Kananan Hukumomi Albishirinku

 

A irin marka-markar da ofishin “A1 Nana” yake tsalawa a fagen tarbiyya, zamantakewar aure, da abubuwan da suka shafi mata, mamakon alheransa ya fara shatata a kananan hukumomin Jihar Kano (44) ta hanyar wani kwarya-kwaryar shiri da ofishin mai bai wa mai girma  gwamna shawara akan ayyuka na musamman (bangaren mata) ya shirya.  

A wata zantawa da Mujallar iyali ta yi da shugabar wannan ofis  Haj. Mariya Sanusi Mahdi game da manufofin wannan shiri, da kuma abin suka yanke shawarar hada-kai da ofishin “A1 nana” don gudanar da wannan aiki, sai ta ce: Babbar manufar wannan shiri agazawa iyaye mata wurin inganta rayuwarsu ta aure, da taimaka musu wurin tarbiyyar ’ya’yansu, da kuma sa su a hanya  wurin neman na-kansu.

 

Game da abin da ya sa suka zabi su yi taimakekeniya da “A1 nana cewa ta yi: Mun yanke wannan shawara ne saboda, wannan ofis-A1 nana- ya yi fuce da nagartattun tsare-tsare, kyawawan manfofi, hanyoyin zartarwa masu tasiri da ban sha’awa, da aiki tukuru, ga kuma matukar burin da yake da shi na tallafawa mata mazauna karkara, da dai wasu tsare-tsare masu kayatarwa. Kuma ya yi mun gani.

Shi kuwa shugaban ruko na ofishin “A1 nana” Eng. Bashir Adamu Aliyu nuna farin-cikinsa ya yi game da wannan goron gayyata, ya kuma yi alkawarin in sha Allahu kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Da Mujallar iyali ta tuntube shi akan tanadin da ofishinsa ya yi gameda  wannan  shiri sai ya ce: Za mu fitar da cikakken bayani akan haka nan gaba,  amma dai za mu fi mayar da hankali ne akan: 

TARBIYYA: (Muhimmacinta fa’idojinta, hanyoyi, da dabarun yinta, kurakuren da suke aukuwa a cikinta, da hanyoyin magancesu 

ZAMANTAKEWA (Shawarwari ga iyaye danganeda auren `ya`yansu – zabi, nema, kayan aure da biki da tariya– Rayuwar iyali mafificiya -Hakkokin ma`aurata, zaman lafiya da taimakekeniya da sadaukarwa a rayuwar aure- Mace-macen aure-yawaitarsa, illolinsa, abubuwan da suke kawo shi da magungunansu)

SANA’O’I: koyar da wadannan sana’o’i (sabulun wanka, man shafawa, abincin jarirai, da maganin kwari). 

 

Published in:  on April 5, 2008 at 2:04 pm Leave a Comment