Adadin Matan da ya halatta a Aura

Saboda kasancewar kyale mutum ya auri mata iya adadin da ya ga dama ba tare da iyaka ba, abu ne da zai iya kaiwa ga rudani, zalunci da rashin kula da hakkokin matan; Kuma saboda takaita mutum ga mace guda kadai zai iya kaiwa ga kokarin biyan bukatar sha’awarsa ta hanyar da a ka haramta; Musulunci ya halatta mutum ya auri mata har zuwa hudu, domin wannan shi ne iyakar adadin matan da mutum zai iya kayiye adalci tare da kula hakkokin matan, idan har ya na bukatar mace fiye da daya.

Fa’idar auren fiye da mace daya ta hada da:

  1. Wasu lokutan ya kan zama dole a yi haka kamr idan matar ta kasance tsohuwa ko ba ta da lafiya kuma idan ya hakura da ita ba zai iya kame sha’awarsa ba, kuma su na da ‘ya’ya tare da ita. Ke nan, idan ya ci gaba da zama da ita kadai, ya na tsoron fadawa  cikin sabon Allah game da sha’awarsa, kuma idan ya sake ta, zai raba ta da ‘ya’yanta. Don haka wannan matsala ba ta da wani magani sai auren mace fiye da daya.
  2. Aure wata hanya ce ta samar da alakoki tsakanin al’ummomi da yawa don haka auren mata da yawa na fadada alakoki tsakanin gidaje da dama da al’ummomi, don haka ne ma Manzon Allah (SAW) ya auri mata da dama. .
  3. Auren mata fiye da daya ya na bayar da kariya gare su ta hanyar samar da bukatunsu na ci da sha da makwanci da sha’awa da haihuwa da sauran manufofin Shari’ar Musulunci.
  4. A cikin mazaje akwai wadanda ke da karfin sha’awa ta yanda mace guda ba za ta iya biya masu bukatunsu ba, ko da kuwa sun kasance masu imani da tsoron Allah, kuma ba sa son fadawa  cikin zina, kuma su na so su biya bukatarsu ta hanyar da Shari’ah ta halatta. Don haka, sai Allah, cikin RahamarSa, ya halatta ma su samun mace fiye da daya ta hanya amintacciya.

Sheikh Ibn Uthaimin

Published in:  on May 16, 2008 at 3:10 pm Leave a Comment

Matan da ya haramta a aura

Matan da ya haramta a aura sun kasu kashi biyu:

(1) Wadanda su ka haramta har abada – su ne:

(A) Mata bakwai (7) wadanda a ka haramta saboda dangantaka ta jini da mijin: kamar yanda ya zo a Suratun Nisa’i aya ta aya ta 23, kamar haka:

(i) Uwayewato mahaifya da kakanni mata ta bangarorin uwa da uba, ko mai nisansu; (ii)’Ya’ya mata – wato ‘yar mutum ta cikinsa da ‘yar dansa ko ‘yarsa, kome nisansu; (iii) ‘Yar uwa – wa ya ko kanwa, uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya;(iv) Gwaggwanni – wato ya ko kanwar uba, da kuma gwaggwannin babansa, da babarsa da kakanninsa (maza da mata); (v) Innoni/Yakumbo – wato ya ko kanwar uwa, da kuma innonin mahaifinsa da mahaifiyarsa da kakanninsa (maza ko mata); (vi) ’Ya’yan ‘Yan uwa maza – wato ‘yar wansa ko kaninsa (uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya) da kuma ‘ya’yan ‘yayansu maza ko mata dss; (vii) ’Ya’yan ‘Yan uwa mata – wato ‘yar yarsa ko kanwarsa (uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya) da kuma ‘ya’yan ‘yayansu maza ko mata dss.

 (B) Mata bakwai (7) wadanda a ka haramta saboda shayarwa: Su ne wadanda su ka haramta a sama kamar yanda Manzon Allah (SAW) ya ce: ((Shayarwa na haramta duk abin da dangantakar jini ke haramtawa)) da sharadin: (i) Yaron ya sha nonon matar (sha na koshi) a kalla sau biyar, (ii) kuma dukkanin shayarwar ta faru ne kafin yaye.

