YAUSHE NE 1000000=1000???!!! (KALU-BALE GA WASU IYAYE)

Wata rana wani matashi ya dawo gida sai ya ga tarin jama’a a kafar gidansu, gabansa ya yanke ya fadi; ya dauka ko rasuwa aka yi, daga baya sai ya ga ashe wai kannensa biyu mata ake daurawa aure, bai san ma an ba da su ba ballantana daurin aurensu! da ya yi magana sai aka ce masa: “To in an gaya maka me za ka iya yi, (Shi da yake fama da taluci me ya yi wa kansa ballantana wasu)?!” Bbai san lokacin da hawaye ya fara shatato masa ba, ya fito waje hawaye shabe-shabe yana cewa: “Allah ya raba mu da talauci!”

Bugu da kari, wata baiwar Allah ita ma ta koka da yadda mahaifanta suke watsi da ita, saboda mijinta ya talauce! Ta ce: A da, da suke da abin hannunsu, komai sai abin da ta ce a gidansu, musamman ma ga shi ita ce babba a gidan, amma da “yau” ta ci su da yaki sai ya zamana, wani lokaci ko sa ranar kannenta da suke ciki daya sai dai ta ji a sama! Ta ce wannan abu yana damu na fiye da misali, a ce talauci ya zabge mata daraja haka a idon iyayenta!

Shi kuma wannan wani karamin ma’aikaci ne, kwatsam sai ya bar wannan aiki ya buge da wata kaskantacciyar sana’a da yake zaton zai yi saurin samun kudi ta ita, da aka tambaye shi, sai ya ce, ya yi haka ne saboda gudin fushin mahaifiyarsa, saboda kannensa da yayyensa duk mawadata  ne,  don haka idan sha’ani ya taso– kamar biki ko suna– su kan ba ta kudi da yawa, shi kuma abin da yake iya ba ta bai taka kara ya karya ba, ita kuma sai ta yi ta fada har barazanar tsine masa take yi in bai yi mata irin yadda ‘yan’uwansa suke yi mata ba, ya yi mata duk wani bayani amma bata yarda ba, shi ya sa ya yanke shawarar shiga wannan sana’a takaskanci ko shi ma ya samu kudi don ya kara kima a idon mahaifiyarsa, kuma ya huta da zagi da tozartawa a gaban kannensa ba iyaka!

Dorawa ‘ya’ya abin da ba za su iya ba, ko fifita wasu akan wasu don kawai suna da kudi, ko suna auren masu da-akwai, ya sabawa koyarwar manzon Allah (SAW).

Ya zo a cikin (Bukhari da Musulim) Wata rana wani sahabin manzon (SAW) ya ba wa dansa wata kyauta, sai ya zo ya ce da Annabi ya yi masa shaida a kai, sai  ya ce masa  ragowar ’ya’yanka ma duk ka yi musu irin wannan kyauta?”

Sai ya ce A’a. sai ya ce:

“Kuma kana son su yi maka biyayya kamar yadda zai maka?

Sai ya ce: Sosai kuwa!

Sai ya ce masa: “Ku ji tsoron Allah ku yi adalci tsakanin ’ya’yanku!” a wata ruwayar: “Kar ka kuskura!” a wata ruwayar “wannan kyautar a fasa ta!” a wata ruwayar “Ka je wani ya yi maka shaida ni ba na shaida akan zalunci!” shikenan sai ya fasa.

Kuma a hankalce idan muka duba za mu ga  da wanda ya mallaki milyan goma, ya bai wa mahaifansa kyautar milyan daya, da wanda ya mallaki dubu goma ya ba su kyautar dubu daya ba wani bambanci tsakaninsu; don kowanne 10% na dukiyarsa ya ba su!

Nura Abdullahi Madina (NAMadina)

 

One response to this post.

  1. Allah ya saka da alkhairi yakuma rabamu da talauci

    Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Connecting to %s

Follow

Get every new post delivered to your Inbox.