Hakika talauci ko kuma yawan barace-barace kan sanya iyaye dorawa ‘ya’yan su talla ko dai ya zama haka din ne basu da abin da hannu wanda za su dogara a kan sa ko kuma ya zama uwa ta sa buri a kan ‘yar ta cewa idan ba ta hanyar talla ba, ba inda za ta samu abinda za ta yiwa ‘yar ta kayan daki.
Wani lokaci akan samu uba bashi da sana’a mai karfi da zata rike shi da iyalin sa bay a wadatar da su. Don haka sai ya zamo abin da ya ke kawowa ba ya wadatar dasu . don haka sai su iyaye mata su dorawa ‘ya ‘yan su talla don neman abinda za su tallafawa kansu.
Dun inda ka shiga a manyan biranan mu da kauyuka, za ka iske yara maza da mata suna ta garamrambar tallace-tallace na abubbuwa daban-daban
Mafi yawan mu daga nan suke lalacewa daga mazan har mata. Su kan shiga lungu-lungu rariya-rariya sune kasuwanci wuraran gyaran motoci tashoshin motoci da kuma wuraren gine-gine, wanda daga nan idan aka samu lalatatu suka lalata yaran maza ne ko mata da yawa an sha samun wadanda daga nan suke sake samun ciki.
Za ka iske yara tun daga shekara bakwai har goma sha suna yawon talla shaguna da wuraren taruwar maza don Allah yau da gobe me ake zato zai faru. Sai shaidanu su fara yaudarar ta da kalmomi masu dadi ko kudi daga nan sai su sami damar biyan bukatar su da ita. Daga nan kuma iyaye su fara da na sani ana neman yadda za’a zubar da cikin ko kuma a rufa abinda za’a samu wani a daura mata aure da shi ba tare da ya san abinda ake ciki ba ‘yan watanni sai a ce ta haihu, shi kuma yace sam bai san haka ba don ba nasa bane. Ta tattara ta koma gaban iyayen ta. Abin kunya dai ya samu ! an kuma tozarta dokar Allah an ci amanar yarinya wajen rashin kula da tarbiyyar ta.
Saboda haka ina kira ga iyaye akan suji tsoron Allah a kan ‘ya ‘yan su, su sami cewa amana ce a ka dora a hannun su. Kuma za’a tambaye su a rana sakamako. Ya zo a cikin Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “kowannen ku makiyayi ne, kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa, shugaba makiyayi ne, namiji makiyayi ne a kan iyalinsa, mace mai kiwo ce game da mijinta da ‘ya’yansa, saboda haka kowannenku mai kiwo ne kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa. (Bukhari)
Ina kira ga iyaye a kan lallai su kula da hakkin ‘ya’yansu da tarbiyyarsu, da kuma mutunci, kada neman abin duniya ya sa idonsu ya rufe har su cutar da ‘ya’yansu su kuma cutar da kansu. Shin daidai ne mu jefa ‘ya’yanmu mata cikin halaka ta hanyar tallace-tallace, alhali babu ma wani abin kirki da suke kullawa?
Kuma wajibi ne muyi la’akari da kalubalen da ke fuskantar mata musulmi a yau saboda rashin karatun ‘ya ‘yan mu mata muna fuskantar wulakanci da tozartarwa da abin takaici duk lokacin da muka je asibiti ganin likita. Ya kamata mu yi wa kanmu kiyamul laili.
A maimakon mu bar ‘ya ‘yan mu suna yawon talla, mu sasu a makarantar lslamiyya da ta zamani don su sami ilimi da zasu taimaki kansu da ‘yan uwansu mata musulmi.
DAGA SAFIYYA HUSAIN FALAKI