Tambaya ta 0002

 Tambaya: Menene matsayin kaffarar wanda ya yi rantsuwa, da ya tashi kaffara ya yi azumi, ba tare da duba abubuwanda aka ce ya yi kafin azumi ba?                                 Maryam Husaini Falaki

***

Amsa: Kaffarar wanda ya yi rantsuwa kuma ya warware ta ita ce: ciyar da miskinai guda goma, ko ba su tufa, ko kuma ‘yanta bawa, kuma yana da zabi wurin gabatar da kowanne daga cikin abubuwa guda uku da aka ambata, idan kuma ya kasance ba shi da halin da zai yi daya daga cikinsu, sai ya yi azumin kwana uku.Saboda haka, danganeda wannan tamabayar, idan ya zamana ya yi azumin ne domin rashi, to kaffararsa ta yi; babu komai a kansa, amma idan ya kasanace ya yi azumin ne tare da cewa yana da halin da zai iya ciyar da miskinai, ko ba su tufa, kaffararsa ba ta inganta ba, ya wajaba a gareshi ya ciyar da miskinai goma, ko ya ba su tufa, domin abin da ya yi ya sabawa fadin Allah a cikin Alkur’ani (Suratul Ma’ida aya ta 89)

Allah shi ne mafi sani.

Dr. Muhd. Alhaji Abubakar
 

Published in: on March 31, 2008 at 9:03 am Leave a Comment

Nana Khadija Uwar Muminai

 

Assalamu alaikum. ‘Yan uwana yara  zan ba ku tarihin wata babbar mata cikin iyayen muminai.  Sunanta Khadijah bintu Khuwailid. Ita ce farkon matan Annabi (S A W) Ita ce farkon wadda ta fara muslinta, Ita ce kuma ta haifawa Manzon Allah (S A W) duka ‘ya yansa ban da Ibrahim. ‘Ya’yan nata su ne: 1) Abdallah, 2)Alqasim, 3) Zainab, 4) Rukayya, 5) Ummu kalsum, 6) Fadima. Yanzu ina so wani ko wata ta ba mu tarihin wata Sahabiyar a takaice kamar yadda ni ma na takaita.

Amina Muhd. Muslim. 

