A cikin watansu na farko bayan bikinsu, ango na ganiyar angwancinsa, amarya na cin amarcinta da tsinke, suna modar madarar soyayya, saboda shakuwa da kaunar dake tsakaninsu kamar sa cinye juna….. Kai abin dai ba’a cewa komai. Suna cikin wannan aljanna duniya sai KWATSAM ba sai mahaifin angon nan ya nemi ya saki matarsa ba! abu kamar almara, ashe wai da gaske yake! Angon ya dauka wani mummunan laifi amaryar ta yi wa mahaifin nasa, ko mahaifiyarsa, ko wani daga cikin magabatnsu, ko kuma wata muguwar illa ce ta bayyana a gareshi game da ita… Uban ya ce duk ba daya, “Dalilin da ya sa na ce ka sake ta; saboda wanta da yake auren kanwarka tun shekaru da suka shude ya sako min ita don rashin mutunci; ni kuma duk wanda ya yi min kan kara sai na yi masa na itace! Don haka kai ma ka sakar musu ‘yarsu” da yaron ya ji wannan ne
dalilin sai ya ce: baba da binciki aka yi aka ga me ya hada su, maimakon wannan mataki” uban sai ya kada baki ya ce: “Wato ’yan ubanci za ka nuna, da cikinku daya ai da ba sai na ce ka sake ta!” Dan ya ce wallahi ba haka ba ne… ya yi juyin duniyan nan da mahaifinsa, ya ce sam. Ya yi kuka kamar hawayensa ya kafe, amarya kuwa cutar yau daban ta gobe daban saboda zulumi, kullum sai su zauna su yi dan koke kokensu, su dan yi ‘yan shawarwari su tashi. Rannan ya je ya samu baffaninsa ya gaya musu halin da ake ciki, suka tausaya matuka, suka je suka yi ta bai wa dan’uwan nan nasu baki, amma kamar turi, suka ce masa to su dai wannan abu ya fi karfinsu. Ya kuma tsurewa, amma dai bai karaya ba, sai ya garzaya wurin wani aminin mahaifin da shi kadai yake iya sa shi ya yi abin da bai niyya ba, da ya yi masa bayani, sai ya ce tashi mu tafi ta kwana gidan sauki!
Ango ya yi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha don murna, har da zai yi wa amaryarsa waya ya yi mata albishir, sai dai ya dakata ya ga yadda za ta kaya. Da ya je ya same shi, dan mutumin nan ya hada girar sama da ta kasa ya ce kwata-kwata ba za ta saku ba. Wato har da kai za’a hada baki a ci min mutunci?! Da dai ya ga ba sarki sai Allah, shi ma sai ya ce: “dana sai dai in taya ka da addu’a, amma abin ni ma ya fi karfina!” Angon nan kamar ya barke da zawo, ya nufi gida a dimauce kamar ya yi hauka.
Daren nan kwanan zaune suka yi suna ta shawarwari, da asussuba sai ya ji bugun kofa ba-ji-ba-gani, yana budewa sai ya ga kannesa ne da suke ciki daya a firgice. Ya ce masa lafiya?! Sai ya ce: Umma jiya ba a gida ta kwana ba! Baba ya kore ta saboda wai tafiyar hawainiyar da kake yi wurin zartar da dokar da ya ba ka ta sakin wance
Ango ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir
Raj’un” ya shiga gida, matar ta taso hankalinta a tashe ta
ce masoyina mai ya faru? Ya ce ba komai, bara in je
masallaci in dawo, yana salla amma hankalinsa ba yana
wani wuri, bayan ya gama zikrin safiya, sai ya kasa komawa
gida, sai ya nufi gidansu don ya tabbar menene
ha}i}anin abin da yake faruwa.
Da ya shiga falon uban sai ya tarar da shi fuskarsa a murtike
kamar an aiko masa da mutuwa, kafin ya ce masa
“Ina kwana” sai cewa ya yi wallahi in ba ka saki yarinyar
nan cikin gaggawa ba a bakin auren uwarka! kuma
yanzun nan ka je ka kawo min mukullin gidanka – da
yake dama uban ne ya gina masa– ango dai ya ga abin
ya fuce “min sharrin” ya kai “ma hala}a” sai ya tafi gida,
idonsa jawar saboda kuka, ya je ya samu amaryarsa, ya
kwashe labari baki ]aya ya gaya mata, don haka yanzu
dai ba wata mafita illa su dangana su rabu, su yi wa juna
addu’a alheri….. Haba take amaryar ta yanke jiki ta fa]i,
yana shafa mata ruwa yana yi mata fifita, yana ba ta
ha}uri, yana ce mata komai }addara ce ta Allah….!
Shi ma yana share nasa hawayen da hankiji. Suna
cikin wannan hali sai ga uban a kansu, ya ce rubuta
takardarta ka ba ta “mu kowa ya ci tuwo da mu miya
ya sha!” wasu da suke tare da uban suna ta ba shi
baki, amma kamar dutse suke yi wa magana, yaron
nan dai da ya ga ba sarki sai Allah, ya ]auki takarda
da biro, ya rubuta mata saki ]aya, suka rungume juna
a gaban mutane suna ta kuka, amma uban nan ko a
jikinsa, sai da ya ga ya ba ta takardar nan hannu-dahannu
sannan ya tafi ya kyale su.
Yanzu dai tuni har sun rabu! Kuma Allah ka]ai ya
san irin mawuyacin halin da kowannesu yake ciki!
FA[AKARWA GA IYAYE:
Sau tari irin wannan