Menene Tsotson Hannu?
Tsotson Hannu shi ne sanya dan-yatsa da yara suke yi a bakinsu suna tsotsa.
Jarirai da yara sukan sa babban dan yatsa, ko yatsu guda biyu a bakinsu suna tsotsa.
Me yasa suke tsotsan hannu?
-
Tsotson wani abu ne da ya zama wajibi a wurin yaro, don ta haka ne zai ci abinci kuma ya rayu.
-
Duk jaririn da bai samu biyan bukatar tsotsansa ta hanyar ciyarwa ba, to zai tsotsi ‘yan yatsun sa.
-
Tsotson hannu yana sa yaro ya samu gamsuwa ta wani dan lokaci.
-
Tsotson hannu yana ba wa yaro damar kama kansa; wato maimakon ya yi kuka sai ya jefa dan yatsansa a baki ya yi ta tsotsa.
-
Tsotsan hannu ya na kwantar sa hankalin yaro.
ILLOLIN TSOTSON HANNU
Dr. Hasana Sani Darma