Wata rana wani matashi ya dawo gida sai ya ga tarin jama’a a kofar gidansu, gabansa ya yanke ya fadi; ya dauka ko rasuwa aka yi, daga baya sai ya ga ashe wai kannensa biyu mata ake daurawa aure, bai san ma an ba da su ba ballantana daurin aurensu! da ya yi magana sai aka ce masa: “To in an gaya maka me za ka iya yi?!” bai san lokacin da hawaye ya fara shatato masa ba, ya fito waje hawaye shabe-shabe yana cewa: “Allah ya raba mu da talauci!”
Bugu da kari, wata baiwar Allah ita ma ta koka da yadda mahaifanta suke watsi da ita, saboda mijinta ya talauce! Ta ce ada da suke da abin hannunsu, komai sai abin da ta ce a gidansu, musamman ma ga shi ita ce babba a gidan, amma da “yau” ta ci su da yaki sai ya zamana, wani lokaci ko sa ranar kannenta da suke ciki daya sai dai ta ji a sama! Ta ce wannan abu yana damuna fiye da misali, a ce talauci ya zabge mata daraja haka a idon iyayenta! Shi kuma wannan wani karamin ma’aikaci, kwatsam sai ya bar wannan aiki ya buge da wata kaskantacciyar sana’a da yake zaton zai yi saurin samun kudi ta ita, da aka tambaye shi, sai ya ce, ya yi haka ne saboda gudin fiushin mahaifiyarsa, saboda kannensa da yayyensa duk mawadata ne, don haka idan sha’ani ya taso– kamar biki ko suna– su kan ba ta kudi da yawa, shi kuma abin da yake iya ba ta bai taka kara ya karya ba, ita kuma sai ta yi ta fada har barazanar tsine masa take yi in bai yi mata irin yadda ‘yan’uwansa suke yi mata ba, ya yi mata duk wani bayani amma bata yarda ba, shi ya sa ya yanke shawarar shiga wannan sana’a ta kaskanci ko shi ma ya samu kudi don ya kara kima a idon mahaifiyarsa, kuma ya huta da zagi da tozartawa a gaban kannensa ba iyaka!