Published in: on at 9:00 am Leave a Comment

Illar Tallace-Tallace ga ‘yan mata

Hakika talauci ko kuma yawan barace-barace kan sanya iyaye dorawa ‘ya’yan su talla ko dai ya zama haka din ne basu da abin da hannu wanda za su dogara a kan sa ko kuma ya zama uwa ta sa buri a kan ‘yar ta cewa idan ba ta hanyar talla ba, ba inda za ta samu abinda za ta yiwa ‘yar ta kayan daki.
Wani lokaci akan samu uba bashi da sana’a mai karfi da zata rike shi da iyalin sa bay a wadatar da su. Don haka sai ya zamo abin da ya ke kawowa ba ya wadatar dasu . don haka sai su iyaye mata su dorawa ‘ya ‘yan su talla don neman abinda za su tallafawa kansu.
Dun inda ka shiga a manyan biranan mu da kauyuka, za ka iske yara maza da mata suna ta garamrambar tallace-tallace na abubbuwa daban-daban
Mafi yawan mu daga nan suke lalacewa daga mazan har mata. Su kan shiga lungu-lungu rariya-rariya sune kasuwanci wuraran gyaran motoci tashoshin motoci da kuma wuraren gine-gine, wanda daga nan idan aka samu lalatatu suka lalata yaran maza ne ko mata da yawa an sha samun wadanda daga nan suke sake samun ciki.
    Za ka iske yara tun daga shekara bakwai har goma sha suna yawon talla shaguna da wuraren taruwar maza don Allah yau da gobe me ake zato zai faru. Sai shaidanu su fara yaudarar ta da kalmomi masu dadi ko kudi daga nan sai su sami damar biyan bukatar su da ita. Daga nan kuma iyaye su fara da na sani ana neman yadda za’a zubar da cikin ko kuma a rufa abinda za’a samu wani a daura mata aure da shi ba tare da ya san abinda ake ciki ba ‘yan watanni sai a ce ta haihu, shi kuma yace sam bai san haka ba don ba nasa bane. Ta tattara ta koma gaban iyayen ta. Abin kunya dai ya samu ! an kuma tozarta dokar Allah an ci amanar yarinya wajen rashin kula da tarbiyyar ta.
    Saboda haka ina kira ga iyaye akan suji tsoron Allah a kan ‘ya ‘yan su, su sami cewa amana ce a ka dora a hannun su. Kuma za’a tambaye su a rana sakamako. Ya zo a cikin Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “kowannen ku makiyayi ne, kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa, shugaba makiyayi ne, namiji makiyayi ne a kan iyalinsa, mace mai kiwo ce game da mijinta da ‘ya’yansa, saboda haka kowannenku mai kiwo ne kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa. (Bukhari)
    Ina kira ga iyaye a kan lallai su kula da hakkin ‘ya’yansu da tarbiyyarsu, da kuma mutunci, kada neman abin duniya ya sa idonsu ya rufe har su cutar da ‘ya’yansu su kuma cutar da kansu. Shin daidai ne mu jefa ‘ya’yanmu mata cikin halaka ta hanyar tallace-tallace, alhali babu ma wani abin kirki da suke kullawa?  
    Kuma wajibi ne muyi la’akari da kalubalen da ke fuskantar mata musulmi a yau saboda rashin karatun ‘ya ‘yan mu mata muna fuskantar wulakanci da tozartarwa da abin takaici duk lokacin da muka je asibiti ganin likita. Ya kamata mu yi wa kanmu kiyamul laili.
A maimakon mu bar ‘ya ‘yan mu suna yawon talla, mu sasu a makarantar lslamiyya da ta zamani don su sami ilimi da zasu taimaki kansu da ‘yan uwansu mata musulmi.
     DAGA SAFIYYA HUSAIN FALAKI

Published in: on March 28, 2008 at 3:31 pm Leave a Comment

Gidan Annabi (SAW)

Anas dan Malik  (RA)  ya ce: Annabi (SAW) yana daga cikin mutanen da suka fi kowa kyawun hali, wata rana sai ya aike wata bukata, sai na ce WALLAHI BA ZA NI BA! Amma a raina ina da niyyar zuwa, sai na je na hadu da yara a kasuwa muka yi ta wasa, ban ankara ba sai na ji Annabi (SAW) ya danke ni ta keyya, da na waiwaya sai na ga yana dariya! Yana cewa “Kai dan Anas kama hanya ka tafi inda na aike ka” sai na ce masa to manzon Allah bara in tafi. Ya ce shekarata (10) ina yi masa aike aike bai taba ce min don me ka yi kaza, ko ba ka yi kaza ba (Muslim

