Tambaya: “Malam menene hukuncin mai yi wa kishiyarta asiri tana bunnewa, kuma ta shiga tsakanin ‘ya’yanta da mahaifinsu, duk ta hanyar asiri”? Lubabatu Aliyu
Amsa: Yi wa wani asiri ta hanyar raba shi da wani da yake kauna da juyar da shi daga halin kauna da soyayya zuwa halin gaba da kiyayya, mummunan aiki ne, kuma nau’i ne na sihiri da ake kira ‘Sihrut Tafrik’, ko ‘As-Sarf’, wato sihirin rabawa tsakanin ma’aura, ko masoya, ko juya hankalin wani da susuta shi da zautar masa da hankalinsa daga wani abu da zai amfane shi zuwa mai cutar da shi, ko kuma daga kaunar abin kaunarsa ko iyayensa zuwa kyamars u da bijire musu. Akwai hanyoyi da dama da masu irin wannan mugun aiki su kan bi wurin cimma burinsu. Hukuncinsa a musulunci ya zo kurukuru a cikin al-Qur’ani mai girma inda Allah Madaukaki ya ambaci cewa kafirci ne, kuma malamai sun bayyana cewa duk wanda aka kama shi da irin wannan aiki to hukuncinsa shi ne alkali ya sa a kashe shi kisan kafirci da ridda ta barin addinin musulunci. Don haka ya wajaba wannan mata da duk wani mai mummunan aiki irin nata mai irin wannan bamagujiyar mugunta da bakar aniya, ya ji tsoron Allah ya tuba.
Lalata kishiya ta hanyar sihiri da raba ta da mijinta da shiga tsakaninta da ‘ya’yanta ba shi ne zai jawowa mai neman a yi mata sihirin alherin duniyar da take fada da kishiyar a kansa ya dawo gare ta ba. Arzikin duniya da na lahira duk a gun Allah yake, kuma babu wata hanya da za’a same shi sai da yardarsa. Yaya za a yi kuwa a ce mutum mumini ya jefa dan uwansa cikin damuwa, ya hana masa kwanciyar hankali; saboda kawai yana ganin cewa shi ne ya hana shi samun wani abin duniya ko kadaituwa da kaunar miji da soyayyarsa, kuma musamman ma a ce ta hanyar kafircewa da Allah da bautawa aljanu. Gaskiya wannan ba karamar tabewa ba ce, da kekasar zuciya, da rashin tsoron Allah, da fito-na-fito da kaddararsa, da rashin yarda da lamarinsa da dogaro da shi.
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam fa ya gaya mana cewa duk wanda ya je wurin boka ko dan duba, kuma ya tambaye shi kan wani abu har ya gaskata shi, to ya kafirta da abin da aka saukarwa (Annabi) Muhammad sallalllahu alaihi wa sallam.
A wata riwayar kuma ba za’a karbi sallarsa ta kwana arba’in ba. Wannan wanda ya gaskata kenan, ba tare da ya aikata sihirin ba. Kuma mafi rinjayen maganar malamai ita ce wannan tambayar da gaskatawar kafirci ne amma karami, ba mai fidda mutum daga musulunci ba. Amma mai aikata sihirin da mai ba da kudi da umurni a yi wa wani, kuma wanda ake ba wa umurnin ya cika sharuddan da aljanun ke nema a yi musu, to duk wannan aikinsu daya ne da shi bokan, kafircinsu na fita daga addini ne.
Babban abin da ke cikin wannan ma shi ne bautawa shaidanu da aljanu da yi musu da’a cikin abin da suke so, na yanke-yanke ko neman cika wasu sharudda masu dan karen wahala, da bada umurnin a je wani wuri a yi tono a binne. Wannan duk bautawa aljanu ne, bayan dumbin dukiyar da mutum zai halakar ta wannan mummunar hanya. Allah ya tsaremu.
Nasihata ga duk wanda Allah ya jarraba da wannan mummunar ta’ada ita ce ya gaggauta tuba zuwa ga Allah, kuma ya yi watsi da wannan shirka, kuma ya dogara da Allah bisa duk abin da yake nema, sannan ya ji tsoron cewa shi ramin mugunta in an tona shi ba a fa san wanda zai fara fadawa ba.
Daga cikin manyan hadurran da wannan mummunan aiki ya kunsa akwai:
1. Shirka da Allah da bauta wa aljanu. Kila wata ta ce ai ita wurin ‘malami’ kawai ta je ba gun aljan ba, to ya kamata ki gane cewa shi wannan da kike kira malami ba ya iya komai da kashin kansa sai ya yi da’a ga aljanu su kuma su ba shi umurni ya cika musu. Wannan da’ar da kuma cika sharuddan yadda aljanin ya nema shi ne bakar shirka, domin bautawa wanin Allah ne da neman yardarsa, wato sanya masa kishiya ta hanyar mika wani hakkin ibada zuwa ga waninSa, kamar yanka dabba domin waninSa ko da da sunan Allah ne, ko kuma cika wasu sharuddan da ba Allah ne Ya ce a cika su ba, musamman kuma wurin bautawa wanda za a yi wannan abu dominsa. Allah kuwa ya yi kashedi ga dukkan al’umma cewa “Duk wanda ya yi tarayya da Allah to lallai Allah ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka”.
