Allah ya kawo ranar da wance za ta je Unguwa!!!

 Ko shakka babu cewa agalabiyyar maza ba sa son matansu su rika yawan fita unguwa barkatai, kuma da ma wannan shi ne abin da shari’a ta yi umarni da shi; wato mata su zauna a gida (in ba wata lalura ba) amma shi wannan gogan namu kullum addu’arsa Allah ya kawo ranar da matarsa za ta tambayi unguwa, ya yi sauri ya bar ta idan ya ga ma ta jima ba ta tambayi unguwa ba, har tayi yakan yi mata ya ce: “wance ba ku da biki ko suna ne?” Ko kun san me yasa kullum mijin nan burinsa matar ta ce za ta je unguwa? Saboda ita a ka’idarta in kika ga ruwa ya taba jikinta to na sama ne, ko tsarki za ta yi, ko wankan tsarki, ko kuma alwala, in ba haka ba, in za ta shekara zancen wanka bai taso ba, ballantana a yi maganar ado da kwalliya, amma duk ranar da za ta tafi unguwa in ta caba ado sai ki dauka a ranar aka kawo ta dakin miji,  shi kuma yana so ya riga ganinta a cakare,  ba kullum kamar an  tono ta daga rami ba, yana ganin ta yana firgita!

A ganinki me yasa wannan mata ta zabi kullum ta rika zama busu-busu, in dai ba unguwa za ta ba, kuma wace shawara za ki bai wa irin wadannan kazaman  na ga-ni-kashe-ni

 

Published in:  on April 16, 2008 at 12:35 pm Leave a Comment

Gidan Qais ibn Asim Assa’dy (RA)

 Lokacin da  Qais ibn Asim Assa’dy (RA) -daya daga cikin Sahabbai– yake cutar ajali, ya tara  ‘ya’yansa  ya ce musu: “Ku yi  aiki da abin  da zan gaya muku; don ba wanda za ku yi aki da maganarsa da ya fi ni son ya gaya muku abin da zai amfane ku. Idan  na cika kada ku yi min kururwa; don na ji Annabi (SAW) yana hana a yi wa mamaci ihu,  kuma shi ma da ya rasu ba’a yi masa ihu ba, ku yi min likkafani da kayan da nake sallah da su, ku shugabantar da manyanku … ku nemi na-kanku, don ku wadatu daga mutane, ba ku ba maula; don maula ita ce hanya mafi kaskanci da mutum zai bi don samun na abinci…”  

 

Published in:  on at 12:33 pm Leave a Comment

Tambaya 0003

 

Tambaya:

Mace ce mijinta ya ba ta  maganin zubar da ciki ba ta sani ba,  kuma cikin nata ya zube. Don Allah malam: Menene hukuncin wannan miji, kuma menene hukuncin aurensa da wannan matar, kza’a iya cewa ya yi kisan kai,  wane  mataki ya kamata ta dauka, kuma menene hukuncin zubar da ciki a musulunci?

Maryam Usman

BISMILLAHIR     RAHMANIR         RAHIM

Alhamdulillah, Wassalatu Wassalamu ala Rasulillah, Wa ba’adu:

‘Ya’ya ni’ima ce daga Allah Subhanahu Wata’ala. Annabawa da bayin Allah na kwarai sun roki Allah da ya ba su’ ya’ya. Kashe yaya don jin tsoron talauci ko kunya, ko wahalar reno al’ada ce ta jahiliyya; sawa’un jahiliyyar zamanin yanzu ko ta da.In har kana son sanin girmar ni’imar da Allah ya yi maka ta ‘ya’ya, ka tambayi wanda ko wadda ba’a taba yi masa haihuwa ba.

Danganeda tambayoyinki kuma:

1. Ina hukuncin mijin da ya bai wa matarsa maganin zubar da ciki, sai ta sha ba tare da saninta ba, kuma cikin ya zube? Amsa: Zubar da ciki a kowane mataki yake; (watannin farko, tsakiya, ko karshe) – ba tare da wata larurar da shari’a ta yarda da ita ba – ya haramta a zance mafi inganci na malamai, sawa’un wanda ya yi sanadin zubar da cikin daya daga cikin iyayen dan ne ko waninsu.

2. Menene hukuncin aurensu? Amsa: Aurensu ya na nan daram.

3. Shin za’a dauka ya yi kisan kai? Amsa: Ya dogara bisa ga halin da aka zubar da cikin; idan cikin ya kai wata hudu ko sama da haka, to za’a iya cewa ya yi kisan kai, tun da yaro a wannan lokaci ya na da rai, kamar yadda ya zo a Hadisi na hudu na Arba’una Hadis.In kuma cikin bai kai wata hudu ba, to ya yi babban laifi, amma ba za a ce ya kashe rai ba, don kuwa a wannan hali yaro ba’a hura masa rai ba.

4. Wane mataki ya kamata ta dauka? Amsa: Ita dai ba ta yi laifi ba, tun da dai ta yi shi ne bisa rashin sani. kamata ya yi kuma ta yi wa mijinta nasiha da ya tsoraci Allah, ya yawaita istigfari da ayyuka na gari. Ita kuma nan gaba sai ta sa hankali, kar ta sha wani magani ba tare da shawarar likita ba. Allah ya kiyaye na gaba.

5. Menene hukuncin zubar da ciki a musulunci? Amsa: Hukuncin zubar da ciki a musulunci haramun ne; sawa’un sabon ciki ne, ko tsoho. Amma in akwai wata larurar da shari’a ta gamsu da ita, to ana iya zubar da ciki. Alal misali: Bakin likitoci ya zo daya akan cewa; in ba’a zubar da cikin nan ba, uwar tana iya rasa ranta, ko za ta jirkata, ko wani abu mai kama da haka, a irin wannan halin, ya zama dole a zubar da cikin don a ceci ran uwar. Wallahu A’alam.

Dr. Bashir ibn Imam Ali       

 

Published in:  on at 12:31 pm Leave a Comment