Published in: on March 26, 2008 at 10:57 am Leave a Comment

‘Yar Canke

Abokaina matasa da kananan yara ga wani wasa mai ban sha’awa da nishadi, da yake kaifafa kwakwalwa da saurin gano abu. Za’a iya yinsa a makaranta lokacin “break” ko a gida lokacin da ba’a komai  Yadda tsarinsa yake: wadanda suke da sha’awar shiga wasan za su zauna wuri guda su jeru, ko su yi da’ira, sannan sai daya daga cikinsu ya tashi ya je can nesa; inda ba zai ji abin da za su fada ba,  su kuma sai su hada-baki akan  wani abu  (mutum ko dabba, ko gari ko ma dai menene, amma ya zama sananne ne ga dukkaninsu, har shi wanda ya tashin ) sannan sai su ce masa sun shirya ya dawo, idan ya zo, shi kuma sai ya yi kokarin gano abin, ta hanyar tambayoyi; zai rika tambayarsu daya bayan daya, kuma  duk wanda ya tambaya zai fada masa gaskiya, amma ba zai yi masa wani  karin bayani ba, in kuma bai san amsar ba, sai kawai ya ce bai sani ba. Haka za su yi ta yi har sai ya gano, sai ya zauna, wani kuma ya tashi, idan ya dauki lokaci mai tsawo bai gano ba (kamar a yi zagaye uku, ko biyu gwargwadon yawan masu wasan, da yadda suka yi yarjejeniya, shikenan ya fadi sai a gaya masa) Saurin gano amsar yana da alaka da hazaka da kwarewarka\ki wurin ya tambaya. GA MISALAI  *Wasu ‘yan mata ne a makarantar kwana, su goma bayan sun yi bitar karatunsu sun gaji, sai suka zauna don yin dan nishadi da wannan wasan, sai suka ce wacece za ta fara? sai  Nusaiba  ta ce ita za ta fara. Sai ta tashi ta tafi nesa, su kuma sai suka hada baki akan Nana A’isha matar manzon Allah (SAW) san nan sai suka kwalla mata kira ta dawo, ta zo ta same su sun yi da’ira tsaf, suka matsa mata ta zauna. Ta fara tambaya. Ta tambayi ta kusa da ita (wato ta daya) ta ce mata: mace ce ko namiji? Ta ce mace. Ta tambayi ta biyu tana raye ko ta mutu? Ta ce ta mutu. Ta tambayi ta uku; A lokacin Annabi (SAW) take ko bayan lokacinsa? Ta ce a lokacinsa take. Sai da ce yauwa! na fara gano bakin zaren! Sannan sai ta tambayi ta hudu: tana daga matan Annabi(SAW) ko ba ta ciki? Sai ta ce a tana ciki. Sai ta ce da ta biyar:  Mahaifinta shi ne babban abokin manzon Allah(SAW) wanda har Allah ya ambaci abotarsu a Kur’ani, ko ba shi ba ne? Sai ta ce shi ne. Sai ta ce Nana A’isha (R.A) Sai suka ce haka ne. Sai wata ta kuma tashi. Haka suka yi ta yi cikin nishadi.  *Sumayya ita ce ta karshe, kuma da yake tana da kokari kwarai, ga ta  gwanar tambaya, sai ta yi ta cika musu baki; tana cewa ita in ta yi tambayoyi da yawa ta yi uku za ta gano! Su kuma da  suka fi ta, sai suka hada-baki akan ita Sumayyar, da ta fara ta yi ta yin tambayoyi ba kakkautawa amma ina! Duk basirar da take ji da ita ta kwakkwafe ta wai ko ta gano  wanda  ko abin da suke nufi ba ta gano ba, har daga karshe ta sallama ta ba da gari. Sai suka ce ai ke ce!Sai  ta rike kai, ta  yi kamar ta yi kuka, su kuma suka yi ta yi mata dariya suna cewa maganin mai cika baki kenan. Bayan sun ji garau sai suka koma kan muraja’arsu.