A GAGGAUTA KAI MACE MAI NAKUDA ASIBITI !!!

Tambaya: Menene mahimmancin mace ta haihuwa a asibiti, kuma shin haihuwar gida tana da wata illa?
Amsa: Na farko dai ba’a cewa an haihu lafiya sai an yi kwana arba’in da haihuwar.
Na biyu ita haihuwa ba yadda za’a yi a hankalaci cewa za’a samu matsala da ita.
Na uku: A asibiti ne ake da ma’aikata kwararru wadanda suke sanin matsalar haihuwa idan ta faru, ko za ta faru; don haka idan aka haihu ko aka fara nakuda a gida, matsala tana iya faruwa, inda ba wanda zai fahimce ta har sai ta yi tsamari, sannan in an je asibiti sakamakon ya zamo abin da ba’a bukata. Amma al’adarmu ta cewa idan mace ba ta haihuhu a gida ba, ana ganin kamar nakasa ce, ko gajiyawa, don haka za ta yi iya kokarinta ta ga ta haihu a gida, ba tare da ta yi la’akari da hadarin da take sa kanta da kuma jairirinta a ciki ba.
    Ba’a son nakuda ta fuce awa 12, kuma ya kamata a gane cewa, mai ciki za ta iya samun ciwo wanda ita a gunta nakuda ce, amma idan aka zo asibiti sai a ga nakudar ba ta tabbata ba, shi ya sa za ka ji wasu suna cewa sun yi kwana hudu ko biyar suna nakuda, kuma sun haihu lafiya. Idan nakuda ta wuce awa 12, jaririn, da uwar suna iya shiga wani mugun hali, irin wannan ne zai janyo ka ga an haifi da babu rai, ko kuma ya fara farfadiya tun yana yaro, ko ya zama wani sususu, sannan idan wadannan ba su samu yaro ba, zai iya tashi dakiki.
     Uwa kuwa mahaifarta za ta iya fashewa idan tsohowar haihuwa ce, idan kuma haihuwar fari ce za ta iya haduwa da yoyon fitsari, ko ma har da na bayan-gida, ko kuma bayan ta haihu ta ci gaba da zub da jini wanda zai iya kaiwa ta rasa ranta. Don haka idan mace ta yi nakuda a gida, cikin biyu ne; Tana iya haihuwa lafiya, to amma idan ta shiga matsala ba za’a gane matsalar da wuri ba, lokacin da za’a zo asibiti kuma ta galabaita, sannan kuma a karshe ko a rasa ta, ko a rasa dan dake cikinta, ko a rasa su gabadaya.

Dr. Idris Sulaiman Abubakar.
(Aminu Kano Teaching Hospital)

Published in:  on March 23, 2009 at 9:21 am Leave a Comment

The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2009/03/23/a-gaggauta-kai-mace-mai-nakuda-asbiti/trackback/

RSS feed for comments on this post.

Leave a Comment