Yana daga cikin abin da duk wani dan adam yake nema a rayuwarsa ta duniya, samun albarka, domin da haka ne zai samu rayuwa ingattacciya , mai cike da dimbin nasara da ci gaba, kuma hanya ce da za ta jawo wa ragowar iyalansa da ma dukkan zurriyarsa samun albarka.
Duba da mahimmancin wannan al’amari naga dacewar in dan yi mana tsokaci game da abubuwan da suke jawo albarka a rayuwarmu ta yau da kullum, dafatan Allah ya amfanar da mu, ya kuma datar da mu izuwa abin da yake shi ne dai dai.
(1)Fara komai da ambaton sunan Allah :
Yana daga cikin abubuwan da suke jawo albarka a rayuwar mutum fara komai da ambaton sunan allah, Manzon Allah (S.A.W) Idan mutum ya shiga gidan sa, yana mai ambaton Allah yayin shiga, da kuma lokacin cin abinci, shaidan zai cewa abokansa : ba ku da gurin kwana da kuma gurin cin abinci a yau”.
Don haka ka ambaci sunan Allah, domin ambaton Allah shine abinda ya kamata musulmi yayi kafin kowane aiki, haka ma har a wajan tarawa da iyali, ( jimai ) anso ka ambaci Allah kana mai cewa : ” Allahumma jannibnas-shaidana, wa jannibus-shaidana ma razaktana”, to idan Allah ya azurta su da da a wannan daren, to hakika zai albarkace shi, domin duk alamarin da mabudinsa ambaton Allah ne, to kuwa albarka ba ta kaurace masa
(2) Jin tsoron Allah da kuma imani da shi :
Allah madaukakin sarki yana fada a cikin Alkur’ani mai girma: (( Lalle da mutanen alkaryu sun yi imani, kuma sun yi takawa, lallai da mun bude albarkatu akansu daga sama da kasa)) (Al-aaraf: 96). Kuma hakan zai kara fitowa fili, a fadin manzon Allah (S.A.W) inda yake cewa: “Muminin bawa mai takawa, da sannu zai rika samun albarka a rayuwarsa, da kuma cikin iyalinsa da ‘ya’yayensa”.
(3)Tsayar da sallah :
Allah (S.W.T) yana cewa : (( ka umarci iyalinka da yin sallah, kuma ka yi hakuri a kanta, Ba mu tambayar ka wani arziki, mu ne muke arzuta ka, kuma akiba mai kyau tana ga masu takawa)) (Daha : 132).
(4)Dogaro ga Allah :
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : ” Da a ce kuna dogaro ga Allah dogaro na gaskiya, da ya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana fita da safe alhalin cikinsa ba komai (mai jin yunwa), sannan ya dawo cikinsa yana koshe”.
(5)Yawaita karatun Al qurani :
Kamar yadda Allah (S.W.A) Yake fada ((kuma wannan littafi ne Mun saukar da shi mai albarka ne)) (An am: 92), domin shi Alkura’ni, Allah ya sanya shi ya zamanto mai albarka ga wanda ya bi koyarwarsa, ya ke yawan karanta shi, yake kuma amfani da hukunce hukuncensa. Saboda haka ne Annabi (S.A.W) ya ce: “Gidan da ake karanta Alkur’ani a cikinsa, mala’iku suna zama a cikinsa, shaidanu kuma na kaurace masa, kuma albarka da alkhairi suna yawaita da kuma fadada a wannan gidan”.
(6)Yawaita Istigfari :
Istigfari wani babban dalili ne da yake samar da albarka, kamar yadda manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya lazimci istigfari Allah zai sanya masa kowane kunci ya zamo masa sauki, kuma ya sanya masa akowace irin damuwa, wata mafita, kuma ya albarkace shi ta in da ba (9)Yawaita yin sadaka : Annabi (S.A.W) ya ce: “Sadakar da mutum yake boye ta yayin bayarwa, tana gusar da fushin Ubangiji”.
(10) Haduwa guri guda yayin cin abinci :
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : ” Ku ci abinci tare; ka da ku rarrabu, domin ita albarka tana tare da jama’a, domin abincin mutum daya zai ishi mutum biyu, abincin mutum biyu zai ishi mutum uku “. Haka nan kuma akwai wasu nau’ikan abinci da suke da albarka,domin haka ana so mutum ya rika yawan cin su, ko ya samu dacewa, su ne kamar haka: Nono, Zuma, Dabino, da kuma Man Zaitun.
(11)Yin Sahur lokacin yin azumi:
Annabi (S.A.W) ya fada : “Ku yi sahur domin a cikin yinsa akwai albarka” , abin da ake nufi da albarka a nan shi ne samun lada, sannan kuma dan mutum ya samu nutsuwa a yayin azumin
(12)Yin amfani da ruwan zam-zam :
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Hakika ruwan zam-zam mai albarka ne, kuma tabbas abinci ne ga mai jin yunwa, kuma magani ga mara lafiya”.
(13)Dacewa da Daren Lailtul Kadri:
Allah madaukakin sarki yana cewa: ((Hakika mun saukar da Alkur’ani a dare mai albarka)) (dukhan : 3), wato Lailatul Kadri, domin alkhairinta ya fi na wata dubu .
(14)Halartar masallacin idi :
Domin ranakun karama da babbar sallah ranaku ne masu albarka; an karbo daga Ummu Adiyyah Allah ya yarda da ita tana cewa: “Mun kasance ana umartar mu (mu taron mata ) da mu fita ranar idi, mace budurwa ma ana so ta fito daga dakinta, mace mai ala’ada ma haka, sai su kasance a bayan maza, suna masu neman albarkar wannan rana da kuma tsarkinta” .
(15)Sa da zumunci :
Manzon Allah (S.A.W) ya na ce wa: ” Sa da zumunci, tare da kyawawan halaye, hadi da kuma kyakykyawar makotaka, suna gina gidaje (wato suna sanya tare da kara albarka a gidaje), kuma suna jawo albarka a rayuwar mutum”.
(16) Sammako wurin fita neman arziki:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah ya yi Albarka ga alummata ya yin da suka yi sammako wurin neman arzikinsu”. Shi ya sa za ki ga yawancin masu arziki da aka tambaye su game da sirrin arzikinsu sai suka ce sammako wurin neman arziki, daga cikinsu akwai Sakhru al- ghamidi, wanda yake cewa: ” yayin da na ji hadisin Manzon Allah (S.A.W) game da yin sammako wurin neman arziki, sai na wayi gari ina fita kasuwancina a farkon yini, kuma an rawaito cewa ya samu arziki mai yawan gaske.
(17) Yin aure:
Allah (S.W.T) yana cewa : ((Ku aurar da gwauraye daga gareku, da salihai daga bayinku, da kuyanginku, idan sun kasance matalauta, Allah zai wadatar da su daga falalarsa)) ( Nur : 32 ), kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Ku nemi samun arziki ta hanyar yin aure ” amma fa ga wanda ya samu halin yin auraen.
Zainab Ja’afar Mahmud Adam