KARATUN JAMAI’A

       Jami’a tana daya daga cikin wurare da suke ba wa mutum ‘yanci, ma’ana ba mai takura masa, kuma ba a damu da abin da yake yi ba. Amma kuma idan aka duba jami’a wuri ne mai hadarin gaske in dai har mutum bai yi mata da gaske ba. Jami’a mahada ce ta mutune daban-daban, daga wurare daban-daban wadanda tarbiyyarsu da al’adunsu suka bambanta; saboda haka ya kamata dalibai musamman sababbi su lura da wadanda za su zauna tare a matsayin abokai, kawaye ko makamancin haka; don akwai mutane da za su batar da mutum in har bai yi a hankali ba, ko kuma shi bai yi kokarin jawo su zuwa hanya ta daidai ba; domin wasu manufarsu ta shiga jami’a ba wai samun ilimin da suka je nema ba ne, a’a, su dai kawai su sami yadda za su yi su lalata tarbiyyar ‘yan uwansu matasa ne. A yanzu da yawa daga cikin dalibai suna jami’a, amma ba su da wata manufa mai nagarta ta kasancewarsu a cikinta, da za ka tambayi wani dalibin ka ce me zai karanta a jami’a, sai ya ce: Ai komai aka ba shi karantawa zai yi. Abin tambaya a nan shi ne: Shin wai yin jami’ar ne ya zama dole, ko kuwa manufa ce babu! Ya kamata mutane su san cewa yin jami’a ba wai zama dole ya yi ba, sai dai don manufar samun ilimi mai nagarta domin taimakon addini da al’ummar musulmi, musamman saboda kalubalen dake fuskantar musulmi ta fuskoki daban-daban a cikin gida da waje. In aka duba bangaren mata misali, na ha]u da wasu sa’o’ina da ba su sami kyakkyawar shawara akan abin da ya kamata su karanta ba, a cikin ire-iren wadannan dalibai sai ka ga mace ta je ta dauki kamar Civil Engineering; (abin da ya kunshi koyar da yadda ake yin tituna, gadoji, dss). Ko kuma irin su Political Science da makamantansu, ni kuma ina ganin cewa gudunmawar da mace za ta bayar ta irin wad annan kwasa-kwasai ba su dace da dabi’ar ‘ya mace ba. A halin da muke ciki a yau, al’ummarmu tana bukatar mata wa]anda suka kware a fannonin aikin asibiti kamar likitanci, nurse da unguwarzoma da makamantansu; saboda haka ne ma nake da burin karanta aikin likita, kuma nake fatan Allah ya cika min burina, ya taimakamin akan samun nasarar shiga da kwarewa a wannan fannin.

FATIMA HUSAIN FALAKI

Published in:  on April 7, 2009 at 12:34 pm Leave a Comment

The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2009/04/07/karatun-jamai%e2%80%99a/trackback/

RSS feed for comments on this post.

Leave a Comment