Badake wani mutum ne da ya ga samu ya ga rashi, ko kuma a ce “ya bata rawarsa da tsalle” Yadda abin kuwa ya faru shi ne: ani sarki ne yake da wata ‘ya “Son kowa kin wanda ya rasa” ya ce ba zai aurawa kowa ba sai wanda ya tsallake wata tsohuwa, kuma wawakekiyar rijiya. Samari suna ta gwadawa amma kowa sai a dauko shi tsamo-tsamo. Rannan sai Badake ya zo ya gwada sa’arsa, aka yi ta yi masa washi, da kirari “Badake Badake!! Badake!!!, da kansa ya gama fasuwa, kawai sai ya zabura, ya sheko aguje, firrr kamar tsuntsu, ya shallake rijiyar nan! Sai aka yi ta iho, ana sowwa, ana yi masa tafi, ana kuma tila masa kasa, sai Badake ya fara cika baki yana cewa: dama wannan ’yar rijiyar ce don abin kunya kwana da kwanaki aka rasa mai tsallake ta! to ni ko da baya da baya ba sai in tsallake ta ba! Sai wasu suka ce gafara nan kai din me! wannan din ma sa’a ka yi! Kawai Badake sai ya tashi a fusace, ya nufi rijiya da baya da baya, su kama ’yan zuga sai ihu suke yi; Badake!, Badake!!. Badake ya taho da gudu da baya zai tsallake rijiya, sai ZUNDUUUM!!! ya fada” shi kenan ya ga samu ya ga rashi! Shi ya sa wanda ya samu kansa a makamancin halin wannan mutum sai a ce “ya yi tsallaen Badake. To, “ Allah ya kiyaye mu da tsallen Badake”
Hukuncin karin gashi
Tambaya: Mene ne matsayin aske gashin kai ga mace ba tare da dalili ba? Kuma menene hukuncin karin gashi?
Maryam Husain Falaki
Amsa: Gashi ado ne ga mace da Allah (SWT) ya ba ta, hukuncin aske gashi ga mace na da halaye guda uku: 1-Ta aske shi saboda wata masifa ta faru a gareta kamar mutuwa da waninta, wannan haramun ne; domin Annabi (SAW) ya ce: ba shi ba matar da take aikata haka, kamar yadda Imam Bukhari da Imam Muslim suka rawaito daga hadisin Abu Musa Al’ash’ari Allah ya yarda da shi. 2-Ta aske shi domin wata larura kamar rashin lafiya. A wannan hali tana da dammar yin haka, babu komai a anta. 3-Ta aske shi ba tare da wata larura ba, mafi yawan malamai suna ganin cewa wannan laifi ne, ba ya halatta, domin canza kama ne. Gameda matsayin karin gashi a musulunci kuwa? Amsa ita ce: Baya halatta ga mace ta kara gashinta. babu bambanci wurin haramci tsakanin gashin mutum da waninsa, ya tabbata a cikin hadisai da dama Annabi (SAW) ya la’anci mace mai kara gashinta. Allah Shi ne mafi sani.
Dr. Muhd. A. Abubakar