Hukuncin Aure a Musulunci

Aure a karan kan sa halal ne, musamman ga wanda ke da sha’awa da iko; Sunna ce ta Manzannin Allah; Haka kuma, Manzo SAW ya yi aure, sannan kuma ya ce: ((Lalle ni ina auren mata, don haka duk wanda ya kyamaci sunnata, to ba ya tare da ni))

Don haka ne malamai su ka ce: “aure ya fi ayyukan nafila, ga wanda ke da sha’awa, domin shi ya kunshi ayyukan alheri da dama”.

Amma kuma a wasu lokuta, aure kan zama wajibi, kamar ga mutumin da ke da tsananin sha’awa kuma ya ke tsoron fadawa  cikin haramun idan bai yi auren ba. A nan, ya zama wajibi ya yi auren don kada ya fada cikin haram.

Published in:  on May 7, 2008 at 7:34 pm Leave a Comment

Dukkaninku Makiyaya ne

Annabi (SAW) y ace: ” Kowa ya saurara ya ji: Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowanneku sai an tambaye shi kiwon da aka ba shi… Namiji makiyayi ne game da mutanen gidansa, kuma sai an tambaye shi akan abin da aka ba shi kiwo, mace ma makiyiya ce a gidan mijinta, da ‘ya’yansa, kuma sai an tambaye ta akansu… (Buhari da Muslim)

Published in:  on at 7:29 pm Leave a Comment