Dana yana zagi na a gaban baki ya zan yi da shi

Yana daga cikin abubuwan da yara suke samun kansu a ciki, yayin matakin yarinta   shine dabi`ar zagi, kuma wannan dabi`ar takan samu ne sakamakon wasu abubuwa da suke bujurowa yaro a wannan mataki da yake ciki, don haka wannan yaron a bisa yadda akayi bayani zagin bai zamo masa dabi`a ba, ta yadda ko yaushe yake yinsa, sai dai kawai yana yinsa ne a wani guri mai matukar girman gaske, don haka sai a bi wadannan matakan kamar haka :

 

1- Lallai ne a samu lokaci a ringa zama da wannan yaron domin kokarin sanin abubuwan da suke damunsa, da kuma kokarin nuna masa baci da munin wannan dabi`a da yakeyi yayin da yaga baki a gidansu.

2- A wannan mataki da yara suke ciki sukan so suyi wani abu da zasu ga sun birge ko a yabesu ko kuma suja hankalin mutane zuwa garesu, musamman ma idan yaga bako, dan haka zai iya yin wannan mummunar dabi`ar domin cimma daya daga cikin wadancan abubuwan da aka ambata, dan haka sai iyaye su yi kokarin saita yaro ta yanda zai kosar da kishinsa da abubuwa masu kyau .

3- Akan sami wasu yaran basa son suga baki ko kuma a je dasu wajan baki, dan haka da zarar anyi baki a gidansu, ko ya sami kansa a gurin baki to zai yi wani abu da Malaman Tarbiyya suke ce masa ( daukan fansa a matakin yarinta) don haka sai yaga menene zai yi wanda yasan bai kyauta ba, saboda ya huce fushinsa da damuwar da yake ciki sakamakon halin da ya samu kansa a ciki, don haka sai iyaye suyi kokarin cusa wa yaro son baki a zuciyar sa, da kuma bin duk wata hanya da ta dace da hankalinsa da kuma shekarunsa .

4- Yana da matukar amfani ya kasance duk ranar da akayi baki ko ya samu kansa cikinsu kuma bai yiwa babarsa abinda ya saba yi mata ba, to ta samu wani abu da tasan yana tsananin sonshi ta bashi shi kyauta, kuma lallai ne ta gaya masa dalilin da yasa ta yi masa wannan kyautar,

Wadannan sune yan shawarwarin da nake ganin zasu iya yin amfani, kuma lallai ne iyaye maza su ringa shiga irin wannan matsalar domin su taya iyaye mata tarbiyyar yaransu, domin alhakin kula da kuma tarbiyyar yara bawai a wuyan iyaye mata kadai yake ba, kamar yadda ya zama wajibi iyaye su tsaftace bakunan su daga irin wadannan munanan dabi`u, domin yara sukan koyi abubuwa da yawa a wajan iyayensu .

Allah ya sa mu dace,

Dr. Ibrahim Abdullahi Sani R\lemo  

 

Published in:  on May 21, 2008 at 2:08 pm Leave a Comment

Wasiyyar Qais Ass’ady (R.A) ga ‘ya’yansa

Lokacin da  Qais ibn Asim Assa’dy (RA) -daya daga cikin Sahabbai– yake cutar ajali, ya tara  ‘ya’yansa  ya ce musu: “Ku yi  aiki da abin  da zan gaya muku; don ba wanda za ku yi aki da maganarsa da ya fi ni son ya gaya muku abin da zai amfane ku. Idan  na cika kada ku yi min kururwa; don na ji Annabi (SAW) yana hana a yi wa mamaci ihu,  kuma shi ma da ya rasu ba’a yi masa ihu ba, ku yi min likkafani da kayan da nake sallah da su, ku shugabantar da manyanku … ku nemi na-kanku, don ku wadatu daga mutane, ba ku ba maula; don maula ita ce hanya mafi kaskanci da mutum zai bi don samun na abinci…”   

 

 

Published in:  on at 2:02 pm Leave a Comment