Gaba tsakanin musulmi babban zunubi ne; domin Allah ya wajabtawa musulmi son juna da kyautata wa juna, shi ya sa gusar da wannan zunubi ta hanyar yin sulhu tsakanin masu gaba ya zamo ibada ce da Allah yake so. Ga wasu ladaddakin wanda ya aikata wannan alheri.
1- Rabauta da rahamar Allah: Allah Ta’ala yana cewa a cikin ma’anar wata aya: ((Hakika muminai ‘yan uwan juna ne ; saboda haka ku sulhunta tsakanin ‘yan uwanku, ku kuma ji tsoron Allah domin ya rahamshe ku)) (Hujurat: 10).
2- Samun soyayyar Allah ; domin duk wanda ya kyautatawa ‘yan uwansa Allah yana son sa kamar yadda ya ce a ma’anar wata aya: ((Ku kyautata, domin kuwa Allah yana son masu kyautawa)). (Bakara: 195). Sulhu kuwa kyautatawa ne ga ‘yan uwa musulmi.
3- Samun ladan yaye wa musulmi matsala da gusar musu da wata cuta ; domin tabbas sabani tsakanin musulmi yana dauke da cutar da su duniya da lahira. Allah ya azarta mu da yi masa biyayya da kuma taimakon bayinsa.
Rabi’atu Aliyu Umar (Umm A’isha).