Assalamu alaikumu
Sunana Yayaha Abdullahi ina matukar sha’awar karanta likitanci, don haka don Allah wadanne shawarwari likita zai ba ni, kuma ina son in zai yiwu a yi min bayani filla-filla na bangarorin da lokunan da likitanci ya kunsa don na zabi bangaren da na fi sha’awa, kuma zan iya shi yadda ya kamata.
Na gode Allah ya saka da alheri
ws
***
Wa Alaikumusssalam Warahmatullah,
Wanda duk yake sha’awan aikin likita, dole ne tun daga sakandare ya dage ma English, Mathematics, Chemistry, Biology da Physics. A o’ level ba’a yafe ma ko daya. A a’ level kuma za ka yi Chemistry, Biology da Physics. Physics din ka iya yin wani darasi maimakon shi.
Inka shiga jami’a, aikin likita zaka koya a dunkule ta yanda zaka iya aiki a ko wani fanni na aikin likita amma ba a matsayin kwararre ba. Kwarewa yana daukan akalla shekaru hudu bayan biyar na jami’a.
Filayen kwarewa suna da yawan gaske amma a dunkule akwai wadanda suke alaka da duba marar lafiya kamarsu duba mata (Obstetrics & Gynaecology), duba yara (Paediatrics), aikin fida (Surgery) da duba cututtukan ciki (Internal Medicine). Wadannan ma akwai raberabensu na zurfafa kwarewa ta inda za ka zabi gaba ka kware kamar su kwakwalwa, zuciya, huhu, hanta, koda, ’kashi, jini da sauransu.
Akwai kuma likitoci da ke kwarewa a fannin bincike ba tare da sai sun ga marar lafiya ba. Suke da hakkin duba hoto ( X ray, Scan da sauransu), jini, fitsari, bayan gari, kaaki da kuma guture na wani gaba da aka samu ta hanyan aiki da sauransu.
A takaice abun da zan iya cewa kenan sai dai shawara kawai, shi aikin likita yana bukatan juriya da kula.
Allah ya sa mu dace.
Wassalam.
Dr. Abubakar Said Yagi