2. Nisantar Allah. Duk wanda Allah ya jarraba da wannan kazamar ta’ada ya fi kowa nisa da ubangiji Mahalicci. Za ka same shi ba ya karatun Al-Kur’ani, ba ya zikirin Allah Ta’ala. Babu abin da yake ba shi sha’awa sai aikin da zai sa shadanin aljaninsa ya yarda da shi.
3. Rashin dogaro ga Allah. Mai sihiri ko kuma mai neman a yi masa sihirin bai yarda da cewa Allah ne abin dogaronsa ba, kuma shi ne mai taimakonsa ba, kuma shi kadai ne mai iya fitar da shi daga kowace matsala, ya kuma dauke masa kowa ce irin damuwa a zuciyarsa ko jikinsa ko abokin zamansa ko zuriyyarsa. Allah Madaukaki yana cewa: “Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa”.
Haba baiwar Allah, ga mahaliccinki, mai kowa mai komai, wanda ba bu abin da zai faru cikin halittarsa sai da saninsa da izininsa, wanda shi ne Mabuwayi, babu wanda ya gagare shi, babu mai iya ja da shi, ga shi da kansa yana ba ki alwashi cewa in kin dogara da shi to ya isar maki, wato ya isar maki daga wata cuta da ta shafe ki daga wani dan Adam ko aljan sai da izininsa, ya isar maki daga abokin gabarki, ya isar maki daga zaluncin azzalumi cikin sammai ko kassai, cikin duhun dare ko ido-na-ganin-ido, ya isar maki daga mai nufin jefa miki badin ciki a zuriyyarki ko a dukiyarki ta hanyar raba ki da abin kaunarki, miji ko da ko dan uwa ko makamantansu, ya isar maki daga dukkan sharri daga dukkan mai nufin sharri. Don Allah ki daure ki dogara da shi, za ko ki ga cika alkawari. “Wa ya fi Allah cika alkawari?” (Suratut Taubah: 111).
4. Cutar da dan uwa ko ‘yar uwa musulmi. Wannan kuma babban abu ne da ya shafi hakkin shi wanda aka cutar din, domin har abada Allah zai bi ki da alhakinsa har sai in ya yafe miki, bayan babban laifin shirkar da aka yi. Abu ne sananne cewa ba ya halatta mutum ya cutar da dan uwansa musulmi. Amma sihiri hanya ce mummuna ta rusa wannan babban umarni na shari’ah. Za ka ga mutum yana zaune tare da abokin zamansa, miji ko mata, ko da, ko uwa, ko uba, ko kaka, ko jika, ko koshin lafiyar da Allah ya hore masa, ko dukiyar rufin asiri da Allah ya ba shi, ko aikinsa da ya ke samun abincinsa ta hanyarsa, ko kasuwancinsa na halaliyarsa, ko mulkin da Allah ya ba shi amanarsa, amma haka kawai sai wani ya bullo cike da hassada da bakin ciki da mugunta, ya hada kai da boka mai sihiri tare da ba shi wani abin duniya don su taru su bautawa wani mugun aljani domin raba wannan bawan Allah da abin da yake so din nan. Duk wanda ya yarda da Allah da Ranar karshe to ya tabbatar da cewa zai hadu da Allah Madaukaki, kuma zai yi masa ukuba mai tsanani akan cutar dan uwansa musulmi ta hanyar sihiri, kuma ya sani cewa in ya tuba ma anan duniya tsakaninsa da Allah to Allah mai gafara ne kuma zai gafarta masa hakkin da yake tsakaninsa da shi na shirkar da ya yi, da tsafin da ya yi, amma in ya bari har ya mutu a kan haka, to shi da aljanna fa faufau, kuma ba zai fita daga Jahannama ba. Sannan kuma hakkin dan uwansa musulmi na cutar da shi da raba shi da abin kaunarsa, to Allah ba zai gafarta masa ba sai ya nefi yafewarsa daga wanda ya cuta din.
5. daurewa wannan karyar gindi ta hanyar karawa wadannan miyagun bokaye wadanda jahilai suke kira ‘malamai’, da samar musu sanadin rayuwa. Wannan kuwa abu ne da yake kara karfin wannan shirkar a cikin al’umma. Da a ce daukacin mutane za su yi watsi da bokaye, su kuma daina zuwa wurinsu, da ba su kudi ko wani abin duniya a kan wannan mugunta da suke yiwa mutane, to hakika da an dode wannan babbar kofar sharri, sai fa idan za su ci gaba da bautawa aljanun nasu, su kuma aljanun su sato musu dukiyar mutane.
