaye “Nakasassu”
kuma saba’in da biyar, inda kowane ango da amarya suka samu gudunmawar Riyal dubu hamsin, bayan bikin da aka yi musu. Abin bai tsaya a nan ba, don kamar yadda ya gabata sati ukun da suka wuce cibiyar AbdulAziz ibn Fahd marayu –wadanda suka tashi a gidan marayu- dari ta aurar, kuma shirinta na wannan shekara shi ne ta aurar da irin wadannan marayun dubu a bangarori da dama na kasar.
- Daukar mataki a aikace don magance matsala, maimakon takaitawa akan korafi da takaici, ko mutum ya tafi da rayuwarsa a “adawa”!
- Fada da cikawa, sau tari za ka ga wasu daga cikin mutane a kasashe irin namu sun bayar da gudunmawar kudi a wurin taro, amma karshenta kafin su fito sai an yi jan ido, wani lokacin ma sai dai a bar shi da Allah! Ko kuma mutum ya ce ya bayar da gudunmawar milyan daya misali, nan kuwa a zuciyarsa dubu goma ya yi niyya, ragowar ya fada ne don alfahari da burga, don haka bayan ya bayar da goman- in ya bayar kenan- ragowar sai dai a yi masa Allah ya isa! Amma su a irin wadannan tarurrukan na su, sau tari kafin ma a bayar da sanarwar cewa wane, ko cibiya kaza ta bayar da gudunmawaR kaza, gudunmawar tuni ta zo hannu. Alal misali kyaututtukan mai rabo ka dauka; gwalagwalai, da sababbin motoci uku a Madina, da wasu sababbin guda bakwai aJidda.. dss, gurin taron ma aka zo da su, take a nan, a gaban jama’a za’a bude takarda, a karanto sunan mutum, a mika masa mukulli, ga motar nan a waje in ya so ya shiga abarsa ya yi gaba a lokacin.
- Dorewa akan aikin alheri, za ka ga duk irin wadannan ayyuka in aka fara su, to an fara kenan kullum sai dai su yi gaba, ba su yi baya ba, ballantana a ce sun mutu, yanzu baya ga matasa 1200 da aka yi bikin aurarwa Jiddah satin da wuce, to kafin hajin bana ma za kuma bikin aurar da wasu guda 1000 (dubu) kamar yadda Shugaban kwamatin gudanarwa na cibiyar –Mawaddah- wato babban alakali a kotun daukaka kara ta Makka Sheikh Abdullah ibn Abdur Rahman Aluthaim ya bayyana a wurin taron, sabanin mu da dorewar abu a wurinmu ba karamin jan aiki ba ne.
- Kowa ya bayar da irin gudunmawar da zai iya, kuma daidai karfinsa, a irin wadanann cibiyoyin za ka ga kowa da irin gudunmawar da yake bayarwa, ba kuma da wani jin nauyi ba, a lokacin da wani zai bayar da kyautar milyan goma, wani dubu goma zai bayar, wani zai bayar da kyautar ruwa da lemukan da za’a sha a wurin taro, wani kuma tashi zai yi ya raba kyauta ba tare da wani jin nauyi ba, tare da cewa zai iya zama malami ko ma’aikaci, wani babban mutum mai matsayi a cikin jama’a amma wannan ba zai hana shi irin wannan aikin da wasu a irin wurinmu za su iya daukar sa a matsayin aiki na kaskanci ba.
- Malamai da managarta a cikin al’umma su rika shiga cikin rayuwar mutane, kuma su rika rike amana, su zama masu iya gudanarwa a duk wani aiki da aka dora musu. Duk da cewa wannan abin nema ne akan kowa, amma dai ba kamar irinsu.
Allah ya sanya musu alheri, ya kara musu taimako, mu ma ya agaza mana wurin kokarin kwatantawa Amin summa Amin.
Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu
(Laraba 6/07/2011
Nura Abdullahi Madina
Posted by N. Y. Mikail on July 9, 2011 at 11:29 am
Malam Nura Allah ya saka da alkhari, lalle mutanen mu na kishirwar irin wannan rahoto. Allah ya datar damu wajen irin wadannan ayyuka na alkhairi.