*Nan kuma ‘yan samari ne suka je gidan su wani abokinsu ziyara, bayan sun ci abinci sai babar abokin nasu ta ce su yi wannan wasan, kuma ta gaya musu yadda ake yi. Sai suka fara. Ita kuma tana zaune tana jin su. Suka yi ta yi tana dada nuna musu dabarun yadda ake yin tambayoyi masu azanci. A karo na kusa da  karshe sai  suka hada-baki akan tsohon shugaban America George Bush uban shi wannan na yanzu. Da wanda ya tashi ya dawo sai ya fara canka. Ya tambayi na daya; dan adam ne ko ba dan adam ba ne? Ya ce dan adam ne. Ya tambayi na biyu: A nan gurin yake ko ba’a nan yake ba? Ya ce ba a nan yake ba. Ya tambayi na uku: ya taba rike wani babban mukami a rayuwarsa ko bai taba ba? Ya ce masa ya taba. Ya tambayi na hudu: musulmi ne ko kafiri? Ya ce kafiri. Ya ce da na biyar: Shugabancin kasa ya yi ko wani mukamin daban? Ya ce shugabancin kasa. Ya ce da na shida: A Amerika ne ko a turai ko a Afrika? Ya ce a Amerika. Sai ya ce Clinton! Sai  aka ce a’a. Sai ya tambayi na bakwai; Yana raye ko ya mutu? Ya ce yana raye. Ya tambayi na takwas; lokacin da yake yakin neman zabe ya yi wa Amerikawa alkawarin cewa yakar musulunci ka’in da na’in shi ne daya daga cikin manyan  ayyukan da zai sa a gaba  in suka zabe shi? Ya ce ya taba fada. Sai ya ce  George Bush Uban  Bush na yanzu. Sai suka ce haka ne. Sai uwar ta ce to ai yanzun ma kamar shi ne yake mulkin, ko ma in ce gara shi,  don kusan Amerika ba ta taba yin wawan shugaba, lusari makaryaci, mai nuna gabarsa ga musulunci da musulmi firi falo ba irin Bush  na yanzu. Ya tashi haikan yana yakar musulmi da muslunci da sunan yaki da ta’addanci. A karshe Allah tona asirin kafiri;  ya matsa bakinsa shi da kansa ya ce (Yakin Cross) yake yi (Ma’ana yaki da musulunci)! Dan karamin misali: Mutanen Iraqi MILYAN GUDA! Aka kashe a cikin shekaru biyar kacal da kasar ta yi karkashin mulkin mallakarsa! Amma har biki ya yi musamman larabar da ta fuce na cika shekaru biyar a Kasar! Kun gani ko ‘ya’yana! Don haka mu ci gaba da addu’a aniyarsu ta bi su, kulle-kullen da suke yi wa musulunci su koma kansu!‘ suka ce amiiin!  Sai ta ce to yanzu sai ku tashi ku tafi gida kada a zo ana nemanku. Sai karamin cikinsu ya ce Umma to ai ni ban yi ba! Sai ta ce don Allah yi hakuri mantawa na yi. Bisimillah: suka hadu akan ZUMA, ita ma  ta shiga cikinsu wannan karon,  Da ya dawo ya fara ita:  Matum ne, ko guri, ko abin ci, ko abin sha? Ta ce Abin sha. Ya ce da na biyu: A kwai abin da ya fi shi zaki? Ya ce babu. Sai ya ce zuma. Sai suka yi ta yi masa kabbara suka ce haka ne. Ita kuma  ta kara masa da Naira 50 saboda bajintar da ya nuna wurinn saurin gano amsar, don kuma ta karfafa masa gwiwa. Yanzu kuma sai ku gwada.        

Published in: on March 23, 2008 at 10:19 am Leave a Comment

Gidan su Abu Huraira

Abu Hurairah (RA) Duk lokacin da zai fita, ko ya dawo gida, sai ya je bakin kofar dakin mahaifiyarsa ya ce: “BABATA Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Sai ta ce: “Wa alaikumus Salam wa rahmatullahi wa barakatuhu DANA” Sai ya kuma cewa: “Allah Ya rahamshe ki; saboda tarbiyyar da kika yi min ina karami, ita kuma sai ta ce: “Kai ma Allah Ya rahamshe ka, ya saka maka da alheri, ya kuma yarda da kai; saboda biyayyar da kake min bayan ka girma” Daga cikin biyayyar da ya yi mata bayan ya girma: Akwai: 1- Rokon Annabi (SAW) da ya yi, kan ya yi mata addu’a ta musulunta, ya yi mata, kuma ta musuluntar. 2- Shi yake jigilar kai ta, da dakko ta daga ban daki; da yake makauniya ce. Bai je haji ba har ta rasu.

Published in: on March 20, 2008 at 6:44 pm Leave a Comment