Hukuncin Aure a Musulunci
The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2008/05/07/hukuncin-aure-a-musulunci/trackback/
Aure a karan kan sa halal ne, musamman ga wanda ke da sha’awa da iko; Sunna ce ta Manzannin Allah; Haka kuma, Manzo SAW ya yi aure, sannan kuma ya ce: ((Lalle ni ina auren mata, don haka duk wanda ya kyamaci sunnata, to ba ya tare da ni))
Don haka ne malamai su ka ce: “aure ya fi ayyukan nafila, ga wanda ke da sha’awa, domin shi ya kunshi ayyukan alheri da dama”.
Amma kuma a wasu lokuta, aure kan zama wajibi, kamar ga mutumin da ke da tsananin sha’awa kuma ya ke tsoron fadawa cikin haramun idan bai yi auren ba. A nan, ya zama wajibi ya yi auren don kada ya fada cikin haram.
The URI to TrackBack this entry is: http://iyalina.wordpress.com/2008/05/07/hukuncin-aure-a-musulunci/trackback/