YA MUTU YA DAWO!!!

Ya ce na dawo daga kwas din aikin soja kenan ina mai cike da farin ciki, ina ta tunanin yadda zan je na samu yara da sauran mutanen gida da masoya.
Bayan na isa gida da ’yan sa’o’i, kowa yana ta murna, manya da yara.
Kwatsam sai na ji ana dukan kofa da karfin gaske, da na fita sai na ga jami’an tsaro, suka kira ni da cikakken sunana, kuma suka ce ni suka zo nema, don haka shige mu je!
Suka tasa keyyata zuwa ofishin ’yan sanda. Har zuwa wannan lokaci ban wani damu ba; don na san ban yi wani laifi ba.
Amma ba zato ba tsammani sai na ji wai ana tuhuma ta da wani mugun laifi, wanda wannan ya sa ba ki daya na rude, na firgice, na dimauce, har na kasa magana.
Ana tuhumar ka da kisan ganganci! Mataimaki D.P.O ya ce min! kai ne ka kashe wane dan wane, kuma kana da sammaci a kotu!
Sai na rasa abin da yake min dadi a duniyan nan, hankalina ya dugunzuma, na kasa gasgata abin da nake ji, na yi ta hakilon gamsar da kaina kan cewa wani ake tuhuma ba ni ba, sunan ne dai ya yi kama, ko wani kuskuren fahimta.
Amma daga karshe na fuskanci abin babba ne, bayan an ta bincika ta ba ji ba gani. Abin ya kara dagulewa bayan masu binciken sun sanar da ni cewa inkarina ba shi da wani amfani; don ga shedu nan duk sun rantse suna masu tabbatarwa cewa kai ne makashin wannan mutum! Ya ce haka na yi ta fafutukar kare kaina, har karfina ya kare, musamman lokacin da na ga an mika ala’amarina zuwa gurin alkali.
Nan wasu mutane suka bayyana gareni suka ba da sheda cewa lallai ni ne na yi kisan nan, kuma Wallahi Billahillazi La Ilaha Illa huhu ban taba ganin shedun nan ba, kuma ban taba sanin mutumin da suka ce na kashe ba!
Haka na zauna tsahon shekaru goma sha biyar a kurkuku! Saboda ’ya’yan mutumin nan kanana ne, bayan sun balaga suka ki yin afuwa, suka ce su kawai kisasi suke nema! Bayan bakin ciki da damuwa, da zaman dar dar da na yi tsahon shekarun nan sha biyar a ciki, rannan da sanyin safiyar ranar Juma’a sai ga jami’an tsaro sun shigo inda nake daure, suka miko min takarda don na rubuta wasiyyata, kuma suka sanar da ni cewa yau ita ce ranata ta karshe a duniya! Suka lakkana min Kalmar shahada.
Bayan na gama rubuta wasiyya da dan lokaci, sai suka sani a gaba zuwa filin sare kai, muka samu filin makare da jama’a, ga jami’an tsaro nan iya ganinka sun yi masa kawanya. Har zuwa wannan lokacin ambaton Allah ba ya yankewa daga bakina.

Aka karasa da ni gurin fille kai bayan an rufe min idanuwana, mai shela ya fara shelanta laifin da aka ce na yi, da madogarar da aka dogara da ita wurin yanke min hukuncin kisa. A daidai wannan lokaci sai na dada tunawa da Allah, kuma na kara dagewa wurin ambatonsa, da addu’a, na ce: “Ya ubangiji zalunta ta aka yi! Ya ubangiji ni zalunta ta aka yi!! Kuma ka yi alkawari, kuma alkawarinka gaskiya ne, kuma kana amsa addu’ar wanda aka zalunta, ya ubangiji ni zalunta ta aka yi, kuma kai ne masanin dukkanin abubuwan da suke boye, na mika lamarina gareka, ba bu abin bautawa da gaskiya sai kai!!!… WALLAHI ban kammala addu’ata a lokacin da ake karanto wancan bayani ba, sai kawai na ji ana hayaniya ana ihu da karfi, na kuma jiyo sautin wani mutum yana cewa da karfi: “Kada ku kashe shi! Ni ne na yi kisan!! kada ku kashe shi! Ni ne na yi kisan!! Sai guri ya rude aka ta hayaniya, karanta bayani ya tsaya cik, sai na ji daya daga cikin jami’an tsaron yana cewa: Ga shedun nan sun yi ikrari cewa su ne suka yi kisan, na ji wasu kuma suna neman a gaggauta zartar da hukunci, haka aka dauki lokaci mai tsaho ana ta cece ku ce, ni kuma ina durkushe, ido a rufe, hannu da kafa a daure! A karshe dai Allah ya fallasa su. Hukuncin kisasi ya fadi daga kaina. Na dawo duniya kai ka ce ranar aka haife ni….
Ina masu bukatu, ina masu fama da bakin ciki da damuwa, ina masu neman waraka… dss. Kun ga yadda addu’a take tasiri? Don haka kar ku sake. Wannan abu ya faru a Saudiyya kamar yadda Badr Almishary ya fada a kaset dinsa قرع لأبواب السماء. Shi kuma ya dakko daga littafin الفرج بعد الشدة

NAMadina

2 responses to this post.

  1. Posted by Abdullah Gambo on April 22, 2011 at 11:14 am

    Salam ! Na karanta wannan labari kuma na fa’idantu kwarai da gaske musamman wajen riko da Addu’a da kuma aiki da Gaskiya a dukkan alamura na rayuwa. Allah ya kara maku kwarin gwiwa. Amin.

    Reply

  2. A koda yaushe Allah yana bayan mai gaskiya, kuma addu’a takobin mumini ce
    na mutukar tausaya maka wata shari’ar sai a lahira

    Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Connecting to %s

Follow

Get every new post delivered to your Inbox.