Wata rana an yi wani tsoho wai shi barau,rannan zai yi barci sai ya fesa maganin sauro a dakinsa,da ya tabbatar maganin ya kashe sauron, sai ya kwanta,to yana cikin barci sai wani rigimammen sauro ya zo yana mai kuka a kunne.sai yace a ransa;[wannan sauron sai na yi maganinshi]. sai ya dauko maganin ya fesa a kunnensa, yace na dai yi maganinka.
Kaga wata shiririta a wajen dan tsoho,wannan fesa maganin da yayi a kunnensa shi yasa aka bashi gado a asibiti na kwana biyu har da karin ruwa