MAGANIN SAURO

Wata rana an yi wani tsoho wai shi barau,rannan zai yi barci sai ya fesa maganin sauro a dakinsa,da ya tabbatar maganin ya kashe sauron, sai ya kwanta,to yana cikin barci sai wani rigimammen sauro ya zo yana mai kuka a kunne.sai yace a ransa;[wannan sauron sai na yi maganinshi]. sai ya dauko maganin ya fesa a kunnensa, yace na dai yi maganinka.

Kaga wata shiririta a wajen dan tsoho,wannan fesa maganin da yayi a kunnensa shi yasa aka bashi gado a asibiti na kwana biyu har da  karin ruwa

Published in: on September 19, 2008 at 4:37 pm Leave a Comment

Muhimmancin Sahur

Cikin abubuwan da mai Azumi ya kamata  ya lura da su akwai Sahur don fadin Annabi Muhammad(S.A.W);”kuyi sahur don a cikin sahur akwai Albarka”

Haka zalika Annabi(S.A.W) ya ce [banbancin azuminmu da azumin masu littafi shi ne cin sahur]

masu littain nan sune yahudu da nasara, don sun kasance basa cin sahur,sai dai su ci abinci tun da dare sannan su tashi da azumi da wannan abincin da suka ci

Published in: on September 6, 2008 at 12:53 pm Leave a Comment

Addu`ar Shan Ruwa

Yana daga cikin sunnah idan Mutum ya zo bude baki yace:”zahabazzama`u wabtallatil uruqu wasabatal ajru insha`allah”

Published in: on at 11:33 am Leave a Comment

Tona asirin Iyali

Wani bawan Allah daga cikin nagartattun bayin da suka shude yayi nufin sakin matarsa,sai wasu suka je suka tambaye shi “kai kuwa mai yasa za ka sake ta? sai yace “mai hankali baya tona asirin matarsa!” bayan ya sake ta, sai suka kuma zuwa suka tambaye shi cewa mai yasa ya sake ta? sai yace,”mai ya hadani da matar wani!”

Published in: on September 5, 2008 at 4:38 pm Leave a Comment