ALLAH YA GAFARTA WA WANCE !!!

Imamu Ahmad (Allah ya ji kansa) bai yi auren fari ba sai da ya kai shekara arba’in; da ya tashi aure sai ya fara tantance gidan da ya kamata ya hada zuriya da su, sai aka ce masa akwai ‘yan mata biyu a gidan, daya kyakkyawa ce, dayar kuma idonta daya, sai ya ce wacce ta fi hankali? sai aka ce mai ido dayan, sai ya ce: ita za ku aura min. Zamansu ya yi dadi sosai. Bai yi wani auren ba sai da ta rasu.

 Yake cewa: Almarwazi daya daga cikin daliban imamu Ahmad (Allah ya ji kansa) ya ce: wata rana imamu Ahmad ya ambaci iyalinsa bayan ta rasu sai ya ce: Allah ya gafarta wa wance, shekararmu ashirin tare amma ko sabani ba mu taba ba.

 

Published in:  on March 27, 2009 at 8:24 pm Leave a Comment

MAKKA BABBAN GARI HAR DA GONAR LANTARKI!!!

In ji wani dan Fulani lokacin da yaje kasa mai tsarki domin yin aikin hajji bayan jirginsu ya sauka a filin jirgin sama na sarki AbdulAziz dake Jidda (kasancewar akwai fitulu da dama akan doron titin filin jirgin).

Published in:  on at 8:10 pm Leave a Comment

AN YI MUSU BUSHARA DA ALJANNA TUN SUNA DUNIYA !!!

SUNAYEN SAHABBAI GOMA DA AMBATONSU YA ZO A HADISI GUDA AKA YI MUSU BUSHARA DA ALJANNA TUN SUNA DUNIYA:

1. Abubakar Assiddik ( Allah ya yarda da shi).

2. Umar Alfaruq (Allah ya yarda da shi).

3. Usman Ibn Affan (Allah ya yarda da shi).

4. Aliyu Ibn Abi Dalib (Allah ya yarda da shi).

5. Abu Ubaida Ibnul Aljarrah (Allah ya yarda da shi).

6. Abdul Rahman Ibnu Auf (Allah ya yarda da shi).

7. Azzubair Ibnul Awwam (Allah ya yarda da shi).

8. Dalhatu Ibnu Ubaidillah (Allah ya yarda da shi).

9. Sa’ad Ibnu Abi Wakkas (Allah ya yarda da shi).

10. Sa’id Ibnu Zaid (Allah ya yarda da shi).

 

Published in:  on at 7:08 pm Leave a Comment

MADUGUN MASU RAYUWA DON SU CI

Mutum mai hankali yana ci ne don ya rayu, amma bayin ciki irin su Ash’abu suna rayuwa ne don su ci! 

Ash’ab wani mutum ne da labarawa suke ba da misali da shi wurin kwalama da babakeri, da hadama da mutunta abinci sama da komai.

Daga cikin labarinsa:

¨ Wata rana budurwarsa ta tambaye shi ya ba ta kyautar zobe don ta rika tunawa da shi, sai ya hana ta, ya ce mata idan kina son tunawa da ni, ki rika tunowa kin tambaye ni zobe na hana ki!

¨ Ya taba yi wa wasu yara karya ya ce ana rabo a gidan wane, da ya ga suna ta tafiya can, sai ya ce a ransa kar fa a ce da gaske ne, sai ya ruga don ya riga su.

¨ Yana sahun sallah da wani shugaba, sai shugaban ya yi tusa daraaam sai shi kuma Ash’ab ya kama hanji ya fita kamar ya yi habo, da shugaban nan ya koma gida sai ya bi shi ya ce ba ni ladana, ya ce wane lada? Ya ce ladan tusar da ka yi; ko ka biya ni, ko in je gari in yayata in ce wannan tusar da ma kai ka yi ba ni ba!

Published in:  on March 26, 2009 at 11:33 am Leave a Comment

A GAGGAUTA KAI MACE MAI NAKUDA ASIBITI !!!

