wata rana wani malami mutumin Najeriya yana zaune a masallacin Annabi Tsira da aminci su tabbata agareshi, akusa dashi akwai wani Balarabe yana karatun Qurani, sai malamin ya hango wani yaro aguje yazo ya sunbanci Babansa yana farin ciki, amma mutuminnan yai kunnen uwar shegu da yaronnan ko daga kai baiyi ya kalleshi ba, bai kuma ce uffan ba .
Da yaron yaga haka sai ya juya ya tafi. can wajen sallar magriba sai ga yaronnan ya dawo yasake gaida Baban nasa kamar yadda al adarsu take wato ya sunbance shi
nan-da-nan Babansa shi ma ya rungume shi ya zaunar da shi suka ci gaba da hira irin ta yaro da Babansa.
Malamin nan yana kallon duk abinda yake faruwa, amma abinda ya dare masa kai shine yadda Uban yaron yaki ce masa : Bata dahu ba balle ta kone, a karon farko amma yanzu ya kula da shi sosai. Da aka jima sai Malamin nan ya matsa kusa da mutumin nan ya tambayeshi dalilin haka, sai Uban yaron yace:- Yaron ya san laifinsa bai je makaranta bane sai maza ya ruga yatafi da ya dawo kuwa muka shirya.
To yaku Iyaye ashe akwai matakai da yawa na tarbiyya da zamu yiwa yayanmu kafin aje ga duka?
kamar su;-
rashin kallo.
ishara da fuska.
kifta ido.
karamar harara.
Kin fita dashi unguwa.
Hana shi rabin kudin alawar da ake bashi zuwa makaranta, misali in Naira goma ne sai abashi Naira biyar.
Daga Hamza Aliyu Ibrahim.