Annabi (SAW) ya ce kar ku yi addu’a ga kawukanku, ‘ya’yanku da dabbokinku in ba ta gari ba, kar ta dace da lokacin karbar addu’a…
Wata rana wani mutum ya kawo wa Abdullahi ibn Mubarak karar wani dansa, sai ya ce masa: Ka tsine masa ne? sai ya ce: ee! sai ya ce: to ai kai ka bata shi!