Abu walid Albaji wani bijimin malami da ya rayu a karni na biyar ya yi wa ‘ya’yansa wata mahimmiyar wasiyya da ya kamata duk wani uba da malamin makaranta ya nazarinta, ya kuma amfana da ita wurin tarbiyyar ‘ya’yansa ko dalibansa.
Bara in dan tsakurowa mai karatu wani abu daga cikin wannan hamshakiyar wasiyya.
-
Ku kiyaye dokokin Allah a fili da boye.
-
Ku kiyayi gina wani hukunci akan ilimin taurari, ko bokanci, domin wannan fitar da wanda ya gasgata shi yake yi daga addni, ya kuma shigar da shi cikin kangararru
-
Ba ku ba zulunci, girman- kai, hassada, gulma da munafunci
-
Ku guji sauraron kade-kade; fitina yake haifarwa a zuci, da tunanin aikata sabo
-
Kada dayanku ya fifita wani abin duniya akan danuwansa, sai ya rika yiwa danuwan nasa rowa saboda shi, ko ya juya masa baya, ko ya rika gasa da shi a ciki. Wanda Allah ya yi wa arzuki a cikinku to su ci tare da danuwansa, kar ya kadaita da shi, ya yi kokarin habaka dukiyar danuwansa, kamar yadda zai yi kokarin habaka tasa… ‘Yaruwa salon wasiyya salo ne na Annabawa da nagartattun bayi a tarbiyya, kuma tasirinsa ya wuce duk yadda kike tsammani, gwada shi ki ga bambanci. Allah ya sa mu dace
Batulu Aminu Dantata