6. Yada gaba tsakanin al’umma. Lallai sihiri babbar hanya ce ta hada mutane gaba da kiyayya. Domin duk wanda ya san kina ko kana da hanu wurin lalata masu dan uwa ko abin kaunarsa to gaba ta kullu kenan tsakaninku.
7. Yada firgici da tsoro tsakanin mutane, ta yadda zai zama in sihiri ya yadu tsakanin al’umma, to komai kankantar abin da ya faru ga mutum ko wani nasa sai ya fara zaton cewa sihiri wani ya yi masa, tun bai yi bincike ko ya je wurin likita ya rasa magani ba.
8. Taho-mu-gama da fushin Allah Madaukaki, domin duk al’ummar da ta fada cikin wannan mummunan hali, kuma malamanta suka yi shiru ba su fadakar da mutane kan hadarinsa ba, to fushin Allah zai fada mata kuma ta rasa albarka, ta rasa zaman lafiya.
Sabubban Yawaituwar Sihiri Da Fantsamarsa Cikin Al’umma
*Raunin imani; Allah Madaukaki na cewa : “Duk wanda ya yarda da Allah to Allah zai shiryar da zuciyarsa”. Daga an ce imani da Allah ya raunana, kuma kaunar taimakonsa da sa ran kariyarsa ta yi sakosako a zuciya, kuma tsoronsa ya yi karanci, dogaro da shi ya raurawa, to za ka ga mutane suna dunguma zuwa turakun bokaye da masu sihiri, su kuma su kara musu nisa daga Allah.
*Jahilcin mutane da hukuncin shari’ar Allah Madaukaki da hanin da ta yi kan sihiri, da kuma jahilcinsu da musulunci kansa da sakon Annabawa da Manzannin Allah Madaukaki ya sa suna kiran matsafa da bokaye da masu sihiri da sunan malamai. Shi kuma aikin sihiri ana kiran sa da sunan aiki ko kuma addu’a ko kuma ‘istihara’, da kuma jahiltarsu da hakikanin wadannan matsafa.
*Ruduwar mutane a zamanin yanzu da rayuwar duniya da tara abin duniya. Duk fadi-tashinsu shi ne: ina zaka? Kudi, ina ka fito? Kudi, kuma mafi yawansu, suna neman kudin ne fiye da bukatunsu na yau da kullum. Ayyukan alheri sun yi karanci, riko da addini ya yi sako-sako, sabon Allah shi ne abin yin takara. Fasikai su ne masu shahara, malamai su ne abin wulakantawa. Sai ya zama kullum mutane cikin matsaloli, da damuwa, da rashin natsuwa da kwanciyar hankali, da yawan munin zato ga mutane, ciwukan zuciya sun yi cunkus a kirazan mutane, kuma suna zaton cewa wadannan matsalolin da damuwar da cutukan ba su da magani sai an je wurin ‘malami’ ya yi wa mutum ‘aiki’, wato ya yi masu asiri, ko dai ya cuci wani, ko kuma a yi masa tsafi da wani bangare na jikin wani dan Adam don ya yi kudi. Wannan yawan sabon Allah da ruduwa da duniya ya jawo cewa mafi yawan gidajen musulmi makwanci ne na shaidanu, wato aljanu, sabo da yawan tara kayan sabon Allah, hotunan batsa da kallon su, kayan wake-wake, fina-finan batsa da watsa al’umma, tsere wurin koyi da kafirai a kowane fage. Kuma mutane suka yi nesa da karanta Al-kur’ani, ko zikirori da suka zo daga Annabin rahama, ko addu’o'in kawar da aljanu da tasirinsu. *Raunin malamai wajen aikinsu na magadan Annabawa wajen fadakar da jama’a da tsoratar da su azabar Allah musamman a kan shirka da tsafi da sihiri, har ta kai wasu ba su ma san cewa wannan abu kafirci ba ne, wasu kuma suna ganin ai in babu sihiri ma wani abin duniyar nasu ba zai samu ba, kamar masu mulki da masu kudi.
Wasu daga hanyoyin Fita Da Kuma Kariya Daga Wannan Musifa
Daga ciki akwai: Jaddada imani a zukatan muminai, da komawa zuwa ga Allah da dogaro da shi, da tabbatar da tauhidi da kadaita Allah cikin bauta, da nesantar duk abin da ke da alaka da shirka. Kada kuma musulmi ya manta da fadin Allah cewa: “Kuma ba su cutar kowa da shi (sihirin) sai da izinin Allah”. Allah ya kare mu Amin summa Amin. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Dr. Abubakar Muhd. Sani B\Kudu