Idan wadannan sharudda sun cika, to yaron ya zama dan wannan mata, kuma ‘ya’yanta sun zama ‘yan uwansa, ko da an haife su kafin ko bayan shayar da shi. Haka kuma, dukkan ‘ya’yan mijin da take shayar da dansa lokacin shayarwar sun zama ‘yan uwansa ko da daga wata matar suke ba ita ba. Amma ya kamata a lura a nan cewa, ‘yan uwan wanda a ka shayar din banda ‘ya’yansa, ba su da wata alaka da wannan shayarwar da hukun-hukuncenta. Don haka, ya halatta ga dan uwansa na jini ya auri matar da ta shayar da shi ko ya auri ‘yan uwarsa ta shawayarwa. Sai dai kuma ‘ya’yan dan da a ka shayar sun zama ‘ya’yan matar da ta shayar da shi da kuma uban dan da ta ke shayarwa a daidai lokacin da ta shayar da shi…

(C) Mata Hudu (4) wadanda a ka haramta saboda aurataiya: Su ne kamar haka:

 (i) Matan Uba wato matan mahaifinsa da kakansa (na uwa na uba) komai nisansa. Kuma da zarar an daura aure tsakanin mutum da wata mata, to ta haramta ga ‘ya’ayansa komai nisansu, ko da bai tare da ita ba. (ii) Matan ‘Ya’ya wato matan ‘ya’yansa komai nisansu, da sharadin dan ya tare da matar. (iii) Babar Matarsa wato mahaifiyar matarsa da kakarta, komai nisanta. Don haka, da zarar mutum ya auri mace, to babarta da kakanninta (na uwa da na uba) sun haramta gareshi, ko da bai tare da ita ba, komai nisan kakannin. (iv) ‘Ya’yan Matarsa da ‘ya’yan ‘ya’yansu (maza ko mata) da kuma jikanninsu komai nisansu, matukar dai ya tare da mata. Amma da saki ya afku kafin ya tare da matar, to wa]annan ‘ya’ya da ‘ya’yansu ba sa haramta gare shi, sawa’un an haife su kafin ko bayan ya aure ta.

 (2) Matan da su ka haramta a aure su zuwa wani lokaci – su ne:

 (A) ’Ya ko Kanwar Matarsa ko Goggonta wato na bangaren uwa ko uba har sai lokacin da su ka rabu da ita kodai ta rasu ko kuma bayan ya sake ta kuma ta kare idda.

(B) Matar da ke cikin Idda har sai ta kare iddar.

(C) Matarsa da ta shiga Harama – har sai ta kare aikin Hajji ko Umarar.

Sheikh Ibn Uthaimin

Published in:  on at 3:07 pm Leave a Comment

Rana zafi Inuwa Kuna

Wata rana na bakunci gidan wani mutum sai ya fito mana da abinci kamar yadda al’adar girmama bako take wurin bahaushe, can sai dansa ya fito yana kuka wurjanjan, ganinsa ke da wuya sai ya kama fada yana cewa yaran nan kawai su su zo su hana mutane sakat! sai kawai ya daga hanu ya dalla masa mari ya ce tafi ka ba ni wuri, sai yaron ya yi kamar zai ruga wurin uwarsa cikin gida, amma sai ya yi turus; ya rasa inda za shi, ashe uwarsa ce ta fara zabga  masa mari ya taho wurin uban ko  ya samu sauki amma ina? ai wannan shine an yi gudun gara an tadda zago, ko in ce “Rana zafi inuwa kuna” ‘yanuwana mahaifa Annabi (SAW) yana cewa: “Tausasawa ba ta taba kasancewa a cikin abu ba sai ta adonta shi, ba’a kuma zare ta daga cikin abu ba sai ya yi muni”

Hamza Aliyu Sakwaya

 

Published in:  on at 2:13 pm Leave a Comment