Badake wani mutum ne da ya ga samu ya ga rashi, ko kuma a ce “ya bata rawarsa da tsalle” Yadda abin kuwa ya faru shi ne: ani sarki ne yake da wata ‘ya “Son kowa kin wanda ya rasa” ya ce ba zai aurawa kowa ba sai wanda ya tsallake wata tsohuwa, kuma wawakekiyar rijiya. Samari suna ta gwadawa amma kowa sai a dauko shi tsamo-tsamo. Rannan sai Badake ya zo ya gwada sa’arsa, aka yi ta yi masa washi, da kirari “Badake Badake!! Badake!!!, da kansa ya gama fasuwa, kawai sai ya zabura, ya sheko aguje, firrr kamar tsuntsu, ya shallake rijiyar nan! Sai aka yi ta iho, ana sowwa, ana yi masa tafi, ana kuma tila masa kasa, sai Badake ya fara cika baki yana cewa: dama wannan ’yar rijiyar ce don abin kunya kwana da kwanaki aka rasa mai tsallake ta! to ni ko da baya da baya ba sai in tsallake ta ba! Sai wasu suka ce gafara nan kai din me! wannan din ma sa’a ka yi! Kawai Badake sai ya tashi a fusace, ya nufi rijiya da baya da baya, su kama ’yan zuga sai ihu suke yi; Badake!, Badake!!. Badake ya taho da gudu da baya zai tsallake rijiya, sai ZUNDUUUM!!! ya fada” shi kenan ya ga samu ya ga rashi! Shi ya sa wanda ya samu kansa a makamancin halin wannan mutum sai a ce “ya yi tsallaen Badake. To, “ Allah ya kiyaye mu da tsallen Badake”
Tsallan Badake
The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2008/05/20/tsallan-badake/trackback/