Tambaya: Mene ne matsayin aske gashin kai ga mace ba tare da dalili ba? Kuma menene hukuncin }arin gashi?
**Maryam Husain Falaki
Amsa: Gashi ado ne ga mace da Allah (SWT) ya ba ta, hukuncin aske gashi ga mace na da halaye guda uku:
1-Ta aske shi saboda wata masifa ta faru a gareta kamar mutuwa da waninta, wannan haramun ne; domin Annabi (SAW) ya ce: ba shi ba matar da take aikata haka, kamar yadda Imam Bukhari da Imam Muslim suka rawaito daga hadisin Abu Musa Al’ash’ari Allah ya yarda da shi.
2-Ta aske shi domin wata larura kamar rashin lafiya. A wannan hali tana da damar yin haka, babu mai a kanta.
3-Ta aske shi ba tare da wata larura ba, mafi yawan malamai suna ganin cewa wannan laifi ne, ba ya halatta, domin canza kama ne. Gameda matsayin }arin gashi a musulunci kuwa? Amsa ita ce: Baya halatta ga mace ta }ara gashinta. babu bambanci wurin haramci tsakanin gashin mutum da waninsa, ya tabbata a cikin hadisai da dama Annabi (SAW) ya la’anci mace mai }ara gashinta.
Allah Shi ne mafi sani.
Dr. Muhd. A. Abubakar