Ma’anar Shaye Shaye
Duk lokacin da aka yi maganar shaye-shaye, ana nufin hadiyar kwayoyi masu sa maye ko ganyayyakin da shakarsu, ko cinsu kan fitar da mutum daga cikin tunani irin na ‘yan adam ya koma na dabbobi, Ko sheka wulakantattun abubuwa da mutumin kwarai bazai taba tunawa da suba a wajen abubuwa masu bugarwa da sa maye kamar:
1. kwatami
2. solution
3. zargina
4. ganyen shayi
5. kashin kadangaru
6. maganin tari na yara dss.(Benelin)
SHIN ME YA JEFA YARAN MU CIKIN IRIN WANNAN?
Ma iya cewa dalilai ne guda hudu ko biyar.
1. kwaikwayon miyagun dabi’u ta hanyar kallon fina-finai ko tashoshin ketare ta hanyar gizo da sauran hanyoyin sadarwa.
2. karance-karancen mujallun batsa marassa amfani
3. watsi da tarbiyyar ‘ya ‘ya a sakarwa mata ko dan maraici a rasa mai dauka daga cikin dangin, ko rabuwa
4. yawon almajiranci, tallace-tallace, da aikatau na kananan yara daga karkara zuwa birane.
5. nunawa yaro gata don iyayensa na da wadata wadannan hanyoyi kowacce na iya jefa yara a cikin mummunar dabiar da zata iya gurbata tarbiyyar su.
To, tunda a zahiri ga shi an san dalilan gurbatar tarbiyyar, menene abin yi don a sami mafita?
LUBANA MUKHAR UMAR
Assalamu alaikum wa rahmatullah. ni a gani na wannan laifin zai fi jingina ga gwamnatocin mu, saboda zaka ga matashi ya gama karatunsa na jami’a ko shekara biyu ko uku amma babu aikin yi sai dai kullum su fito bakin layi a kafa majalisa, ana gulmace-gulmace da shaye-shaye, mutum tun baya sha’awar shan wani abu, a hankali sai ya rinka ganin ba komai bane sai ya ce bari ya dan taba shima ya ji, daga nan shike nan. idan da gwamnati zata nema wa matasa aikin yi, ni a ganina yawan shaye-shaye zai ragu.