An karbo Hadisi daga Abu Huraira Allah ya kara yarda da shi ya ce:
An tambayi manzon Allah (S.A.W) cewa: Ya Rasulallah! hakika (wance) tana sallar dare, ta yi azumin nafila da rana, tana aikata ayyukan alkhairi, kuma tana sadaka, amma tana cutar da Makotanta (da harshenta)! Sai ya ce: “Babu alkhairi a gareta tana daga cikin ‘yan wuta” sannan aka ce (wance) kuma tana salloli wajibabbu, ta yi sadaka da dan abu kadan, amma bata cutar da kowa. Sai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ita yar aljanna ce”. (Bukhari fil adabil mufrad).
‘YAR UWA IDAN KIKA DUBA WANNAN HADISI ZA KI GA CEWA DUK ALKHAIRIN DA KIKA KULLA TO CUTAR KISHIYA YA WARWARE SHI. WANNAN SHI NE TUFKA DA WARWARA. ALLAH YA YA KIYAYE AMIN.
Ummu Huwailat
Jamilat Bint Abdul’Aziz Alkazauriyya.