Tambaya: Menene mahimmancin mace ta haihuwa a asibiti, kuma shin haihuwar gida tana da wata illa?
Amsa: Na farko dai ba’a cewa an haihu lafiya sai an yi kwana arba’in da haihuwar.
Na biyu ita haihuwa ba yadda za’a yi a hankalaci cewa za’a samu matsala da ita.
Na uku: A asibiti ne ake da ma’aikata kwararru wadanda suke sanin matsalar haihuwa idan ta faru, ko za ta faru; don haka idan aka haihu ko aka fara nakuda a gida, matsala tana iya faruwa, inda ba wanda zai fahimce ta har sai ta yi tsamari, sannan in an je asibiti sakamakon ya zamo abin da ba’a bukata. Amma al’adarmu ta cewa idan mace ba ta haihuhu a gida ba, ana ganin kamar nakasa ce, ko gajiyawa, don haka za ta yi iya kokarinta ta ga ta haihu a gida, ba tare da ta yi la’akari da hadarin da take sa kanta da kuma jairirinta a ciki ba.
    Ba’a son nakuda ta fuce awa 12, kuma ya kamata a gane cewa, mai ciki za ta iya samun ciwo wanda ita a gunta nakuda ce, amma idan aka zo asibiti sai a ga nakudar ba ta tabbata ba, shi ya sa za ka ji wasu suna cewa sun yi kwana hudu ko biyar suna nakuda, kuma sun haihu lafiya. Idan nakuda ta wuce awa 12, jaririn, da uwar suna iya shiga wani mugun hali, irin wannan ne zai janyo ka ga an haifi da babu rai, ko kuma ya fara farfadiya tun yana yaro, ko ya zama wani sususu, sannan idan wadannan ba su samu yaro ba, zai iya tashi dakiki.
     Uwa kuwa mahaifarta za ta iya fashewa idan tsohowar haihuwa ce, idan kuma haihuwar fari ce za ta iya haduwa da yoyon fitsari, ko ma har da na bayan-gida, ko kuma bayan ta haihu ta ci gaba da zub da jini wanda zai iya kaiwa ta rasa ranta. Don haka idan mace ta yi nakuda a gida, cikin biyu ne; Tana iya haihuwa lafiya, to amma idan ta shiga matsala ba za’a gane matsalar da wuri ba, lokacin da za’a zo asibiti kuma ta galabaita, sannan kuma a karshe ko a rasa ta, ko a rasa dan dake cikinta, ko a rasa su gabadaya.

Dr. Idris Sulaiman Abubakar.
(Aminu Kano Teaching Hospital)

Published in:  on March 23, 2009 at 9:21 am Leave a Comment

HUKUNCIN KORAR YARO DAGA MASALLACI !!!

Tambaya:    Menene hukuncin korar YARO daga masallaci, ko daga sahun farko don BABBA ya maye gurbinsa? **   

                                                                                         Ba Suna

 Amsa:   Idan yaro ba ya cutar da kowa – da aikinsa ko maganarsa to bai halarta a fitar da shi daga masallaci, ko a dawo da shi sahun da yake baya da wanda yake tsaye a cikinsa ba, koda kuwa a bayan liman yake kai tsaye; saboda a sunna wanda ya fara zuwa wuri shi ya fi cancanta da shi, kuma Annabi (SAW) ya hana mutum ya tashi danuwansa daga wurinsa shi don ya zauna a wurin, masallatai kuma gidajen Allah ne, bayin Allah (baba da yaro) daya suke a cikinsu. Hadisin da Annabi (SAW) yake cewa “Masu hankalin cikinku ya zama su suke biye da ni a sahu” kuwa ba ya nuna a rika korar yara daga sahun farko koda daga su sai liman kamar yadda wasu malamai suka dauka. Wannan hadisi yana kwadaitar da manyan ne kan su je masallaci da wuri don su samu tsayawa a bayan liman. Sannan korar su daga sahun da suke zuwa na baya zai haifar da matsaloli kamar: Taruwarsu a wuri guda wanda wannan zai sa su yi ta wasa da hayaniya lokacin sallah Za su rika kin Masallaci Za su rika in masallata, musamman mai korar su.

Shiekh Ibn Uthaimin

Published in:  on March 21, 2009 at 12:10 pm Leave a Comment

SHIN A SHIRYE KUKE KUWA?

 ¨ Shin kun shirya tafiya garin da ba dawowa?

¨ Shin kun shirya tafiya gidan da sai an cika jaka a ke zuwa?

¨ Shin kun shirya amsa tambayoyin da basu da iyaka?

¨ Shin kun shirya barin masoyanku?

¨ Shin kun shirya sa fararen kaya wadanda ba dugon baki a jikinsu?

¨ Shin mai kuka tanadarwa bakonku wanda ba zai yi sallama ba in zai shigo?

¨ Shin kun tanadi guzurin tafiya na inda bakon zai kai ku? Wal’ iyazu billah wa inna lillahi wa inna ilaihi raji‘un Wayyo mutuwa! Mutuwa!! Mutuwa!!!

Allah ka sa mu cika da imani 

 Daga:

SAUDA M. SANI GGSS Garko

 

 

 

 

Published in:  on March 18, 2009 at 2:25 pm Leave a Comment

Uwar gida fara daga yau

Published in:  on at 10:53 am Leave a Comment